Gwamnatin Isra’ila Tana Tsoron Kama Fira Ministanta Don Haka Ta Canja Tsarin Tafiyarsa Zuwa Amurka
Published: 3rd, February 2025 GMT
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi!
A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan haramtacciyar kasar, Benjamin Netanyahu zuwa birnin Washington na Amurka, ya dauki wata hanya ta musamman, domin ya gwammace ya kaucewa wucewa ta sararin samaniyar kasashe wadanda suka tabbatar da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da sammacin kama Netanyahu idan ya shiga sararin samaniyarsu.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya, bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta bayyana aniyar ta fitar da sammacin neman kame jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan hare-haren wuce gona da iri da ta kai kan Gaza, lamarin da ya dada nuna damuwar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan yiwuwar daukar matakin shari’a kan shugabanninta yayin da suke balaguro zuwa kasashen waje.
Tun a jiya Lahadi ce Benjamin Netanyahu ya kama hanyar tafiya Amurka don ganawa da Donald Trump, a ziyarar aiki da ake sa ran za ta kai har zuwa ranar Alhamis.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: haramtacciyar kasar
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.
Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp