’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja
Published: 12th, September 2025 GMT
’Yan bindiga sun kai wa wata mota hari a kan hanyar Tegina zuwa Kontagora a Jihar Neja, inda suka jikkata mutum biyu.
Harin ya faru ne a Tudun-Fulani bayan direban motar ya ƙi tsayawa lokacin da ’yan bindigar suka buƙaci ya tsaya.
’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027Rashin tsayawarsa ya sa maharan suka buɗe wa motar wuta, inda suka jikkata fasinjoji biyu da ke zaune a kujerar gaba.
Wannan lamarin ya faru ne bayan sa’o’i da ’yan bindigar suka sace wasu makiyaya a garin Usalle da daren ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewar ’yan bindigar sun tura makiyayan bakin hanya sannan suka yi yunƙurin amfani da su wajen tare motocin da ke wucewa a kusa da ƙauyen Samaza Sauri da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora.
Wani mutum ya ce: “Da misalin ƙarfe 10:30 na dare, sun sace wasu makiyaya a Usalle.
“Bayan nan suka tare hanya a Samaza Sauri, sun buɗe wa motoci da ke zuwa Kontagora wuta, inda suka jikkata mutum biyu a ƙafafunsu.”
Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, ta tabbatar da aukuwar harin.
Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya ce: “A ranar 11/09/2025 da misalin ƙarfe 12:15 na dare, wasu ’yan bindiga sun yi ƙoƙarin tare wata mota a Tudun-Fulani.
“Direban ya tsere, amma sun buɗe musu wuta tare da jikkata fasinjoji biyu. An kai su asibiti, amma ba a sace kowa ba.”
’Yan sanda da jami’an tsaro sun isa wajen da harin ya auku, amma ’yan bindigar sun tsere cikin daji.
A wani harin kuma, ’yan bindiga sun shiga ƙauyukan Uzange da Matachibu a gundumar Masuga da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora, inda suka sace mutum uku cikin daren ranar Alhamis.
Mazauna Ƙananan Hukumomin Kontagora, Mariga, da Magama, sun bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga sun ƙaru a baya-bayan nan, inda suka ce an sace mutane da dama tare da yin awon gaba da ɗaruruwan shanu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga mahara Yan bindiga sun yan bindiga sun yan bindigar
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025
Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda October 30, 2025
Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025