Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Published: 4th, February 2025 GMT
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya kasance daga cikin shirye-shiryen kasar na shirin kare sararin samaniyar kasar ta sama.
Labarin ya kara da cewa a wannan karom ma sojojin Iran da kuma dakarun juyin juya halin musulunci zasu yi atisayen hadin giwa ne don gwada karfin sojojin kasar da kuma IRGC na kare sararin samaniyar kasar. Kafin haka dai sojojin sun gwada karfinsu a bangarori daban daban na sojojin kasar don tabbatar da cewa a shirye suka su kare JMI daga makiyanta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp