Aragchi Yace Duk Wani Harin Da Aka Kaiwa Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran Hakan Wata Musiba ce Ga Yankin Asiya Ta Yamma
Published: 28th, January 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba.
Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a wata hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Sky News a nan Tehran.
Ya kuma kara da cewa, ban tsamman zasu yi haka ba. Amma idan sun, to kuwa ba zasu ji ta da dadi ba.
Yace: JMI ta rattaba hannu a kan yarjeniyar Nukliya da manya-manyan kasashe 6 a duniya kan shirin ta na makacin Nukliya wanda ake fi sani da JCPOA amma a shekara ta 2018 shugaba Trump a wa’adin mulkinsa na farko ya fitar da Amurka cikin yarjeniyar, sannan ya dora mata takunkuman arziki mafi muni a tarihin kasar Iran, da nufin karya gwamnatin JMI. Amma hakan bai faru ba. Sai kuma a shekara ta 2019 Iran ta fara dauke kataita shirin makamashin nukliyarta ta zaman lafiya da ta saboda maida martani ga dayan bangaren wacce ta sabawa alkawulanta su.
A baya-bayan nan mun ji Trump yana fadin wasu maganganu, wanda yake cewa masu dadi, amma sai mun ganshi a kasa. Sai dai yakamata Amurka da kawayenta su sani ka cewa Iran ba zata sake tattaunawa da su da sauki ba.
Daga karshe ministan ya mayarwa Trump Martani kan mutanen gaza, da cewa ya maida HKI zuwa Green Island ya fi mata sauki da ya maida Falasdinawa Masar da Jordan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron.
Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore.
Har’ila yau ana gudanar da bincike a cikin barikokin sojojin kasar a birnin Wagadugu a kokarin gano wadanda suke adawa da gwamnatin Traore, sannan suke aiki wa kasashen yamma musamman kasar Faransa wajen ganin bayan shugaba Ibrahim Traore.
Kafin haka dai an nakalto ministan tsaron kasar ta Burkina faso Muhammada Sana ya na wani bayani a tashar talabijin na kasar, kan cewa kafin su gano shirin juyin mulki sun satar maganar wayar tarho tsakanin wani babban sojan kasar da shugaban wata kungiyar ta’addaci wanda aka shirya za su kashe shugaba Traore.