Wani ya kashe ’yarsa saboda bidiyon TikTok a Pakistan
Published: 30th, January 2025 GMT
Wani uba a ƙasar Pakistan ya kashe ɗiyarsa matashiya bayan ta saka wasu faifan bidiyo da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su dace ba a manhajar sada zumunta ta TikTok, in ji ‘yan sanda a ranar Alhamis.
Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin wanda aka ce yana da shekara 50 a duniya, ya dawo da iyalansa daga ƙasar Amurka kwanan nan, domin su zauna a birnin Ƙuetta da ke Kudu maso Yammacin Pakistan.
Mahaifin, wanda yanzu haka yake tsare, ya amsa laifin harbe ’yarsa a farkon wannan makon bayan ta ƙi sanya suturar da ta dace kuma ta daina sanya bidiyon da ‘yan uwanta suka ɗauka a matsayin “bidiyon marasa mutunci” akan TikTok, in ji Baloch.
‘Yan sanda na ɗaukar lamarin a matsayin kisan gilla.
Kimanin mata 1,000 ne ake kashe wa a Pakistan ta hannun danginsu, uba, ’yan’uwa da ’ya’yansu bisa zargin ceto mutuncin iyali, a cewar Hukumar Kare Haƙƙoƙin Ɗan Adam ta Pakistan (HRCP).
Kungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International ta ce waɗanda suka kashe a mafi yawan lokuta suna tserewa hukunci saboda wata doka ta Musulunci a cikin dokokin da ke bai wa ’yan uwan waɗanda aka kashe damar yafe wa wanda ya aikata laifin.
Pakistan ta amince da wata doka a shekara ta 2016 don kawar da wani ɓangare na magana mai cike da cece-kuce, amma hakan bai kai ga dakatar da wannan ɗabi’ar ba, a cewar HRCP.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya.
Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jinjirin watan ba a ranar Lahadi.
Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da UkraineHakan na nufin yau Litinin, 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.
A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Asabar da ta gabata ce Fadar Sarkin Musulmin ta ba da umarnin duban watan na Zhul Qi’ida.