2025-10-16@14:49:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 165
«sahayoniyar su»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ta tabbata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga ta bana bayan da Bayer Leverkusen ta buga canjaras a wasanta da Freiburg yau Lahadi. Itama Munich canjaras ta buga a wasanta na ranar Asabar tsakaninta da RB Leipzig inda aka tashi da ci 3-3, amma kuma sakamakon wasan Bayer Leverkusen dake matsayi na biyu ya tabbatarwa Munich nasarar lashe gasar Bundesliga karo na 34 a tarihinta. Harry Maguire Ya Sanya Hannun Kwantaragin Shekara Ɗaya A Manchester United Dortmund Ta Doke Bayern Munich A Wasan Hammayya A Gasar Bundesliga Za a iya cewa kocin ƙungiyar Vincent Kompany, wanda ya karɓi aikin horar da ƙungiyar bayan korar Thomas Tuchel ya shigo da kafar dama, wannan ne karon farko da...

Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Suka Kai Kan Kasar Siriya
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Siriya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah-wadai da harin bam da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Siriya a ranar Asabar. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullahi ta fitar ta ce: Tana jaddada tofin Allah tsine da yin Allah wadai da zaluncin yahudawan sahayoniyya da suka addabi kasar Siriya a wani mummunan hari da suka kai kan yankunan kasar, tare da fakewa da munanan kalamai da take-take na aiwatar da ayyukanta na fadadawa da wargaza kasar Siriya da nufin rusa hadin kan kasar da kuma haifar da...
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin tada zaune tsaye daga ‘yan sahayoniyya Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi, ya yi gargadin yadda yunwa ke barazana ga Falasdinawa sama da miliyan biyu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa a idon dukkanin bil’adama. Yana mai jaddada cewa: Wannan abin kunya ne ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa. A jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar shelar Falasdinawa kan neman taimakon Falasdinawa dangane da hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, Sayyid Al-Houthi ya yi bayani kan sabbin abubuwa da suka shafi wuce gona...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko Wata majiyar unguwar da lamarin ya faru ta shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis, maharan sun kai harin ne ’yan mintuna kaɗan bayan jirgin ruwan fasinjan ya tashi daga gaɓar ruwan Swali a Yenagoa, babban birnin jihar....
Cikin adadin, masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Saudiyya da Serbia, suna cikin mafiya bayyana matukar baiken matakin na Amurka, da karin kaso 28.5 bisa dari. Yayin da a daya bangaren al’ummun Malaysia, da Isra’ila, da Australia, da Singapore, da Philippines, da Najeriya, da Portugal, da Pakistan, da Afirka ta kudu, kasonsu na nuna baiken matakan kara harajin na Amurka ya karu da sama da kaso 20 bisa dari. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata tsohuwa mai shekara 80 a kasar Turkiyya za ta shafe sama da shekara 4 a gidan yari, saboda ta daki jikarta ’yar shekara 18 da silifa a lokacin da suke takaddama. Asiye Kaytan na zaune tare da jikarta Vural a unguwar Topraklık da ke Denizli a Kudu maso Yammacin Turkiyya. Tuntuni dai iyayen yarinyar suka rabu, inda tsohuwar mai shekara 80 take kulawa da ita fiye da kanta. A ranar 9 ga Agustan bara, bayan Vural ta dawo daga aiki, ta fada wa kakarta cewa, za ta fita waje tare da wasu abokanta. Tsohuwar ta ji tsoron fitar don kare lafiyarta, ta ce ba za ta yarda ba, har ma ta kulle kofa don tabbatar da cewa Vural ba...
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama. A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar...
Bari mu dauki dala a matsayin misali, tattalin arzikin Amurka na dogara ne kacokan da girman dalar Amurka. Yayin da kasafin kudinta ke gazawa wajen biyan bukatunta na cikin gida, kuma tana da al’adar dogaro da kasashen waje kan kudaden da take kashewa da ke da alaka da jingina gazawar mulkinta ga sauran kasashen duniya, kamar yadda ta yi a lokacin rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008, ta yaya masana’antunta za su farfado bisa wannan tsarin? Hakazalika, babu yadda za a yi Amurka ta sake zama cibiyar masana’antun duniya bayan da ta yi watsi da matsalolin da ake fuskanta a zahiri kamar sauyin yanayi, wanda ayyukan masana’antu ne suka haifar da shi tun farko. Bari mu dauka...

Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Darajar Cinikin Sarin Kaya Da Sayen Kayan Masarufin Sin Ta Karu Da Dala Biliyan 452.5 a Rubu’In Farkon Bana
Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a rubu’in farko wato daga watan Janairu zuwa Maris na bana, darajar wadannan bangarori ta karu da dalar biliyan 452.5 a wadannan watanni uku, wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokacin bara, kana adadin ya kai kashi 10.4% bisa na dukkan GDPn kasar. Nagartacciyar bunkasar wadannan sana’o’i na nuna goyon baya na tsarin habaka bukatu cikin gidan kasar da tafiyar da tattalin...
Dubban jama’a ne suka hallara domin ɗaurin auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar. Cikin baƙi akwai Shugaban Kamfanin rukuin Media trust Malam Kabiru Yusuf da sauran manyan baƙi suka hallara a birnin domin ɗaurin auren da kuma naɗin sarautar “Makama Babba I da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar. Masu garkuwa za su mutu ta hanyar rataya a Edo – Okepebolo An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja Alhaji Bala Ahmad babban limamin Bauchi ne ya jagoranci ɗaurin auren, wanda Shettima ya kasance a matsayin waliyyin ɗiyar...
Cibiyar Nazarin Jinsi (CGS) Jami’ar Bayero Kano BUK ta jaddada aniyar ta na ci gaba da ayyukan da suka shafi jinsi ta hanyar sabunta aikinta da kuma inganta karfinta na ma’aikata. Darakta CGS, Dakta Ambasada Safiya Nuhu, ta bayyana haka a lokacin da ta kai ziyarar ban girma ga Shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas. Ta ba da tabbacin mataimakiyar shugabar gudanarwa ta CG ta ci gaba da ba da goyon baya wajen tinkarar al’amuran al’umma, musamman wajen karfafa dabi’un iyali, inganta al’adun gargajiya, da kuma haifar da kyakkyawar tarbiyya. Dokta Safiya ta jaddada cewa sabbin nade-naden mukaman da aka yi wa mataimakan daraktoci na cibiyar na nuni da yadda jami’ar ta yi hadin...
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da ya kunshi yin Allawadai da keta hurumin masallacin kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a cikin kwanaki uku a jere. “Yan sahayoniyar dai sun rika shiga cikin harabar masallacin na Kudus, suna yin ibadunsu na yahudanci, tare da kariyar ‘yan sandan HKI. Kungiyar ta Hizbullah ta kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniyar suke yi nuna kiyayya ne, da keta hurumin masallacin kudus. Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa; Abinda ;yan sahayoniyar suke yi, ya isa bakantawa musulmi al’ummunsu da gwmanatocinsu, ya kuma sa su yunkurawa domin hana ci gaba da abinda yake faruwa. Hizbullah ta kuma ce; Al’ummarmu ta larabawa da musulmi tana da cikakkiyar masaniya akan bukatar...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatarsa da sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam kuma shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam ya yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki kasar daga ranar 14 zuwa 15 ga wata. Haka kuma, bisa gayyatarsa da firaministan kasar Malaysia da sarkin Cambodia suka yi, shugaban na kasar Sin kuma sakatare janar na JKS, zai ziyarci kasashen Malaysia da Cambodia daga ranar 15 zuwa 18 ga wata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
A wani mataki na kara nesanta kanta da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci. Kamfanin dillancin labarin kasar AFP ne ya ruwaito hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 31 ga Maris. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista Tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Muhammad Bazoum, Nijar ɗin ke ɗaukar matakan nesanta kanta da Faransa, inda ta fara da korar sojojinta da kuma sauyawa wurare da dama da ke da alaƙa da kasar suna. Bayan haka kuma, Nijar ɗin da sauran ƙasashen da Faransan ta yi...
Babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ruben Amorim ya ce ya shaida wa Bruno Fernandes cewa ba zai bar shi ya bar kungiyar ba a bazara, kyaftin din kungiyar Fernandes wanda ya rattaba hannu a kan kwantiragin har zuwa 2027 a watan Agustan da ya gabata ya kasance tauraron dan wasan United a kakar wasa ta bana. Bruno Fernandes ya ci kwallaye 95 a wasanni 277 da ya buga tun zuwansa Manchester United daga Sporting a shekarar 2020, a karshen mako rahotanni sun bayyana ana danganta dan wasan mai shekaru 30 da komawa Real Madrid. Spain Ta Lallasa Ingila A Wasan Ƙarshe Na Kofin Euro 2024 De Bruyne Zai Bar Manchester City A Ƙarshen Kakar Wasanni “A’a, ba...
Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da Amurka ta yi, al’amarin da a cewarsu, ka iya janyo ramuwar gayya daga kasashe daban-daban, har ma zai iya ta’azzara yakin harajin fito a duniya, da kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya. Kashi 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna cewa, yayin da ake fuskantar rashin daidaiton ci gaba da karfin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, neman cike gibin cinikayya da...
Jaridar BusinessDay tayi nazari kan manyan ayyuka biyar na Layukan Dogo da suka samar wani sauki, a zirga-zirgar Jirgin kasa a kasar nan. 1 Layin Dogo Daga Legas Zuwa Ibadan Ingantaccen aikin layin Dogo mai tsawon kilomita 157 da ya taso daga jihar Legas zuwa garin Ibadan. An faro aikin ne a watan Maris na 2017 aka kuma kaddamar da shi, a ranar 10 na watan Yununin 2021. Aikin ya kasance mai tagwayen hanya biyu da ake da shi, Afrika ta Yamma. An kammala aikin layin na Dogon ne, cikin shekaru hudu, wanda kuma aka kara fadada shi zuwa kimanin kilomita 7 domin ya hade da layin Dogo na tashar Jirgen Ruwa da ke Apapa. Wannan layin Dogon, na bayar...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari daga shugabancin Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL). Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar da safiyar Laraba ta tabbatar da naɗa Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin.
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar. Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Ofishin firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ”wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a...
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar. Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Ofishin firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ”wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a...
Kungiyar Hamasa a gaza ta bada sanarwan cewa ta amince da shawarar da kasashen da suke shiga tskaninta da HKI kan cewa ta amince da kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa, amma ba zata taba mika makamanta ga wani ba ko waye shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Kungiyar Khalil Al-Hayya yana fadar haka a jiya Asabar a wani jawabin da ya gabatar da faifen bidiyo. Al-Hayya ya kara da cewa muna karban dukkan shawarori masu ma’ana idan an bijirosu gare mua. Amma batun makamanmu, ba zamu taba kyale mutanemmu a hannun yahudawan sahyoniyya ko kuma wasu shuwagabannin Falasdinawa wadanda zasu mika su ga yahudawa ba suna ta yawo da hanka;linsu ba. Yace fatammu ne gwamnatin...
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi Dabarun Rabauta Da Kwanaki 10 Na Ƙarshen Ramadan “Muna bai wa makarantun Tsangaya 85 kayan abinci 85, biyar a kowace Ƙaramar Hukuma, inda muke ciyar da almajirai tsakanin 300 zuwa 400 a kowace makaranta,” in ji shi. Ya ƙara da cewa Gwamna Mai Mala Buni ne, ya amince da wannan shiri domin tallafa wa yara marasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma. Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da...
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja. Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze. Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara. Wasiƙar ta ce PDP ta gaza biyan kuɗin tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni (FCTA) ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen. Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a...
A daren ranar Lahadi Barcelona ta buga wasa mafi kayatarwa a wannan kakar wasanni ta bana bayan ta doke abokiyar karawarta Athletico Madrid duk da cewar Athletico din ta jefa kwallaye biyu a ragar Barcelona a minti 70 na wasan. A kokarin da take yi na sake darewa kan teburin Laliga, Barcelona ta zura kwallaye 4 a cikin minti 20 domin komawa gida da maki uku, Lewondowski, Ferran Torres da Lamine Yamal ne su ka jefawa Barcelona kwallayenta. Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu Julian Alvarez na Athletico Madrid ya fara bude kasuwa a...
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi. Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar da yanayin na zafi kan haifar a jihohi goma sha tara na ƙasar daga yankin arewa ta tsakiya da yankin gabashin ƙasar. Kan haka ne muka tuntuɓi likita domin ya yi mana ƙarin bayani game da cututtuka biyar da aka fi kamuwa da su a lokacin zafi da kuma hanyoyin kare kai. Sanƙarau – Dakta Hassan Ibrahim, likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha. Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018,...

China Ta Yi Gargadin Cewa Duniyar Zata Zama Ba Doka Da Oda Idan Amurka Ta Ci Gaba Da Yakin Kudaden Fito Da Ta fara
A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...

Kasar Chaina Ta Yi Gargadin Cewa Duniyar Zata Zama Ba Doka Da Oda Idan Amurka Ta Ci Gaba Da Yakin Kudaden Fito Da Ta fara
A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...
Sakataren watsa labarai na Fadar white House ta tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza kai tsaye. Tashar talabijin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto Karoline Leavitt tana fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya aiki Adam Boehler mutumin da yake wakiltansa a al-amuran fursinonin Amurka a waje, zuwa kasashen yankin kudancin Asiya don tattauna batun Amurkawa da suke hannun kungiyar Hamas a Zirin Gaza. Leavitt ta kara da cewa Amurkawa sun cancanci a shiga tattaunawa ko kuma a bi duk hanyoyin da suka dace don ganin, an kubutar da Amurka wadanda suka shiga hanun makiyansu a ko ina suke...
Hakika, kasar Sin ta nuna bajinta a kan habakar da take samu a fagen kere-keren mutum-mutumi musamman ma a yayin bikin bazara na shekarar 2025 inda aka jero wasu mutum-mutumi 16 suka gudanar da raye-raye masu kayatarwa a wani bangare na shagulgulan jajibirin bikin. Yadda mutum-mutumin suka rika kwarkwasa da rawa da juyi ya yi matukar birge ’yan kallo na ciki da wajen kasar. Bugu da kari, a karon farko, mutum-mutumi za su shiga a dama da su a wasan gudun fanfalakin da za a gudanar cikin watan Afrilu mai zuwa a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda ake sa ran mutum-mutumin nan da aka saka masa fasahar kirkirarriyar basira ta AI, Tian Kung wanda cibiyar bunkasa kere-keren mutum-mutumi masu...
Kasar Afrika ta Kudu, ta yi Allah wadai da yadda ta ce Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki a Gaza ta hanyar toshe agajin jin kai ga Zirin tun ranar Lahadi. Isra’ila na “amfani da yunwa a matsayin makamin yaki” a Gaza ta hanyar toshe inji Afirka ta Kudu a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fiyar yau Laraba 5. “Ta hanyar hana shigowar abinci a Gaza, Isra’ila na ci gaba da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,” in ji Pretoria, wacce dama tun tuni ta shigar da korafi kan Isra’ila akan kisan kiyashi a Gaza a gaban kotun duniya. Afirka ta Kudu ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta yi Allah-wadai da...
Sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, ta bayyana cewa saɓani ne ya shiga tsakanin matashin da mahaifiyarsa, wanda ya haifar da tashin hankalin. Majiyoyi daga unguwar sun ce matashin yana shaye-shaye, kuma mahaifiyarsa ta faɗa masa ya daina, wanda hakan ne ya fusata shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...

Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron inda ministocin harkokin wajen kasashen na G20 suka tattauna a kansu. Ministan harkokin wajen na kasar Afrika ta Kudu Ronal Ramola ya bayyana cewa duk tare da cewa babu wani babban jami’an gwamnatin kasar Amurka a taron amma taron ya gudana kamar yadda ake saba. Kungiyar G20 Taron kasashe masu arziki a duniya, wadanda suke da kasha 85% na tattalin arziki a duniya sannan suna...
Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas zai saki fursunonin ‘yan sahayoniyya guda 6 a madadin fursunonin Falasɗinawa 602 A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, a ranar Asabar, tare da bayyana sunayensu. A sakamakon haka, mamayar za ta saki fursunonin Falasdinawa 602: Falasdinawa 50 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne, wasu 60 daga cikinsu kuma an yanke musu hukunci mai tsawo, da kuma fursunoni 47 na Wafa al-Ahrar da aka sake kama su, bayan zaman gidan yari a baya. Haka...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila. An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu tsakanin Isra’ila da Hamas. Tun dai bayan cimma yarjejeniyar Hamas ta saki Isra’ilawa 22, a yayin da ita kuwa Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa sama da 1,100. A karshen matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta, za a yi musayar fursunonin Falasdinawa 1,900 da aka yi garkuwa da ‘yan Isra’ila su 33 da suka hada da matattu takwas. Ana dai ci gaba...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke ci gaba da bunkasa, za su ci gaba da bayar da shawarwarin ci gaba da gudanar da shirye-shirye na inganta karfin harkokin mulki. Shugaban ya bayyana cewa, wannan yunkurin zai sa a fi amfani da shawarwarin manyan Sakatarorin wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Sani Haidara ya kuma ce a matsayinsu na manyan masu gudanar da mulki, ya ba da tabbacin goyon bayansu...
Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran juyin juya halin musulunci ya fadar cewa a halin yanzu babu wani abunda HKI zata yi a gaza sai idan kungiyoyi masu gwagwarmaya suna sun abin ya faru, saboda kekkyawar riko da suka yiwa yankin. Imam Seyyed Ali Khamenei, ya yabawa kungiyoyin falasdinawa kan hadin kai da suka nuna a yankin da ya gabata. Ziyad al-Nakhalah, babban sakataren kungiyar Jihad Islami, ya bayyana cewa sun...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Hakan dai ya faru ne dalilin baiko da fitaccen mawaƙin ya yi da ’yar majalisar jiha mai wakiltar Egor a jihar Edo, Natasha Osawuru, a wani bidiyo da ya karaɗe soshiyal midiya. Ɓullar bidiyon ke da wuya mahaifiyar 2Face, Rose Idibia, ta fito a wani bidiyo tana roƙon duk wata uwa ta taya ta roƙon ‘yar majalisar ta karya asirin da ta yi wa ɗanta. Kalaman mahaifiyar tasa dai na da nasaba da rabuwar 2Face da matarsa Annie da har yanzu bai kammala ba a hukumance. Mahaifiyar tasa ta ce rashin haƙurin jiran aurensa ya rabu da tsohuwar matar tasa, da gaggawar neman auren ‘yar majalisar ne ya sanya ta gano cewa ɗan nata ba a hayyacinsa ya ke ba....
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai wa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a wannan Litinin ɗin. Aminiya ta ruwaito cewa, da misalin ƙarfe 12:36 na yau Litinin ce tawagar da Atikun ya jagoranta ta isa gidan tsohon Shugaban Ƙasar da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. Gwamnan Zamfara ya gindaya sharaɗin sulhu da ’yan bindiga Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke da takwaransa na Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal haɗi da ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Abdul Ningi. Bayanai sun ce an shafe tsawon sa’a ɗaya da rabi ana ganawar wadda aka yi ta...

Shugaban Kungiyar Hamas Yace: Iran Bata Gusheba Tana Taimaka Mana, Kuma Shirin Trump Na Kwace Gaza Zai Ya Lalace
Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar sa kuma tana ci gaba da taimaka mata, har’ila yau yana da yakini Iran zata ci gaba da taimakawa kungiyar Hamas har zuwa nasara. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta watsa jawabin Al-Hay kai tsaye daga birnin Tehran a safiyar yau litinin, inda ya yi Jawabi a dandalin Azadi dake tsakiyar birnin Tehran. Yace, farmakin ‘waadu Sadik na daya da na biyu duk...
Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma. Kamar dai a makon da ya gabata, za a yi musaya ta biyar a wurare biyu a zirin Gaza a jere inji rahotanni. A maimakon haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da 18 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ciki har da wasu fitattun mutane irin su Iyad Abu Shidam, wanda Isra’ila ta yankewa hukuncin daurin rai da rai a Beersheva a shekara ta 2004. Bayanai sun ce kimanin 111 daga cikin wadannan...
A wani rahoto na ibtila’i da ya afku a unguwar Ukubie da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa inda wata mata mai suna Madam Stella ta jefa ‘yarta ’yar shekara shida mai suna Rachael a cikin kogi saboda fushi. A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da gargaɗin da mahaifiyarta ta yi mata. Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa An sace tsohon Shugaban Hukumar NYSC, Janar Tsiga “Lokacin da mahaifiyar ta samu ’yarta a bakin kogin, sai ta fusata. Duk da gargaɗin da aka yi mata na ƙauracewa kogin, Rachael ta ƙi, wanda hakan ya sa mahaifiyar tashin hankali ta fusata,” in ji wani ganau. A cikin fushi,...
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin hajji. Da yake jawabi ga al’ummar yankin, Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata cikin gaggawa. “Dole ne mu yi wa wadanda suka rasu addu’a da kuma baiwa iyalansu ikon jure wannan rashi, Allah ya sa wannan ya zama na karshe a cikin irin wannan mummunan lamari a cikin al’ummarmu,” inji...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Sanya Sheikh Na’im Kasim A Matsayin My Wakiltarsa A Kasar Lebanon
A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon. Sheikh Qasim dai ya taka rawar a zo a gani wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...

Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya kasance daga cikin shirye-shiryen kasar na shirin kare sararin samaniyar kasar ta sama. Labarin ya kara da cewa a wannan karom ma sojojin Iran da kuma dakarun juyin juya halin musulunci zasu yi atisayen hadin giwa ne don gwada karfin sojojin kasar da kuma IRGC na kare sararin samaniyar kasar. Kafin haka dai sojojin sun gwada karfinsu a bangarori daban daban na sojojin kasar don...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga bakin masana gwagwadon lokacinda muke da shi. Dafan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///..Madalla, masu sauraro, shirimmu nay au za iyi Magana dangane da ‘abinda ya sa ranar 9 ga watan Day ko kuma 29 ga watan Decemba yake da matukar muhimmanci ga Iraniyawa ko JMI?. A nan Iran ranar 9 ga watan Day na ko wace shekara tun shekara ta 2009, wanda...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin makaman tsaro a yankin da ke yammacin kasar, a karon farko sun nuna wasu jiragen saman yaki maras matuki ciki da aka kera a cikin gida masu tsnanin karfin munanan hare-hare irin na kunan bakin wake kirar “Ababil” da “Arash-2” da dakarun sojin kasar Iran zasu yi amfani da su wajen kare tsaron kasa duk lokacin da ya dace. Jiragen saman “Ababil” ne suka jagoranci...
Wani uba a ƙasar Pakistan ya kashe ɗiyarsa matashiya bayan ta saka wasu faifan bidiyo da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su dace ba a manhajar sada zumunta ta TikTok, in ji ‘yan sanda a ranar Alhamis. Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin wanda aka ce yana da shekara 50 a duniya, ya dawo da iyalansa daga ƙasar Amurka kwanan nan, domin su zauna a birnin Ƙuetta da ke Kudu maso Yammacin Pakistan. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Jirage sun yi karo a sararin samaniya a Amurka Mahaifin, wanda yanzu haka yake tsare, ya amsa laifin harbe ’yarsa a farkon wannan makon bayan ta ƙi sanya suturar da ta dace kuma ta daina...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa. Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20 da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26. Ga jerin rashin ƙoƙarin ƙungiyar a shekarun baya: Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94. United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...