DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen M23 —Shugaba Tshisekedi
Published: 30th, January 2025 GMT
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar.
Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu.
A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji.
A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana iya ƙara munin al’amarin.
NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a AmurkaƘazancewar halin da ke ciki a Gabashin kasar ta DR Congo ya haifar da fargabar ƙara taɓarɓarewar yanayin rayuwar ’yan gudun da matsalar abubuwan more rayuwa a ƙasar.
Amma a ranar Laraba Shugaba Tshisekedi ya bayyana cewa ’yan tawayen suna ɗanɗana kuɗarsu a hannun sojojin ƙasar mai arziƙin zinare da lu’ulu da sauran ma’adinai.
Shugaba Felix Tshisekedi, a jawabinsa na farko tun bayan faruwar hare-haren na M23 a tsawon makonni, ya bayyana cewa sojojin sun samu gagarumar nasara.
Gabashin ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya shafe shekaru sama da 30 yana fama rikici inda ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke addabar al’umma, baya ga tawaye ga gwamnati.
Ana alaƙanta wanna rikici da kisan kiyashi da aya auku a shekarar 1994 lokacin yaƙin basasa ƙasar Rwanda, maƙwabciyar DR Congo.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mayaƙan M23 Rwanda
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.