Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154
Published: 12th, September 2025 GMT
An kammala taron baje kolin zuba jari na duniya na Sin karo na 25 (CIFIT) a jiya Alhamis 11 a birnin Xiamen. A yayin taro na wannan karo, an kulla yarjejeniyoyin ayyukan zuba jari guda 1,154, inda jimillar kudin dake kunshe a ciki ta kai kudin Sin Yuan biliyan 644 (kwatankwacin sama da dala biliyan 90.
Taron mai taken “Hadin kai da Sin don zuba jari ta yadda za a samu bunkasa nan gaba,” ya gudana ne a fadin filin baje koli da ya kai murabba’in kilomita 12. An gudanar da ayyukan habaka zuba jari sama da dari, kuma tawagogin kasashe da yankuna fiye da 120 sun halarta, tare da kokarin kirkirar wani babban baje koli na “Zuba jari a Sin” da kuma muhimmin dandali don habaka zuba jari tsakanin bangarorin biyu.
A lokacin taron, an gudanar da tattaunawa tsakanin manyan kamfanoni na duniya, da kuma tattaunawa tsakanin shahararrun kamfanoni masu zaman kansu da manyan kamfanoni dake sahun gaba a duniya guda 500, da kuma ayyukan tallata kasuwanci sama da 30, wanda ya nuna cikakkiyar dama da samun kuzarin “Zuba jari a Sin” a kowane fanni. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba
Bugu da kari, shaidu na zahiri sun tabbatar da cewa alakar ci gaban kirkire-kirkiren fasahohin Sin da sauran sassan duniya, ya kunshi kafa tushe na samar da karin daidaito a fannoni da dama, ciki har da hada-hadar cinikayya ta dijital, da ilimi da jagoranci.
Ta hanyar rage gibin dake akwai tsakanin mabanbantan sassan duniya, sashen kirkire-kirkiren fasahohin Sin na kara fadada damar raya masana’antun duniya, da samar da guraben ayyukan yi, musamman a yankunan duniya da aka jima da yin watsi da su, wanda hakan zai yi matukar amfanar da tsarin kasuwancin duniya.
A fannin raya fasahohin cin gajiyar makamashi marar dumama yanayi ma kasar Sin na kara taka rawar gani, inda alal misali Sin ke bayar da babbar gudummawa ga babban burin nahiyar Turai na fadada amfani da nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa, wani mataki da a halin da ake ciki ke kara ingiza aniyar manyan kamfanonin kera batira na kasar Sin, su zuba jari a kamfanonin kirar ababen hawa masu amfani da lantarki na Turai, irin su kamfanonin dake kasashen Jamus, da Faransa da Hungary.
Ta haka, kamfanonin Turai za su ci karin gajiyar fasahohin Sin na kera batiran ababen hawa, da ingiza saurin ci gaban fasahohin da kamfanonin na Turai ke bukata a wannan fage.
Ko shakka babu, ta hanyar samar da kyakkyawan yanayin bude kofa ne kadai, gajiyar kirkire-kirkiren fasahohin kimiyya da fasaha tsakanin sassan kasa da kasa za su amfani duniya baki daya. Musamman duba da cewa, tattalin arzikin duniya ba wai wani abu ne guda daya da wasu za su ci gajiyarsa wasu kuma su rasa ba, maimakon haka, wani tsari ne mai sassauyawa wanda a cikinsa tsarin gudanar kirkire-kirkiren fasahohi ke iya fadada damar dukkanin sassan duniya ta cin gajiya marar iyaka.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA