Sauyin Yanayi : Shugabannin Afirka sun bukaci a yi adalci
Published: 11th, September 2025 GMT
Shugabannin kasashen Afirka sun kammala taron kwanaki 3 kan sauyin yanayi na Afirka a babban birnin kasar Habasha a jiya Laraba tare da amincewa da sanarwar Addis Ababa, inda suka yi alkawarin mayar da nahiyar ta zama cibiyar samar da makamashi mai safta da kuma hanyoyin magance sauyin yanayi a yayin da suke neman kudade na gaske.
Shugaban kasar Habasha Taye Atske Selassie, wanda ya rufe taron, ya ce taron ya nuna cewa Afirka ba ta shiga cikin rikicin da ba ta haifar da shi ba.
” Mun himmatu wajen samar da wata nahiya mai wadata,” in ji shi.
“Zalunci ne cewa sama da ‘yan Afirka miliyan 600 har yanzu suna rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba.
Dole ne aikin mu na yanayi ya fara da saka hannun jari mai yawa don sabunta makamashi da kuma yin kira ga tabbatar da adalci.”
Taron na neman karfafa murya guda daya ta Afirka a fagen duniya kan rage illolin sauyin yanayi, tare da bunkasa tsare-tsaren da ke da amfani ga kasashen Afirka kafin taron COP da za a gudanar a Brazil a watan Nuwamba mai zuwa.
Bayar da kudi da tabbatar da adalci na yanayi a na daga cikin ajandar babban taron.
Bankin raya kasashen Afirka ya yi kiyasin cewa ana bukatar dala biliyan 100 a duk shekara domin daidaita ababen more rayuwa, da tsaron aikin gona, da zuba jari a fannin makamashin da ake iya sabuntawa a Afirka.
Sai dai a cewar wani rahoton sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, dala biliyan 30 ne kawai aka tara wa Afirka tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024 ta asusun kula da yanayi na Green Climate (GCF).
A cewar Mahamoud Ali Youssouf, shugaban hukumar ta AU, “kasashen Afirka na bukatar garanti mai karfi da sabbin hanyoyin samar da kudade don sauya burinsu zuwa ayyuka na zahiri.”
Bisa takardar share fagen taron, Afirka na bukatar kusan dala biliyan 579 don samar da kudaden da za ta samar da daidaita tsakanin shekarar 2020 zuwa 2030.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sheikh Qasim: Hare-Haren HKI Kan Qatar Sashe Ne NA Shirinta Na “Isra’ila Babba” September 10, 2025 Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar September 10, 2025 Aragchi: Yarjeniya Da IAEA Ya Nuna Hakurin Iran Bayan Hare-Hare Kan Cibiyoyin Nukliyarta September 10, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Guda kan HKI bayan Harin Qatar September 10, 2025 Sojojin HKI Sun Ragargaza Hasumiyyar Tayyib II A Kokarin Korar Falasdinawa Daga Birnin Gaza September 10, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138 September 10, 2025 Araqchi Ya Isa Kasar Tunisiya A Wata Ziyarar Aiki Da Ya Kai. September 10, 2025 Babu Gaggawa Na Fara cire Haraji Kashi 5 Na Man Fetur A Nijeriya September 10, 2025 Da Alama Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya September 10, 2025 Iran Da Hukumar IAEA Sun Fahimci Juna Kan Shirinta Na Nukiliya . September 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sauyin yanayi
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
Rahotanni da muka samu sun nuna cew wasu yan ta’adda sun kashe wasu dakarun sa kai guda biyu a kudu masu gabashin iran a yankin sisitan Baluchistan.
Jami’In huda da jama’a na dakarun kare juyi yayi karin harke game da harin da aka kai, yace an kashe mutane ne yayin da suke kokarin ketare da jami’an tsaro suna tafiya akan babbar hanyar da ta hada birnin kashsh dake lardin da kuma babban birnin zahidan
An bayyana cewa wanda abin ya shafa sun hada da Esma’il shavarzi da kuma mukhtar shahouze da kuma wadanda suka samu mummuan rauni a lokacin kai harin
Lardin sistan baluchestan na da iyaka da kasar Pakistan da ya dade yana fuskantar tashe tashen hankula kan fararen hula da kuma jami’an tsaro
Hukumomin yankin sun sha bin asalin tushen irin wadannan hare-hare zuwa cibiyoyin leken asirin na kasashen waje dake nuna goyon bayan yan’ taa’dda dake irin wadannan ayyukan a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci