Iran Da Pakisatan Sun Jaddada Bukatar Samar Da Harkokin Kasuwanci Na Akalla Dalar Amurka Billiyon $10 A Tsakaninsu
Published: 3rd, February 2025 GMT
Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10.
Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a kasar ta Pakistan.
Muqaddam ya kuma kara da cewa gwamnatocin kasashen biyu suna da dangantaka ta hanyoyi da dama, wadanda suka hada da kasuwanci, al-adu, addini da tsaro da sauransi.
Cibiyar kasuwanci da kuma kamfanoni a kasar Pakistan yana daga cikin cibiyoyin kasuwanci mafi girma a kasar ta Pakistan.
Daga karshe Jakadan ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arziki mafi munin da gwamnatin Amurka ta dorawa kasar Iran amma ta aiwatar da harkokin kasuwanci da kasashen yankin musamman kasar Pakistan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.