2025-09-17@23:36:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3730
«Aisha Humaira»:
Amma Andrew na jihar Taraba, an kama shi ne a ranar Talata, 26 ga watan Agusta lokacin da jami’an NDLEA da hadin gwiwar jami’an Sojin Nijeriya, da Hukumar Tsaron Daji, da kungiyar matasan Mambila da ‘yan banga, suka kai farmaki a gonarsa mai fadin hekta 71.5 ta tabar wiwi da ke dajin Mayodoga, gundumar...
Kungiyar wasan Volleyball na kasar Iran sun sami nasarar kaiwa da wajen karshe a gasar FIVB ta duniya bayan ta lallasa kungiyar kwallon Vallibal ta kasar Amurka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an tashi gasar da Iran 3 Amurka 0. Labaran ya kara da cewa Iran ta sami nasarar mamayar...
Jakadan shugaban kasar Rasha na musamman kan al-amuran yaki a Ukraine ya bayyana cewa masu son yaki a cikin shuwagabannin kasashen turai suna zagon kasa ga kokarin shugaba Trump na kasar Amurka yake yi na kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kirill Dmitriev yana fadar haka, a...
Cibiyar CDC Na Afirka Da WHO Suna Aiki Tare Don Kawo Karshen Cholera Cibiyar Africa Centres for Disease Control and Prevention (Africa CDC) da kuma hukumar lafiya ta Dunita (WHO) sun hada kai don ganin an kawo karshen cutar colera a nahiyar ta Afirk, tare da hada kai da kasashen Nahiyar. Kamfanin yana labarai ta...
Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar Mohammed Sinwar, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin jagoranta a Gaza. Wannan tabbaci ta Hamas ta bayar na zuwa ne fiye da watanni uku bayan Isra’ila ta ce ta kashe shi a wani harin sama. Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara Xi na...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka na rashin bin doka da oda. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar...
Fadar shugaban kasar Yemen a Sana’a ta sanar da shahadar firayim minista Ahmed Ghaleb al-Rahwi tare da wasu ministocin kasar, sakamakon harin da Isra’ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata. Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kara da cewa, wasu ministoci da dama sun samu raunuka sakamakon...
Lauyoyin kare hakkin bil’adama a Argentina sun shigar da kara a gaban kotunan tarayya suna neman a kama firayim ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu idan ya saka kafarsa a kasar, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna yiwuwar cewa zai kai ziyara a kasar a wata mai zuwa. Karar da lauyoyin kasar Argentina masu rajin kare...
Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar. Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a...
A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, a birnin tashar ruwa na Tianjin dake arewacin kasar Sin. Yayin zantawarsu, shugaba Xi ya ce alakar Sin da Masar na cikin wani yanayi mafi kyau a tarihi, ya kuma yi kira da a yi amfani da damar bikin...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin ganawarsa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin tsaron kasar Armeniya a yau Asabar, ya jaddada cewa: Dole ne su tabbatar da cewa babu wani karfin kasashen waje da...
Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya. Ali...
Kungiyar Hamas ta yi maraba da Allah wadai da kasashen Turai 6 suka yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka kan Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi marhabin da matakin da wasu kasashen Turai shida suka dauka na yin Allah wadai da wuce gona da iri da...
Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza. Ya kara da cewa: Abin da...
Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse. Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar. Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Dokar ta-ɓaci: Fubara...
Shi yasa ta ce duk kowa daga ciki al’umma yana da irin gudunmawar da zai bada wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar da zai tafi makaranta, ta kuma kara jaddada tsarin nastressing TaRL yana bada dama ga Jihohi su samu kira da sa duk masu ruwa da tsaki. A tasu gabatarwar ta...
Yayin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da tura manyan ayyukan ci gaba zuwa Legas, tambaya a nan shi ne: shin za a ji daɗin “Renewed Hope” daidai da yadda ake ji a bakin tekun Legas a ƙauyukan Arewa maso Gabas? Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake...
Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka...
Majalisar dokokin kasar Turkiyya ta yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza sannan ta amince da hana jiragen fisinja na HKI wucewa ta sararin samaniyar kasar. Banda haka ta bukaci a kore daga Majalisar dinkin duniya. Majalisar ta bukaci a kula da hakkin Falasdinawa a fagen kasashen a kuma kawo karshen...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kama ma’aikatan Mosad na HKI a lardin Khorasan Razavi da ke arewa maso gabacin kasar, wadanda suka taimakawa HKI a kan hare-haren da ta kaiwa kasar na kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran...
Jakadan kasar Iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeed Iravani yayi watsi da shirin kasashen turai 3 na sake farfado da takunkuman MDD kan Iran.. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa Iran tana kan bakanta na tattauna da wadan nan...
A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa da kwarewa wajen gano yadda aka boye kwayoyin. “Wannan lamari ya nuna jajircewar hukumar wajen katse hanyar rarraba miyagun kwayoyi da tabbatar da tsaron al’umma.” Ya rawaito kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da himma wajen gudanar da aikin....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu. Shugaban ya kuma koka kan yadda...
A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD. Kasashen uku da aka fi sani da E3 sun...
