Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Sanya Sheikh Na’im Kasim A Matsayin My Wakiltarsa A Kasar Lebanon
Published: 6th, February 2025 GMT
A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon.
Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon.
Sheikh Qasim dai ya taka rawar a zo a gani wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA