Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5
Published: 18th, September 2025 GMT
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta wuce yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.
Darektan kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhang Yuzhuo ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 har zuwa yanzu, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnati ta karu daga kasa da yuan tiriliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka kimanin tiriliyan 10, zuwa sama da yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6, yayin da jimillar ribar da suka samu ta karu daga yuan tiriliyan 1.9, kwatankwacin sama da dalar Amurka biliyan 267, zuwa yuan tiriliyan 2.6, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 365. Matsakaicin karuwar jimlolin biyu a kowace shekara kuwa ya kai kashi 7.3 cikin dari da kashi 8.3 cikin dari bi da bi.
Bugu da kari, tun daga aka fara aiwatar da shirin, kamfanoni mallakar gwamnati sun biya kudin harajin da yawansu ya zarce yuan tiriliyan 10, kwatankwacin fiye da dalar Amurka triliyan 1.4, kuma darajar yawan hannun jarin da suka mikawa asusun inshorar zaman al’umma ta kai yuan tiriliyan 1.2, kwatankwacin fiye da dalar Amurka biliyan 168.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: mallakar gwamnati da dalar Amurka yuan tiriliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.
An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”
Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.
“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”
Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.