Cibiyar Bloomberg ta bayar da rahoton cewa, Rwanda ta karbi rukunin farko na bakin haure da aka kora daga Amurka, a karkashin wata yarjejeniya mai cike da takaddama tsakanin gwamnatin kasar da gwamnatin Donald Trump. Mai magana da yawun gwamnatin Rwanda Yolande Makolo ya tabbatar da cewa “rukunin farko na bakin haure bakwai da aka...
Jack Neriya, tsohon shugaban hukumar leken asirin Isra’ila a Syria da Lebanon, ya yi gargadi game da masu tunann cewa ta yi rauni, yana mai jaddada cewa “kungiyar ta sake gina karfin soji kuma ba ta da niyyar yin watsi da makamanta.” A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, Neriya...
Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa. Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba. Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima,...
Shugaban kamfanin rarraba wutan lantarki na kasar Iran ya bada sanarwan cewa kasar China ta zuba jari na kimanin dalar Amurka miliyon 70 a aikin samar da wutan lantarki mai karfin MW 200 wanda kamafanin SATBA yake ginawa a lardin Bushar na kudancin kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Gholam...
“Ban ga dalilin da ya sa ba a raba fifikon fasaha na Brazil da Afirka ba. Mun tabbatar wa junanmu cewa mune kawai za mu iya bunkasa tattalin arzikinmu don taimakawa kasarmu,” Tinubu ya shaida. Tinubu ya kuma bai wa masu zuba hannun jari tabbacin cewa manufofin farfado da tattalin arzikin Nijeriya na haifar da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama. Ambaliya ta raba...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙara kuɗin fasfo. Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta ƙara kuɗin fasfo mai shafi 32 zuwa Naira 100,000, yayin da mai shafi 64 ya koma Naira 200,000. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan...
Ambaliyar ruwar da ta biyo bayan mamakon ruwan saman da aka tafka ta raba kauyuka shida da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato da saurann yankunan jihar. Kauyukkan da ambaliyar ta shafa su ne Makuwana da Dangawo da Faru da Gumbula da ’Yan Faruna da kuma Magajin Dawaki, sannan ta lalata hanyar da...
Bayan sanarwar da E3 (Faransa, Jamus, da Burtaniya) suka yi na haifar da hanyar da za ta kai ga dawo da takunkumin da aka kakaba wa Tehran kan shirinta ma nukiliya, Majalisar Dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da wani kudirin doka na gaggawa da ke ba da shawarar ficewa gaba daya daga yarjejeniyar...
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa...
Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar. Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki. Masu shirya taron...
Annabi (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya tashi a ranar Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, shi ne wanda Allah ya kebanta da tsani da wasilah, shi kuma ya kebanci muminai masoyansa da ita. Allah ya girmama Manzon Allah (SAW) da abin da bai girmama wani dan Adam...
Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake...
Harshen Hausa shine kan gaba a yawan masu magana a Afrika ta Yamma ta yadda yake da karbuwa a Nijeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Benin, Gabon, Togo, Afrika ta Tsakiya, Sudan da Saudiyya da sauran su. Hasalima kowace nahiya ta duniya akwai jami’ar da ake koyar da harshen Hausa da Hausanci. Bunkasar Harshen Hausa ya sa...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dangantaka tsakanin Iran da China na dauke da dabarun manufofi masu kyau Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Kasar Iran na da sha’awar gudanar da hadin gwiwa mai ma’ana da kasar China, musamman a fannin raya dabarun kiyaye hanya, yana mai bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Matakin da gungun kasashen Turai ke son dauka kan Iran yana dagula tsarin diflomasiyya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi la’akari da yadda kasashen Turai uku suka yi amfani da tsarin warware takaddamar da ba bisa ka’ida ba a karkashin tsarin hadin gwiwa na (JCPOA)...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta mayar da martani ga Tawagar Turai na kokarin dawo da takunkumi kan kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da sanarwa a matsayin martani ga sanarwar da Tawagar Tura ta yi wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da baya kan ka’ida dangane da kuduri mai lamba 2231. Ma’aikatar harkokin wajen...
Jami’in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: A shirye suke su ci gaba da yaki na dogon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila Jami’in kungiyar Ansarullah ta Mabiya Huthi ta kasar Yemen Mohammed al-Bukhaiti ya bayyana cewa: A shirye al’ummar Yemen su ci gaba da yaki na tsawon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila, kuma...
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan mummunan sakamakon Shirin Isra’ila na fadada ayyukanta a birnin Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi gargadi kan mummunan sakamakon matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila zata dauka na fadada ayyukan soji a birnin Gaza, yana mai yin Allah wadai da manufofin fadada gine-ginen...

Baki Kusan 50 Daga Kasashe 30 Na Turai Za Su Halarci Bikin Tunawa Da Nasarar Yakin Turjiyar Sinawa Kan Zaluncin Japanawa
A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika...
A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da...
Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci. Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana. Daga kanmu, magana ta...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a zantawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen Turai guda uku wato E3, ya ja kunnensu kan sake maida takunkuman MDD da ke cikin yarjeniyar JCPOA. Ya gargadesu kan cewa Tehran zata maida martanin da ya dace da aikinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran...