NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya
Published: 12th, September 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Sau da dama wadanda ke dauke da nau’in jini na AA na bayyana cewa sun fi kowa lafiya.
Suna bayyana cewa basa rashin lafiya kamar yadda masu sauran na’ukan jini ke yi.
NAJERIYA A YAU: Rayukan Da Aka Rasa Sakamakon Ambaliyan Wannan Shekarar DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuShirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan ko da gaske ne masu nau’in jini na AA sun fi sauran masu nau’ukan jini lafiya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
Wasu lauyoyi biyu a Najeriya sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya da ta yi taka-tsantsan wajen yin hulɗa da ƙasar Amurka, inda suka ce maganganun Amurka a kan Najeriya abun ruɗarwa ne
Babban lauyan nan, Cuf Okoi Obono-Obla, wanda tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara ne, ya zargi Amurka da son raba kan ’yan Najeriya da sunan kare Kiristoci.
Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a NijeriyaYa ce iƙirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya ƙarya ne face nufin tayar da hankali da kawo rikici.
“Najeriya ba ta taɓa zama barazana ga zaman lafiyar duniya ba,” in ji Obono-Obla.
“Idan Amurka, inda ake yawan harbe mutane a coci-coci, ba ta gayyaci sojojin ƙetare su shigo musu ba, to kamata ya yi ta bar Najeriya ta magance nata matsalolin.”
Ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin Amurka na yin katsa-landan cikin harkokin Najeriya zai zama take doka da tauye ikon ƙasa.
Shi ma Barista Leonard Anyogo, kuma shugaban ƙungiyar ‘Good Governance Advocacy International’, ya shawarci Najeriya da ta bi hanyoyin diflomasiyya wajen mayar wa Amurka martani ba da faɗa ba.
“Ya kamata mu tattauna, ba mu yi fada ba,” in ji Anyogo.
“Najeriya ta nemi haɗin kai da Amurka a fannin tsaro da diflomasiyya domin kare muradunta.”