2025-09-17@21:53:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6281
«Hatsarin Jirgin Ruwa»:
Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata. A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa...
Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya...
A ranar Litinin 8 ga Satumba, 2025 ne gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabuwar majalisar Shurah, karkashin jagorancin gwamna Abba Kabiru Yusuf. Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a gidan gwamnati dake Kano. Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar wa auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa...
Kwace makaman kungiyar Hizbullah… Fadan ne da ba zai yi nasara, inda daga karshe zai zame siyasa bayan gazawar nuna karfi Ana ci gaba da tabka muhawara kan batun neman kwance damarar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Labanon, a daidai lokacin da ‘yan sahayoniya da Amurka ke kokarin cimma wannan buri a siyasance...
Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24 Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da...
Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta...
Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya. A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun...
Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko...
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), ta yi kira ga Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) da ta ƙara mayar da hankali wajen yada labarai kan wasannin gargajiya, irin su langa da kokawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe wanda shi ne shugaban ALGON reshen Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana haka ne...
Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya...
Ta ce cikin ƙasa da shekara biyu, Kaduna ta fito daga durƙushewar tsari zuwa zama jihar da ake ganin tsari. Haka kuma, gwamnatin ta yi zargin cewa El-Rufai ya ƙara ƙoƙarin tayar da rikici bayan abokan siyarsarsa sun sha kaye a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga watan Agusta. Ta ce sakamakon ya nuna...
Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari....
’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai...
An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta. Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin...
shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na...

Araghchi : China da Rasha sun bi sahun Iran wajen kin amincewa da yunkurin E3 na dawo mata da takunkumai
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana....
Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari. Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa,...

Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing...
Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An...
Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya. An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa. Babale ya ce, ana ci...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar...
Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Afghanistan ya haura 800, yayin da ake sa tsammanin karuwar wadanda suka jikkata Hukumomin kasar Afganistan sun sanar da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Afghanistan ya haura 800, yayin da sama da 1,500 suka jikkata, adadin da ake sa...
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Simon Ekpa: An ɗaure...
Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa. Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan. Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a...
Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace. El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin...
Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sallami dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar. Gwamnan ya bayyana labari sallamar ta su ne a taron majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, da safiyar yau Litinin 1 ga Satumbar 2025 Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan Daje...
’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta...
Ana jin tsaron daruruwan mutane ne suka rasa ransa sanadiyyar girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 6 da ta fadawa yankin tsaunuka na kasar Afganistan dake kan iyaka da kasar Pakisatan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran rauters na cewa an jirage masu saukar ungulu suna sauke wadanda suka...
A safiyar yau litininn ce aka fara jan’izar shugaban gwamnatin kasar Lemen Ahmad Ghalib Arrahwi da ministocinsa da suka yi shahada a hareharen da HKI ta kai kansu a lokacinda suke taro a birnin San’a babban birnin kasar. Tashar talabijin ta al-amayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa an gudanar da taron janaizar ne a...
Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa da ta afku a gabashin ƙasar ya haura mutane 610, yayin da aka samu ƙarin mutane 12 da suka mutu a Nangarhar, abin da ya kai jimillar mutuwar zuwa 622. Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka...
Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala...
Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum 610 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 1,300 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta afku a ƙasar Afghanistan. Rahotanni daga hukumomi da kafafen watsa labarai na duniya sun ce ibtila’in ya auku ne a yankin gabashin ƙasar Afghanistan, kusa da iyakarta da Pakistan. Rahoton Hukumar Binciken Ƙasa...
Ya kuma tuna da tsohon abokin ajinsu wanda ya kasance tsohon Sufeton ƴansanda, marigayi Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. El-Rufai ya bayyana shi a matsayin mutum nagari, yana mai cewa tsarin ƴansanda na yanzu ya sha bamban da lokacin da Arase ya jagoranta. Daga ƙarshe, ya...
Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini. Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai...
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai,...
’Yar Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Khadijah, wadda aka fi sani da Andijo, ta rasu. Ta rasu a Abuja tana da shekara 35, kuma ta bar ’ya’ya uku. Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata An yi jana’izarta a...
Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki...

Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO
Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori. Kafin liyafar maraba, Shugaba...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Muhimmancin Aiwatar Da Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei...
Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya tabbatar da cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da...

Gwamnatin Kenya Ta Ci Gaba Da Tono Gawarwakin Da Masu Tsaurin Addinin Kirista Da Suka Kashe Kansu A Kenya
Kenya ta tono gawarwakin mutane 32 a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mace-macen ‘yan darikar addini masu tsattsauran ra’ayi Hukumomin kasar Kenya sun tono gawarwaki 32 a makon da ya gabata a kudu maso gabashin kasar, wani sabon bala’i da ya sake haifar da sukar gwamnatin kasar, wadda a...