Leadership News Hausa:
2025-04-30@19:41:27 GMT

Zantawa Da Shugaban Kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake

Published: 26th, January 2025 GMT

Zantawa Da Shugaban Kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake

Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki.

Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya.

Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari a kan hanyar ci gaban kasar Sin wani abu ne da ya kamata mu yi, musamman yadda za mu iya koyon abubuwa masu daraja da yawa daga gogewarta. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka

A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.

 

Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai EU ta zartas da matakan mayar da martani kan Amurka a zagaye na farko. Firaministan kasar Japan Ishiba Shigeru kuma ya bayyana a fili cewa, bai shirya mika wuya don cimma yarjejeniya kan harajin kwastam cikin hanzari ba.

 

Yanayin rudani da Amurka ke ciki cikin kwanaki 100 da suka gabata ya ilmantar da jama’a cewa, babu wanda zai yi danniya bisa ganin dama. Kuma babu wanda zai hana dunkulewar tattalin arzikin duniya. Hadin gwiwa mai kunshe da kowa da samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare, ita ce hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
  • Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
  • Cinikayyar Hidima Ta Kasar Sin Ta Matukar Bunkasa A Rubu’in Farko Na Nana
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu
  • Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
  • Shin Amurka Na Iya Komawa Kan Kadaminta A Matsayin Cibiyar Masana’antun Duniya?
  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA