Aminiya:
2025-11-02@17:09:41 GMT

Jirage su yi karo a sararin samaniya a Amurka

Published: 30th, January 2025 GMT

An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka.

A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a birnin Washington DC.

Jiragen da suka yi karo sun auka a cikin kogin Potomac, inda a halin yanzu ake aikin ceto, tun baya aukuwar hatsarin jiragen daga misalin ƙarfe 9 na dare.

Jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa jirgin fasinjan na dauke da iyalai da kuma tawagar ’yan wasa Skating, bayan sun kammala atisaye.

DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen M23 —Shugaba Tshisekedi Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin waya

Kafar yaɗa labaran ƙasar Rasha ta ce ’yan wasan Skating Dan ƙasar ma’aurata, Evgenia Shishkova da Vadim Naumov, suna cikin jirgin.

Ma’auratan sun lashe Gasar Skating na Duniya da aka gudanar a Amurka a shekarar 1994.

Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce rundunar tsaron kasar ta fara bincike kan hatsarin jiragen, a yayin da Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa hatsarin mummunan abu ne kuma da za a iya kauce wa.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara na Birnin Washington DC, John A Donnelly Sr, ya ce aikin ceton yana da matukar sarkakiya, a yayin da aka dakatar da suka da tashin jirage zuwa ƙarfe 4 na yamma agogon GMT.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.

Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.

Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.

“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.

Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.

“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.

Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.

“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum