2025-05-23@21:08:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 991
«kiwon lafiyar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta baiwa mutane 311 tallafi a karkashin shirin tallafa wa mata da matasa kan harkokin noma da nufin bunkasa dogaro da kai da ’yancin tattalin arziki a fadin jihar. Da take jawabi a yayin kaddamar da gagarumin bikin a Gusau, babban birnin jihar, Hajiya Huriyya ta jaddada kudirinta na gwamnati na bunkasa sabbin manoma, ‘yan kasuwa, da matasa da suka samar da su don kawo sauyi a fannin noma. Ta bayyana cewa daga cikin 311 da suka ci gajiyar tallafin, 201 mata ne yayin da 110 kuma samari ne, wadanda dukkansu za su samu cikakken goyon baya a karkashin shirin. “Kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai samu jarin...
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan zaman lafiya a duniya bas u yi hakan da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana fadar haka a jiya talata ya kuma kara da cewa a halin yanzu majalisar tana tafiyar da ayyukan zaman lafiya har 11 a kasashen duniya wadanda suka hana da nahiyar Afirka Asia da kuma turai. Guterres ya kara da cewa majalisar tana da...
Amurka ta sanar da cimma wata yarjejeniya makamai mai tsoka ta Dala biliyan 142 da Saudiyya. Wanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, ke gudanar da ziyara a kasar Saudiyya irinta ta farko a ketare tun bayan sake hawansa karagar mulki. Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “mafi girma a tarihi. ” Wannan yarjejeniya, wacce wani bangare ne na babban kunshin alkawurran saka hannun jari – da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 600, a cewar gwamnatin Amurka – za ta ba wa masarautar Saudiyya damar sayen “kayan aikin soja daga kamfanonin tsaron Amurka goma sha biyu,” musamman a fannin tsaron sararrin samaniya, makamai masu linzami, tsaron teku da tsarin sadarwa. A wani...
Iran ta yi tir da sabbin takunkuman da ta danganta da na rashin adalci da Amurka ta kakaba mata. Amurka dai ta kakaba wa Iran sabbin takunkuman, ne duk da ci gaba da tattaunawar nukiliyar da ake yi tsakanin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ayyana wasu ‘yan kasar Iran guda uku da wani kamfani mai suna Fuya Pars Prospective Technologists, bisa zargin cewa suna da hannu wajen gudanar da bincike da kuma ayyukan da suka shafi makaman nukiliya. Amurka, ta ce takunkumin ya shafi toshe duk wasu kadarori na mutanen a Amurka tare da hana mu’amalar kasuwanci da su. Sabon takunkumin ya zo ne kwana guda bayan Iran da...

Gwamna Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi. “Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri. “Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141. “Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala,...
An zabi Comrade Isma’il Ibrahim Dutse na ma’aikatar yada labarai a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridu NUJ ta kasa reshen jihar Jigawa ba tare da hamayya ba. A lokacin da yake sanar da sakamakon zaben, mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyya ta daya wato Zone A, Comrade Tukur Umar Muhammad ya ce an kuma zabi Nura Sani Bello da Najib Umar da Aminu Umar Shuwajo ba tare da hamayya ba. Tukur ya ce Aisha Abba Ahmed ta kamfanin dillancin labarai na kasa NAN dake Dutse ta samu nasara da yawan kuri’u 46, shi kuma Abdullahi Mukhtar ya sami kuri’u 34, yayin da Larai Musa na NTA ta sami kuri’u 14. Tukur Umar, ya bayyana...
Wasu ma’aikatan lafiya biyu sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan motarsu ta taka bom a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri a Jihar Borno. Ana zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa bom din a wani hari da kungiyar ta kai a kan babbar hanyar a ranar Litinin. Shaidu sun bayyana cewa, wadanda suka mutun suna zaune ne a gaban motar jigilar mangoro, kirar Toyota Hiace da ta dauko su daga Damboa zuwa Maiduguri. Sun kara da cewa tashin bom din ya haifar da sabuwar damuwa game da lafiyar matafiya a kan hanyar. Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Ya kashe abokinsa...
A yau Talata ne dai aka bude taron karawa juna sani karo na 31 a birnin Mashhad wanda shi ne karo na 31 da zai mayar da hankali akan yadda za a ci moriyar wannan fasaha ta fuskokin zaman lafiya. Hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ce dai ta tsara wannan taron kara wa juna sanin wanda ya sami halartar masana wannan fage. Wasu batutuwa da za a tattauna a wurin taron sun kunshi; Bututun tace sanadarin Uranium, shi kanshi makamashin da kuma hanyoyin tafiyar da da kula cibiyoyin dake aikin tace da sarrafa makamashin na Nukiliya.
Jami’an tsaro sun killace wajen da lamarin ya faru, kuma suna ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Musulunci kan zargin yi wa matar maƙwabcinsa dukan kawo wuƙa a Jihar Kano. Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun da ke zama a unguwar Kurna Asabe cewa wanda ake zargin ya kuma ji wa matar auren munanan raunuka. Ya yi wa matar wannan aika-aika ne bayan wata taƙaddama, inda ya ji mata munanan raunuka a fuska da wasu sassan jikinta. Alƙalin kotun, Khadi Alhaji Jibrin Ɗanzaki, ya ba da umarnin tsare mutumin a gidan yari sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Mayu. Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano Matashi ya kashe saurayin ƙanwarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasin ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai don takurawa da kuma matsin lambar da takewa gwamnatin kasar Lebanon don kawo karshen kungiyar ba. Tashar talabijin ta Almanar ta nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a jiya litinin, a wanijawabinda ya yi ta tashar talabijin ta AL-Amnar na kungiyar don tunawa da babban kwamandar kungiyar Sayyed Mustafa Badreddin wanda yayi shahada shekaru 9 da suka gabata. Sheikh Kasim ya kara da cewa kungiyar tana kan al-kawalinda na tsagaita budewa juna wuta duk tare da cewa HKI ta keta wannan yarjeniyar har sau 3000. HKI dai ta amince da tsagaita budewa juna wuta bayan fafatawa da kungiyar Hizbullah na tsawon watanni 14,...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya. Trump zai ziyarci wasu kasashen larabawa a yankin, wadanda suka hada da Qatar da HDL da kuma Turkiya inda ake saran zai tattauna dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine tare da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyid Urdugan. Shugaban yana zuwa yankin ne a dai-dali lokacinda HKI ta ci gaba da kissan kiayashi ga Falasdinawa a Gaza da kuma hana abinci shiga Gaza. Shugaban ya sami labarin saken wani ba’amerike mai suna Edan Alezander wanda yake tsare a hannun kungiyar Hamas tun shekara ta 2023. Kungiyar Hamas...
Kasar Sin ta harba wani rukunin taurarin dan adam daga cibiyar harba tauraron na Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar. An harba taurarin ne jiya Lahadi da misalin karfe 9:27pm agogon Beijing, bisa amfani da samfurin rokar Long March-6 da aka yi wa ‘yan gyare-gyare. A cewar cibiyar ta Taiyuan, rukunin taurarin mai suna Yaogan-40 02, ya shiga da’irarsa cikin nasara. Za a yi amfani da taurarin ne wajen gwaje-gwajen fasahohi da gano yankuna masu tasirin haduwar maganadisu da lantarki. Aikin na jiya shi ne karo na 574 da aka yi amfani da samfurin rokar Long March. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kashe naira biliyan 2 da miliyan 300 domin sayo na’urar binciken cututtukan zuciya (cardiac catheterization machine) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato. Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja. A cewar ministan, wadannan kayan aiki na zamani za su taimaka matuka wajen aikin gano cutar da kuma warkar da cututtukamasu alaƙa da zuciya. Ya bayyana cewa hakan wani mataki ne na gwamnatin tarayya don ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya na musamman a yankin Arewa maso Yamma da kuma rage bukatar zuwa ƙasashen waje...
Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar da Siriya daga cikin sahun masu fada da makirce-makircen yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta hanyar kulla kyakkyawar alaka da su, da janyewa daga duk hakkokin kasar Siriya da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta mamaye na Siriya a baya-bayan nan. Manufar samar da sabuwar gwamnatin masu da’awar jihadi, kamar yadda aka sani, ita ce tabbatar da tsaron babban sansanin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya,...
Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na kungiyar Rapid Support Forces masu aikata laifuka suka kai hari kan gidan yarin Al-Obeid. Al-Aiser ya bayyana cewa: Harin da aka kai ya hada da asibitin birnin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane musamman majinyata masu yawa tare da raunata wasu kimanin 50, wadanda dukkansu fararen hula ne, yana mai cewa wannan yana daga cikin manyan laifukan yaki. Ministan ya kara da cewa: “Abin da ya faru...
‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi. A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19. Taken da aka bai wa taron karo na 19 shi ne: “Kafa Gwamnatoci masu hikima a kuma cibiyoyi masu karfi a matsayin ginshikin jajurcewa.” Tawagar ta Iran dai wacce Ruhullah Mutafakkir Azad yake jagoranta, ta kuma kunshi Sara Fallahi, Sayyid Yahya Sulaimani, da Muhammad Mahdi Shahriyari. Taron zai ci gaba har zuwa ranar 15 ga watan nan na Mayu da ake ciki, kuma tawagar ta Iran za ta gabatar da jawabi a...
Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar ma’aikatan jiniya ta duniya, Daraktan riƙo na Hukumar ta WHO a Afirka, Chikwe Ihekweazu, ya ce ficewar tasu za ta nakasa harkokin kiwon lafiyar da ake riritawa a nahiyar. Ihekweazu ya cigaba da cewa wannan ɓangare na masu aikin jinyar na da matuƙar muhimmanci ga ɗaukacin al’umma, don haka bashi kulawa, abu ne da ya dace, domin zai ba da gudunmawa ga cigaban ɓangaren lafiya,...
Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata. Sanarwar ta PKK ta kuma kunshi cewa;Jam’iyyun siyasa na kurdawa za su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa domin bunkasa tsarin demokradiyya da sake gina al’ummar Kurdawa.” Haka nan kuma PKK ta ce, da akwai alakar a sake Shata salon alakar Kurdawa da Turkiya. A martanin da jam’iyyar dake Mulki a Turkiya ta fitar, ta bayyana cewa; Zartar da matakin da kungiyar...
Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa. Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare...
Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’an kungiyar tana fadar haka a jiya Lahadi. Khalil Al-Hayya shugaban kungiyar ya bayyana cewa Hamas ta amince da hakan ne bayan wata tattaunawa da Amurka kan batun. Ya kuma kara da cewa kungiyar tana son a fara tattaunawa da gaske tsakaninta da HKI ta hanyar masu shiga tsakani, don kawo karshen yakin da kuma ficewar sojojin yahudawa gaba daya daga...
Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin da aka sauya ƙwayoyin halittarsa. Hakan dai na faruwa ne duk da bayanan da wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance. Tuni dai wasu masanan, waɗanda suka shirya wani taron bita ga manema labarai, suka yi gargaɗi game da illolin irin. Ko mece ce gaskiya game da amfani da wannan iri na GMO? NAJERIYA A YAU: Abin ya sa aka kasa kawo ƙarshen Tamowa a Arewa Maso Gabas DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannann rana zai...
Ɓallewar ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) bayan kwashe fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakaninta da su, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga ci gaba da kasancewar kungiyar ta Ecowas. A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne kasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta suka sanar da ECOWAS a hukumance dangane da buƙatar ficewar tasu. Muna bayan Tinubu a Zaɓen 2027 — Patience Jonathan Muhawarar da ta ɓarke kan saya wa Sarkin Kano motocin naira miliyan 670 To sai dai bisa dokokin kungiyar, kasashen na buƙatar sanar da ita shekara guda kafin amincewa da ficewar. Bayan wa’adin da kungiyar ta deba musu...
Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar. Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan, babban kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai ziyara a kasar Nijar a ran gadinsa a Afrika. A ziyarar tasa ya gana da firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangaré, da ministan harkokin cikin gida Janar Mohammed Tomba, da shugaban ‘yan sandan Nijar Janar Omar Chiyani. A yayin ganawar, M. Zein ya jaddada karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda a tsakanin kasashen biyu inda ya ce: “A shirye muke mu yi amfani da gogewar da ‘yan sandan Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke da ita a dukkan...
Tsohon jami’in harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Josep Borrell ya yi kakkausar suka ga kungiyar kan rashin daukar mataki game da kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi a zirin Gaza yana mai cewa “rabin bama-baman da aka jefa a zirin Gaza ne muke kawowa.” Da yake jawabi bayan karbar lambar yabo ta Carlos V ta Turai da ke Spain, Josep Borrell ya ce nahiyar Turai na shaida kawar da wata kabila tun bayan karshen yakin duniya na biyu, domin gina wurin yawon bude ido bayan korar da Falasdinawa. Ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin kisan kiyashi, ya kuma ce kungiyar EU, duk da cewa tana da hanyoyin nunna adawa da kuma kawo karshen ayyukan Isra’ila,...
Kazalika, sanarwar ta sanar da cewa, ana bukatar kwamtin ya sanya ido wajen ganin an gabatar da kasidu da alkalan da za su yi hunci kan bayanan da za a tattauna a wajen taron da baje kolin kanana da matsakaitan sana’oi da za a yi a wajen taron tare da kuma mika kyaututtuka ga ‘yan kasuwar kasar da suka dace, a wajen taron. Acewar sanarwar, Mataimakin Shugaban Ma’aikata da ke a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne, zai shugabaci kwamtin. Sauran ‘ya’yan kwamtin sun hada da, Ministar Ma’aikatar Kasuwanci da zuba hannun jari Dakta Jumoke Oduwole; Ministan sadarwa da kere-kere da kuma tattalin arziki na fasahar zamani Dakta Bosun Tijani; Ministar yawon bude ido da kirkiren tattalin...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta jadada cewa ko kadan sojojin kasar ba su keta tsagaita wutar yaki da Indiya ba. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta fitar ta ce; kasar tana ci gaba da aiki da tsagaita wutar yaki wacce aka sanar da ita, kuma sojojin kasar sun kai zuciya nesa, duk da cewa Indiya ce ta keta wutar yakin. Saanrwar da Pakistan ta biyo bayan zargin da Indiya ta yi wa kasar ne cewa tana keta yarjejeniyar wutar yaki bayan an cimma yarjejeniya a kan hakan. Jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Indiya Bigram Maisari ne ya bayyana hakan a wani taron manema labaru da ya gabatar a yau, sannan ya kara da cea;...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana fuska biyu na kasashen yamma, dangane da shirin magakamashin nukliya na kasarsa, da kuma yadda basa magana kan makaman nukliya wanda HKI take da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar, a birnin Doha na kasar Qatar a inda yake halattan taron JMI da kasashen larabawa a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa, wannan rashin adalci ne a fili sannan nuna fuska biyu, Iran wacce babu tabbas kan shirinta na makamashin nukliya na soje ne, an cika duniya da cewa tana son ta mallaki makaman nukliya amma ga HKI wacce aka tabbatar da cewa tana da makaman na nukliya, babu...
Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya sun gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin. Taron wanda ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, inda suka tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin. An kama matashi da kawunan mutanen a Legas Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da Filato da Yobe da Jigawa da Kogi da Adamawa da kuma Zamfara na cikin waɗanda suka halarci taron. A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed...
Kasashen Indiya da Pakistan sun tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan shafe kwanaki suna yi wa juna luguden wuta da makaman atilare. Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da cewa ƙasashen biyu maƙwabta sun amince su cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta nan take bayan shafe dare guda ana tattaunawa. Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina “Bayan doguwar tattaunawa da Amurka ta yi na a cikin dare, ina farin cikin sanar da cewa Indiya da Pakistan sun amince da tsagaita wuta cikin gaggawa. “Ina taya ƙasashen biyu murna a kan amfani da hankalinsu da kuma basira,” kamar yadda Trump ɗin ya...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna. A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana...
Shugaban kasar Amurka ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, wanda Amurka ta shiga tsakani wajen kulla ta. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba, da aka samu, inda ya yaba da amfani da hankali da basirar da kasashen biyu suka nuna wajen daukar wannan mataki. Ya kuma jaddada cewa, dogon tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu ya haifar da wannan yarjejeniya, wanda ke nuna muradin bangarorin biyu na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan sanarwar...
Farfesa Lawan Abubakar tsohon jagora na ASUU shiyyar Bauchi shi, ya wakilci wanda ya kira taron, ya ce yadda aka yi zaben wadanda suka cancanci samun tallafin kuma an yi amfani da adalci tsakanin jinsin mace da namiji, suma wadanda suke da bukata ta musamman, saboda a taimaka masu wajen bunkasa iiminsu. Ya ce a shekaru biyu da suka gabata kungiyar ASUU ta kashe fiye da Naira milyan 164.kudaden bada tallafin karatu ga wadanda ba su da halin biyan kudin a Jami’oin da ake da su a fadin tarayyar Nijeriya. Ya ce“Kungiyarmu ta ci gaba da amfani da kuma kula da lamarin bayar da tallafin karatu na Gani Fawehinmi,tsawon shekrun da suka gabata.Ba kawai mun tsaya bane sai kawai ta...
Jami’in ya kara da cewa, wannan ya dace da muhimman muradun Indiya da Pakistan, kuma zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, sannan kuma shi ne fata na gama-gari na kasashen duniya. Kuma kasar Sin na son ci gaba da taka muhimmyar rawa mai ma’ana a wannan fanni. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gidauniyar attajirin ɗan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ta yi wa masu fama da cutar gwaiwa da taruwar ruwa a wasu sassan jiki fiye da 12,300 tiyata kyauta. Da yake yi wa wakilin bayani, Malam Husaaini Kabir, mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar ne ya tabbatar da hakan a Katsina, a lokacin ƙaddamar da aikin kashi na biyu. Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso Kabir ya bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da aikin tiyatar da bayar da magani kyauta a duk bayan watanni uku tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2013. Ya ƙara da cewa, “majinyata masu rauni...
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki ’yan siyasar da ke sauya sheƙa daga jam’iyyar da a ƙarƙashinta suka samu nasarar lashe zaɓe zuwa wata. Kwankwaso ya bayyana lamarin a matsayin cin moriyar ganga, yana mai cewa hakan babban kuskure ne a siyasance. HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025 Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Miller Road a Kano yayin da yake karɓar wasu ’yan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa NNPP daga Ƙaramar Hukumar Takai. Kwankwaso ya ƙara jaddada irin juriya da haɗin kai da ke tafiyar Kwankwasiyya duk kuwa da cewa an ta ƙoƙarin ganin an kawar da hankalin mabiya....
Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza. Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad Fu’ad dulaibh, da matarsa Hindu, da ‘ya’yansu Ahmad, Hamzah, da Abdulazizi. Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren ta jirgin sama maras matuki a unguwar “Tuffah” dake birnin Gaza, da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. Su ma jiragen ruwan HKI sun kai wasu hare-haren munanan a garin Rafah da ya yi sanadiyyar shahadar Muhammad Sa’id al-Burudawil. A tsakiyar birnin Gaza, ma dai...
Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar da su yi taro. Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya. Ita dai Majalisar kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya da kuma manufofin kasa na koli, ta kunshi manyan kwamandojin soja, da fararen hula, aikinta kuma shi ne kula da manyan batutuwa da su ka shafi kasa daga ciki har da siyasar makaman Nukiliya da kuma makamai masu linzami.An kafa wannan majalisar ne dai a 2000. Tashar talabijin din “Sama News” ta bayar da labarin dake cewa; Mahalarta taron za su yi bitar halin da...

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda
Na yi wannan wannan ziyara ne saboda shaukin da nike da shi a kan abin da ya shafi kishin kasata Nijeriya, da kuma neman hadin kan kasashen Afirika ta yamma mu zama tsintsiya madaurinki daya,da son zaman lafiya da ci gaban Dimokaradiyya. Kazalika, na yi wannan rangadi ne domin murnar cikar kungiyar ECOWAS shekara 50 da kafuwa. Kasan an kafa kungiyar ne ranar 28 ga watan Mayu,1975 bana kungiyar za ta cika shekaru 50. To kasancewa shekaru 50 sun wuce wasa na ga cewa, kungiyar ta cancanci a yaba mata, kuma a kara matakaimi da azama. Kuma za ka yarda da ni idan na ce ma cikin wadannan shekaru 50, Kungiyar ta taka muhimmiyyar rawa ta a zo a gani...
A sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkar yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya bayyana cewa a jawabin sa na buɗe taron, ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda haɗin kai ke ƙaruwa a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai a cikin gwamnatin. Ya ce haɗin kan da daidaiton manufa sun ƙara inganta isar da saƙo da kuma fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu. Ministan ya yaba da yadda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da shugabannin hukumomin yaɗa labarai da kuma mataimakan shugaban ƙasa a ɓangaren watsa labarai da dabarun sadarwa. Ya ce wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen tabbatar da cewa saƙonnin gwamnati suna...
A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta. “Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.” Bayanin hakan ya...
Kasashen NIjar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu a bangarori da dama. Bangarorin sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a yayin ganawar data wakana tsakanin ministan harkokin cikin gida da tsaron jama’a da wata tawagar Iran karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar tsaron kasa Birgediya Janar Ahmad Rezaei RADAN. A yayin wannan zama Nijar da Iran sun amince da kafa kwamitin kwararru domin yin musayar ra’ayi lokaci-lokaci da karfafa hadin gwiwa. Nijar da Iran, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman a fagen yaki da ta’addanci, da manyan laifuffukan kasa da kasa, tsaron iyakoki, da kuma shige da fice ba bisa ka’ida ba.
Wasu daliban jami’a da ke shirin tafiyar aikin yi wa kasa hidima NYSC sun rasu a wani harin da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka kai musu a yankin Gbarabtoru-Ekpetiama, Karamar Hukumar Yenagoa. Matasan biyu da suka kammala karatunsu a Jami’ar Niger Delta (NDU), Amassomma, sun rasu ne bayan da gungun wasu mutane da ke wake-waken kungiyar asiri a cikin wata mota suka kai musu hari da adduna. Kwamandan Kungiyar ‘Yan Banga (VGN) na Jihar Bayelsa,Tolummbofa Akpoebibo Jonathan ya ce, daya daga cikin samarin ya yi kokarin tserewa, amma maharan suka bi shi suka kama shi suka sassare shi. Ya bayyana cewa da misalin karfe 11:00 na daren ranar Alhamis ne, abin ya faru kuma matasan biyu biyu sun...
Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirerren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da dala biliyan...
Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
Minista Tuggar ya bayyana cewa, kasar Cuba ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da ‘yancin kai ga wasu kasashen Afrika a lokacin da ake gwagwarmaryar kwato ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekkarun 60s, 70s, 80s da 90s. “Cuba da Nijeriya sun yi aiki tare wajen yaki da ‘yan mulkin mallaka a kasashen Angola, Namibia, Afrika ta Kudu da Zimbabwe” in ji shi, ya kara da cewa, wannan sabon yarjejeniyar za ta karfafa hadin kai a bangarorin kimiyya da fasaha, bincike da kuma samar da ci gaba mai dorewa. A nasa tsokacin, Ministan harkokin waje na Cuba, ya ce, dangantakar da ke tsakanin Cuba da Afrika mai karfi ne, ya kuma gode wa Nijeriya a kan goyon bayan da ta...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa. Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kuma ce, a baya, ba a Kallon laifuka irin wadannan kai tsaye ta talbijin amma a yanzu ana Kallon ta akwatin talabijin. Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi,...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a taron da aka fara gudanarwa a yau a makarantar Darushafia dake birnin Qom. Taron na Qom yana Magana dangane da “Makarantun Hauza a Qum, Juyin juya halin musulunci a Iran da kuma Gwagwarmaya’. Sheik Kasim ya kara da cewa mutanen kasar Lebanon sun fara gwagwarmaya ne bayan gwamnatin HKI ta mamaye kasarsu, sannan bayan sun sami jagoranci da tunanin Imam Khumaini (q)...

An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet
An gudanar da taron musayar al’adu da cudanyar al’umma na murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya na jama’ar kasar Sin a kan zaluncin kasar Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kamfanin gidajen talabijin da rediyo na kasar Rasha suka shirya a birnin Moscow. An karanta wasikun taya murna daga shugaban kasar Sin Xi Jinping da na Rasha Vladimir Putin a wajen taron. A jawabinsa, babban darektan CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, yayin da bikin shekarar al’adun Sin da Rasha ya kankama, bari mu dauki ruhin sakon wasiku na taya murna a matsayin jagora, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu....
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar. Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar tare da batanci da haddasa rikici. Sanata Usman ta Kara da cewa, Abure yana aikata laifufuka wanda suke kalubalantar mutunci Jam’iyar da kuma yin karo da manufofin dimokuradiyya. Don haka, majalisar zartaswa ta Jam’iyar ta dauki matakin kaddamar da bincike kan wannan munanan halayya. Bugu da Kari Sanata Nenadi Usman tace majalisar zantaswa na Jamiyar Labour bayan dogon nazari akan hukuncin da kotun...
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar. Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar tare da batanci da haddasa rikici. Sanata Usman ta Kara da cewa, Abure yana aikata laifufuka wanda suke kalubalantar mutunci Jam’iyar da kuma yin karo da manufofin dimokuradiyya. Don haka, majalisar zartaswa ta Jam’iyar ta dauki matakin kaddamar da bincike kan wannan munanan halayya. Bugu da Kari Sanata Nenadi Usman tace majalisar zantaswa na Jamiyar Labour bayan dogon nazari akan hukuncin da kotun...
Houthis sun kai hari kan babban filin jirgin sama na Isra’ila kusa da Tel Aviv a ranar Lahadi, a wani ɓangare na yaƙi da ‘yan tawayen ke yi kan Isra’ila, a matsayin tallafin ga Falasdinawa a Gaza. Iran ta musanta cewa ta goyi bayan Houthis a harin. Duk da haka, Isra’ila ta mayar da martani kan Houthis tare da kai hare-hare kan filin jirgin sama na babban birnin Sana’a da ke hannun ‘yan tawayen da kuma tashoshin wutar lantarki a kewayen birnin. Amurka da Houthis sun cimma yarjejeniyar sasantawa, kamar yadda Oman ta sanar a ranar Talata, inda ta ce yarjejeniyar za ta tabbatar da ” ‘yancin kewayawa” a cikin bahar maliya, inda ‘yan tawayen suke kai hare-hare kan jiragen...

Yemen Ta Jaddada Cewa: Idan Amurka Ta Kai Mata Hari, Tabbas Yarjejeniyar Kawo Karshen Bude Wuta Tsakaninsu Zata Ruguje
Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta. Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka...
Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin. Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin...
Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu. Kazalika, ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kasance cikin daidaito da sama da dalar Amurka tiriliyan 3.2 na tsawon watanni 17 a jere. Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da...
A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi. Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai. Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.” Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu. Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin...
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta “Hauza” wanda aka yi a yau a birnin Kum, anan Iran, ya bayyana cewa: Aiki mafi muhimmanci na makarantar addini shi ne isar da sakon addinin musulunci domin gina sabon ci gaba na addinin musulunci. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa da akwai ayyuka masu yawa da suke na cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza ne da sun kunshi bayar da jawabi akan sabbin batutuwa na zamani da suke bijirowa, ruhin ci gaba, tsarkake zukata, da kuma siffa ta juyin juya hali.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa daga...

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa. Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka...
A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing domin kai ziyarar aiki a kasar Rasha da kuma halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tarayyar Soviet a birnin Moscow, bisa gayyatar da shugaban kasar Vladimir Putin na Rasha ya yi masa. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar . Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin...
Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari. Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza. Yarjejeniyar da Amurka ba ta da alaka da matsayinmu na goyan bayan Gaza, inji Abdul-Salam. A jiya ne masarautar Oman ta sanar cewa Amurka da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtshis a Yeman suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi a baya-bayan...
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a fannin tsaro, ko kuma tana neman ƙawancen da zai fi dacewa da manufofinta na cikin gida da waje. Duk da haka, ƙwararru na ganin cewa hakan na iya janyo sabon matsin lamba daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin yanki kamar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat ɗinta a ƙasar Gulf ɗin. Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi Inter Milan ta kori Barcelona daga Gasar Zakarun Turai Ya zargi UAE da take hurumin Sudan ta hanyar “ƙawarta”, wato Rundunar RSF, wacce ke yaƙi da sojojin Sudan tun watan Afrilu 2023. “Dukkan duniya ta shaida, fiye da shekaru biyu, laifin kai hari...
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullahi ya bayyana cewa: Sanarwar Trump gazawa ce ga Netanyahu, kuma dole ne fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi murabus daga kan mukaminsa. Ya kara da cewa: “Za su fara tantance sanarwar da Trump ya bayar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen,” bisa la’akari...
Shugaban tawagar kasar Yemen, Mohammed Abdul Salam, ya sanar da cewa ayyukan Yemen na tallafawa Gaza ba zai tsayawa ba Shugaban tawagar shiga Tsakani na kasar Yemen Abdul Salam ya bayyana cewa: Yemen ta samu sakon bukatu daga Amurka ta hanyar masarautar Oman, kuma wanda ya sauya matsayinsa Amurka ce, ba Yemen ba. Ya kara da cewa ikirari da Amurka ta yi na mika wuya, yana nuni ne ga gazawa, saboda Amurka ba zata iya kare jiragen ruwan haramtaciyar kasar Isra’ila daga hare-haren Yemen ba. Abdul-Salam ya kara da cewa: Fahimtar farko da aka samu tsakanin Amurka da Yemen ba ta da wata alaka da matsayar Yemen kan goyon bayan Gaza, yana mai nuni da cewa za a samu ci...
Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kiran hanzarta dawowar ma’aikatan ofishin jakadancin Sudan gida daga Abu Dhabi. Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron Sudan ya bayyana cewa: Fiye da shekaru biyu, daukacin duniya take bibiyar laifuffukan wuce gona da iri kan kasar Sudan, da tabbatar da tsaron yankunanta, da tsaron ‘yan kasarta daga hadaddiyar daular Larabawa ta hanyar wakiliyarta na cikin...
Da yake tsokaci game da wasan na karshe na jiya, Mark Williams daga yankin Wales, ya ce Zhao abokin karawa ne mai hazaka. Don haka ba abun da zai fada game da shi illa jinjinawa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata ƙungiya mai rajin kare muradun al’ummar Hausawa a Nijeriya mai suna Kungiyar Hausawan Nijeriya ta tsaya kai da fata cewa dole a ƙyale Hausawa su kafa ƙungiyarsu kamar kowacce ƙabila tun da dai doka ba ta hana su ba. Martanin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da masu kiran ke shan sukar cewa suna ƙoƙarin rura wutar ƙabilanci ne a Arewacin Nijeriya Najeriya, musamman a daidai lokacin da yankin ke buƙatar haɗin kai domin magance matsalolinsa. Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus To sai dai ƙungiyar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a ƙalubalanci yunƙurin nasu ba, tun da dai ’yan ƙabilar Yarabawa suna da ƙungiyar Afenifere,...
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta ARD-FCTA, Dokta George Ebong, da babban sakataren kungiyar, Dr. Agbor Affiong, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnati ta dauka na cire ma’aikatan da abin ya shafa daga cikin tsarin albashi ba tare da sanarwa ko tuntuba ba, inda kungiyar ta ya bayyana matakin a matsayin “rashin gaskiya da adalci”. A cewar kungiyar, ma’aikatan da aka kora da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya, masu kula da bangaren magunguna, da masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, an yi kuskure ne aka bayyana su a matsayin ma’aikatan bogi ko kuma wadanda basu zuwa aiki, duk kuwa da gudummawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan asibiti. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawa ta wayar tarho da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaja Kallas. Labarin ya kara da cewa ministan yana ganin matsalolin shirin Nucliya da kuma tsaron kasar ba za’a iya warwaresu ba sai ta wannan hanyar. JMI ta dauki wannan hanya ce don ita ce kadai wacce zata kai da gamsuwar ko wani bangare a cikin al-amuran da suke sabani a cikinsu. Aragchi ya fadawa Kallas kan cewa da wannan dalilin ne JMI ta dauki hanyar...
Karamar Hukumar Birnin Kdu tace tana nazarin samar da cibiyar horas da maniyyata aikin hajji ta dindindin a yankin domin karawa mahajjata kaimi wajen gudanar da aikin karbabbe. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin a lokacin rufe bitar da aka shiryawa maniyyatan yankin na Birnin kuudu. Yana mai cewar, idan aka samar da cibiyar zata kunshi dukkanin muhimman wuraren da ake ziyarta a lokacin gudanar da aikin hajji. Alhaji Muhammad Uba, yace za a kuma samar da ajujuwan horas da maniyyata da ofisoshin malaman bita da sauran dukkan abubuwan daya dace a cibiyar. Kazalika, Shugaban Karamar Hukumar, ya biya malaman bitar alawus dinsu na wannan shekarar da ma kwanton na shekarar...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da manyan jami’an likitocin kasa a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Umar Ahmed Labbo ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da aikin da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, hukumar ta kaddamar da tawagar likitocin guda 10, inda ya bukaci kungiyar da ta yi aiki da gaskiya, hakuri, da jajircewa wajen yi wa alhazan jihar hidima a kasar Saudiyya. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce aikin amana ce da bai kamata kungiyar ta dauka da wasa ba. Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewa da wannan tawagar, inda ya nuna cewa, wannan shi ne karon farko da jihar...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa tattaunawar sulhu a Gaza ba ta da wani tasiri a wannan mataki. Ofishin kungiyar, ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba kan gwamnatin Netanyahu don kawo karshen laifukan yunwa, kishirwa da kisan kai a Gaza, in ji wani babban jami’in kungiyar. Halin da ake ciki a Gaza ya kai intaha inji kungiyoyin kasa da kasa. A wani rahoto data fitar a baya baya nan kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta yi gargadi kan halin da ake ciki a zirin fiye da na watanni 19 da suka gabata.” kungiyar ta jaddada cewa “mafi yawan jama’a na yankin na fuskantar matsananciyar hadarin yunwa.” Sama da mutane miliyan daya...
Ya ƙara da cewa Ganduje mutum ne da kullum yana cikin yi wa ma’aikatansa fara’a. Ya ce masu yaɗa bidiyon na ƙoƙarin tada rikici ne domin dalilan siyasa. “Wannan ba zai rage farin jinin Ganduje ba,” in ji shi. “Ya yi wa Jihar Kano aiki tuƙuru, yanzu kuma yana yi wa ƙasa. ‘Yan adawa ba sa jin daɗin yadda APC ke ƙara ƙarfi a ƙarƙashin jagorancinsa.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Yin Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Kan Kasar Yemen
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da zaluncin ‘yan sahayoniyya a kan kasar Yemen Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai tashar jiragen ruwa na Hodeidah da sauran ababen more rayuwa na kasar Yemen, yana mai bayyana hakan a matsayin babban laifi da kuma keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa. A cikin bayaninsa da sanyin safiyar yau Talata, Baqa’i ya yi nuni da cewa: Hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai kan tashar jiragen ruwa, da masana’antu, da kuma wuraren zama a kasar Yemen, ana aiwatar da su ne tare da goyon baya da kuma taimakon Amurka. Ya bayyana wadannan hare-haren...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko da kuwa wani mataki ne da ya sabawa ‘yancin kai, ko cikakken amincin Iran ko kuma muhimman muradun kasa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, za a mayar da martani cikin gaggawa, da ya dace kuma halastacce. Wannan dai ya zo ne a cikin wata wasika da Amir Sa’ed Irawani, jakada kuma wakilin din-din-din na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya aikewa babban...
Tawagar jiragen saman yaki da dama ne suka kai munanan hare-hare kan sassa daban-daban na kasar Yemen a jiya Litinin Kafofin yada labaran kasar Yemen sun rawaito a jiya litinin cewa: Wata tawagar jiragen saman yakin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankuna daban-daban na kasar Yemen da suka hada da gundumar Bajil da wasu wurare a gundumar Al Hudaydah da ke yammacin kasar ta Yemen, da kuma gundumar Sinjan da ke birnin San’a. Ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa: Mutane 21 ne suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da aka kai kan masana’antar siminti na Bajel da ke gundumar Al Hudaydah. A nata bangaren, tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto...
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.” Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.” Iran dai ta sha yin watsi da...
Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi. A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta da goyon bayan dakarun (RSF) da suka shafe shekaru biyu suna yaki da sojojin Sudan. Khartoum na zarginsu da kasancewa masu goyan bayan kisan kare dangi” da ake ci gaba da yi wa al’ummar Massalit na Darfur, saboda zarginsu da goyon bayan dakarun gaggawa na Janar Hemedti (RSF). Khartoum na fatan alkalan kotun su umurci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta daina goyon bayan kungiyar RSF,...
Sojojin Yemen sun sanar da killace sararin samaniyar Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya suka mamaye Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Lahadi cewa: Za su kakaba wa haramtacciyar kasar Isra’ila cikakken takunkumi ta sama, yayin da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa suka yi gargadin hadarin da ke tattare da zirga-zirga daga filayen jiragen saman yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga karuwar hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza. Kakakin rundunar sojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Sari’e, ya ce za su kakaba takunkumin ne ta hanyar kai hare-hare akai-akai kan filayen jiragen saman haramtacciyar kasar Isra’ila, musamman filin jirgin sama na Ben Gurion. Sanarwar ta yi...
Ta tabbata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga ta bana bayan da Bayer Leverkusen ta buga canjaras a wasanta da Freiburg yau Lahadi. Itama Munich canjaras ta buga a wasanta na ranar Asabar tsakaninta da RB Leipzig inda aka tashi da ci 3-3, amma kuma sakamakon wasan Bayer Leverkusen dake matsayi na biyu ya tabbatarwa Munich nasarar lashe gasar Bundesliga karo na 34 a tarihinta. Harry Maguire Ya Sanya Hannun Kwantaragin Shekara Ɗaya A Manchester United Dortmund Ta Doke Bayern Munich A Wasan Hammayya A Gasar Bundesliga Za a iya cewa kocin ƙungiyar Vincent Kompany, wanda ya karɓi aikin horar da ƙungiyar bayan korar Thomas Tuchel ya shigo da kafar dama, wannan ne karon farko da...
Jami’in ya kara da cewa, dakarun tsaron yankunan teku na Sin sun aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, na gargadi da korar jirgin saman na Japan, wanda hakan mataki ne halastacce da kuma ya dace da doka. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya ta hori manoma da kada su yi fargaba bisa yadda Gwamnatin Tarayya ke shigo da abinci daga ƙasashen waje. Shugaban Cibiyar, Farfesa Ado Yusuf ya ba da shawarar ce a yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron bita da tsare-tsaren aikin noma na shekarar 2025 da ya gudana a dakin taro na Tanimu Balarabe da ke Cibiyar IAR Samaru, Zaria. Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato Ya tunasar da manoma cewa, nau’o’in abincin da suke nomawa ba a kasar nan kadai ake amfani da su ba, don haka...
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kuma kawayensu na wajen kungiyar sunce zasu kara yawan man fetur da suke haka da ganga 411,000 a cikin watan Yuli mai zuwa. Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiya ya bayyana cewa kungiyar da kawayenta sun gudanar da taro ta kafar sadarwa ta Bidiyo a ranar 3 ga watan mayu wato jiya inda suka tsaida wannan shawarar. Labarin ya kara da cewa kungiyar tana son ta maida ganga miliyon 2.2 da suke rage da radin kansu a shekarun bayana a hankali-a hankali. Sannan kungiyar zata ci gaba da gudanr da taro a farkon ko wani wata don sanin yadda kasuwar man take a duniya da kuma yadda zasu ci gaba da kara yawan...
113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauransu inda muke masu karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasasnce tare da mu. ///…Madallah, masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da cewa {gwagwarmayar kwace kasar Falasdinu zai fara da tube Mahmood Abbas daga shugabancin kungiyar Kwatar yencin Palasdinawa PLO}. Shugaba Mahmood Abbas, shugaban gwamnatin jeka na yi ka na Palasdinawa ya dade yana hana ruwa guda a gwagwarmayan da Falasdinawa Musamman a Gaza suke yi...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi yana shirin kai ziyara a kasashen Pakistan da Indiya a wannan makon a wani bangare na tuntubar juna tsakanin Tehran da kasashen yankin. Ministan harkokin wajen Iran din zai isa Pakistan a ranar Litinin 5 ga watan Mayu, domin tattaunawa da manyan jami’an kasar. Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da sabbin ci gaban yanki da na kasa da kasa, in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, kafin ya tabbatar da cewa Mr. Araghchi zai kai ziyarar aiki a Indiya nan gaba a cikin mako. Ziyarar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin Indiya da Pakistan, kasashe biyu masu...
Kyari ya mayar da martani ne a shafinsa na X a daren ranar Asabar 3 ga watan Mayun 2025. Wata jarida ta yanar gizo ce ta yi ikirarin cewa, Mele Kyari yana tsare a hannun EFCC domin amsa tambayoyi game da zarge-zargen almundahana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Suka Kai Kan Kasar Siriya
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Siriya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah-wadai da harin bam da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Siriya a ranar Asabar. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullahi ta fitar ta ce: Tana jaddada tofin Allah tsine da yin Allah wadai da zaluncin yahudawan sahayoniyya da suka addabi kasar Siriya a wani mummunan hari da suka kai kan yankunan kasar, tare da fakewa da munanan kalamai da take-take na aiwatar da ayyukanta na fadadawa da wargaza kasar Siriya da nufin rusa hadin kan kasar da kuma haifar da...
A yanzu kuma, Amurka na son kawar da dimbin gibin kudaden asusunta, ta hanyar amfani da kare-karen haraji. A baya Amurka ta yi kokarin hakan ba tare da cimma nasara ba, kuma a yanzu ma hakan ne zai sake faruwa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri. An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata. Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an gurfanar da 64 daga cikin wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin Maphites, Eiye, da Aye kuma ake zarginsu da kisan gilla da aka yi kwanan nan a rikicin kungiyoyin asiri. Kayan da aka ƙwato sun hada da bindigogi biyu ƙirar gida, bindiga guda mai tashi daya, da harsashi 24. ’Yan sandan sun shawarci iyaye da su kula da ayyukan ’ya’yansu kuma sun gargadi...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa Iran, ya kara haifar da shakku game da aniyar Washington na neman hanyar diflomasiyya. “Don ci gaba a kan wannan tafarki dole ne dayan bangaren ya nuna kyakkyawar niyya cewa da gaske ya ke,” in ji shi, kafin ya ce: “Iran, a matsayinta na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), dole ne ta ci moriyar makamashin nukiliya don dalilai na zaman lafiya.” Ministan...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean (Euro-Med) ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani jirgin ruwan Freedom Flotilla da ke dauke da kayan agaji zuwa zirin Gaza da aka yi wa kawanya. An kai harin ne a ruwan kasa da kasa kusa da Malta. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Euro-Med ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya a karkashin ikon Malta, tare da halartar Majalisar Dinkin Duniya. Kungiyar mai hedkwata a birnin Geneva ta jaddada cewa dole ne a hukunta wadanda suka aikata irin wannan ta’asa. Kungiyar ta kara da cewa “Hare-haren da aka kai kan jirgin ruwan...
Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar. Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da dan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa hudu zuwa 12, amma sakamakon hakurin da ya bayar aka rage hukuncin zuwa wasanni hudu. Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki hudu tsakani da Barcelona mai jan ragama, za ta karbi bakuncin Celta Bigo ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island. Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar Data, har da lokacin da ya dace, a fara gudanar da aiki. Ya sanar da cewa, idan an kammala wannan aikin, za su kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan Hukumar, na tsawon sa’oi 24. Dantosho wanda Manajan Sashen Tashar da ke a jihar Legas Lawal Ibrahim ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma yi hadaka da Rundunar Sojin Ruwa,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp