’Yan bindiga sun buɗe wa ’yan zaman makoki wuta a Anambra
Published: 13th, September 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, ta fara bincike kan kisan wasu mutum huɗu da ’yan bindiga suka yi lokacin da suke zaman makoki.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa masu makokin wuta ne a ranar Alhamis a garin Ogidi, da ke Ƙaramar Hukumar Idemili.
Hilda Baci ta kafa tarihin dafa shinkafa buhu 200 a tukunya guda Abba ya tarbi tagwayen da aka raba da juna bayan yi musu tiyata a SaudiyyaHarin ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu tare da jikkata aƙalla mutum 15.
Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga, ya ce suna zargin harin ya shafi rikicin ƙungiyoyin asiri ne.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da suka isa wajen sun gano harsasai 16, kuma za su yi amfani da su wajen bincike.
Ikenga, ya ce nan gaba za su sanar da jama’a abin da binciken nasu ya gano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Anambra hari
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA