2025-10-18@18:53:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 710

«Nukliyar kasar Iran»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Hadakar Kasashen Sahel na AES, sun yi ban kwana da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO a hukumance bayan shekaru 50 na kasancewa mamba a cikinta. Ya zuwa wannan Laraba, 29 ga Janairu, bangarorin biyu sun raba gari duk da cwa kungiyar ta ECOWAS ta baiwa kasashen wa’adin watannin shida ko zasu canza ra’ayi. Kasashen na Mali, Nijar da kuma Burkina Faso sun ce bakin alkalami ya riga fa ya bushe. A jiya Talata al’umomin kasashen guda uku sun gudanar da gangami da jerin gwano na nuna murnar ficewa daga kungiyar da suka ce ta zama ‘yar amshin shatan kasashen yamma musamman faransa wacce ta yi musu mulkin mallaka. Haka zalika a wannan Larabar ce...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a wata hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Sky News a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, ban tsamman zasu yi haka ba. Amma idan sun, to kuwa ba zasu ji ta da dadi ba. Yace: JMI ta rattaba hannu a kan yarjeniyar Nukliya da manya-manyan kasashe 6 a duniya kan shirin ta na makacin Nukliya wanda...
    Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
    An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan. Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon. “Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,”...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wani harin Amurka kuma ya gargadin sojojin haya Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya tabbatar da cewa: Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta wajen tallafawa haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kokarin murkushe al’ummar Falasdinu, yana mai jaddada tsayin daka da matsayarsa da ke tafiya a kan tubalin gaskiya, ikhlasi da ke gudana a tsakanin al’ummar Falastinu da ‘yan gwagwarmayarsu. Sayyid Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya bayyana a yayin zagayowar ranar shahadar Sayyid Hussein Badruddeen al-Houthi, cewa: Abin da hukumomi suka yi a shekara ta 2004 kan shahidi wanda shi ne ya kafa tattakin Alkur’ani, kuma shugaba shahidi Hussein Adwan, ba a yi adalci...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare kasar Lebanon daga ha’incin makiya ba wai kawai tawada ne a takarda ba, don haka sun daurawa kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen da suke daukar nauyin yarjejeniyar da aka cimma alhakin take hakki da laifuffukan makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta mata ficewa gaba daya daga yankin Lebanon. ‎Tun daga shekara ta 2000 har zuwa yau, lamarin ya ci gaba da maimaita kansa, domin al’ummar...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey  Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya. SERAP, ta ce wannan karin an yi sa...
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
    Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas. A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza. Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke...