2025-11-03@17:23:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 335
«Sheikh Ɗahiru Bauchi»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Amina Yakubu, ɗaliba a ajin farko a Sashen Ilimin Halittu na Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta rasu a wani hatsari da ya rutsa da ita a Damaturu. Sanarwa daga ofishin mataimakin shugaban jami’ar da Abdulmumin Kolo Gulani, ta fitar ta tabbatar da rasuwar ɗlaibar. Babban malamin Tijjaniyya, Sheikh Umar Bojude, ya rasu Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe Ɗalibai da malaman jami’ar sun bayyana jimaminsu game da rasuwarta. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Asabar a kan titin Gujba daura da ƙofar jami’ar. Keke Napep da ɗalibar ke ciki ne ya yi taho mu gama da wata mota wadda ta murƙushe su. A cewar sanarwar, wasu mutum huɗu sun samu raunuka.
A yayin zaman majalisar dokokin jihar Katsina, Babban Mai Tsawatarwa na majalisar, Hon. Ibrahim Umar Dikko, ya fashe da kuka a gaban takwarorinsa, yana bayyana yadda ’yan bindiga suka mamaye mafi yawan yankunan da ke cikin Ƙaramar Hukumar Matazu da yake wakilta. Hon. Dikko ya bayyana cewa daga cikin gundumomi 10 da ke cikin Matazu, guda 8 sun faɗa hannun ’yan bindiga, inda ya ce manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda tsoron harin da ake kai musu. “A jiya da safe, a bakin garin kusa da makarantar sakandare, sun kashe wani matashi sannan suka sace shanu hudu da ake amfani da su wajen noma,” in ji shi cikin hawaye. Ya kara da cewa a cikin kwanaki biyu da suka...
A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu tare da tabbatar wa al’ummar yankin ƙudurinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi. A nasa jawabin, gwamnan ya yi kakkausar suka ga hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a baya-bayan nan, yana mai cewa da gangan maƙiya ke nufin waɗannan munanan ayyuka don yaɗa tsoro a tsakanin al’umma. “Na ziyarci garin Banga ne domin jajanta wa jama’a game da harin da ‘yan bindiga suka kai a kwanakin baya. “Lokacin da abin takaicin ya faru, na kasance ba na kusa, amma daga samun labarin, na umarci mataimakin gwamna da ya jagoranci wata babbar tawaga domin ziyarar jaje. “A jiya ne na dawo...
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe, mai wakiltar Nafada ta Kudu, Adamu A. Musa, ya zargi gwamnati da ‘yan majalisun jihar da kasa aiwatar da dokokin da suke zartarwa. Ya ce akwai dokar da aka zartar shekaru takwas da suka gabata domin yaƙi da fyaɗe da cin zarafin mata da yara, amma har yanzu ba a aiwatar da ita ba. Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki A cewarsa, majalisa tana yin doka sannan ta tura wa gwamna ya sanya hannu, amma daga baya a bar ta kamar ba ta da amfani. Ya yi gargaɗin cewa irin wannan sakaci yana ƙara wa masu aikata laifi ƙwarin guiwa...
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙudiri niyyar kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da kuma inganta rayuwar ’yan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rijistaran makarantar, Alhaji Kasimu Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an rufe makaranta kuma an umarci ɗalibai su bar harabar makarantar har sai an bayar da sanarwa ta gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk Lokaci wani abu ne da yake nuna yanayi a kodayaushe, sannan yake bada damar aiwatar da abubuwa masu kyau da mararsa kyau a rayuwa. Haka kuma yanayi ne da yake bada damar rayuwa a cikin daƙiƙu, mintuna, da kuma, awowi, ranaku, makonni dakuma shekaru. Ana amfani da lokaci ne ta hanyar da ya kamata kamar gudanar da rayuwa maikyau da zamantakewar yau da gobe, da kuma hanyoyin da ya dace na gudanar da rayuwa. Lokaci na yana da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da rayuwa. Amfanin lokaci na nufin amfani da lokaci ko kuma yadda ake amfani da shi wajen cimma burin mutum ko gudanar da ayyuka. Ga wasu daga cikin amfanin lokaci; inganta...
Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu. NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu Ta bayyana...
“Baya ga alaƙa da Ruwa, ƙasashen da ke Afirka ta Gabas da kuma waɗanda ke a Afrika ta Tsakiya, da suke yi musharaka da irin ƙalubalensu da kuma sauran damarmakinsu, dole ne mu zage mu amfana da tattalin arzikin da ake da shin a Tekuna, musamman ta hanyar haɗa kanmu da kuma yin haɗaka, wanda idan ba a yi hakan ba, tamkar muna kawai yaudarar kawunan mu ne,” Ɗantso ya ce. A cewar Shugaban na Hukumar NPA, alƙaluman da ake da su, sune za su bamu damar, ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata, na wajen ci gaba da bai wa Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika, kulawar da ta dace. Kazalika, Shugaban ya kuma jinkinawa shugaban ƙasa Bola Tinubu,...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar. Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, dukkan ɗaliban aji na ƙarshe na makarantun sakandaren Larabci na gwamnati da suka amfana da wannan tallafi sun kammala rubuta jarabawar NBAIS makon da ya gabata, kuma suna jiran sakamakon. Ya ce wannan tallafi na daga cikin ɗawainiyar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ke yi wajen taimaka wa ɗaliban aji na ƙarshe na sakandaren Larabci domin...
Bayan da aka ɗaura auren, masoyanta da abokan aikinta suka tura mata saƙonni taya murna daga sassa daban-daban na Nijeriya. Wannan aure ya zo watanni kaɗan bayan rasuwar mahaifinta, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sakamakon kama Mu’azu Ɓarga, yanzu haka abokan ta’asar tasa sai tsallakewa suke domin tserewa kamun rundunar ‘yan sanda, duk da gudun da suke rundunar na ci gaba da farautarsu har kuma an samu nasarar ƙara damƙe mutane biyu cikin sama da mutane arba’in da Ɓarga ya bayyana wa ‘yan sanda. Wannan tasa a ranar Juma’ar da ta gabata Al’ummar Sheka ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Muryar Jama’ar Sheka ta ziyarci Shelkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai domin jinjina wa ƙoƙarinsu. Cikin shahararrun mafaɗatan da suka gamu da ajalinsu alokacin arangama daban-daban akwai matashin da ya addabi al’ummar Unguwar Ɗorayi mai Suna Barakita, sai kuma wani mai suna Khalufa ɗan unguwar Ƙofar Mazugal Da kuma wani guda da ke tafka irin wannan...
Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 “Innalillahi wa inna IlaiHi rajiun. Allah Ya yi wa Mahaifin Dokta Bello Galadanchi (Dan Bello) rasuwa yanzun nan. Allah Ya gafarta masa. Ameen,” a cewar saƙon da Abba Hikima ya wallafa. Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin rasuwar mahaifin Ɗan Bellon ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa marigayi ya...
Sayar da Nunez zai ba Liverpool damar siyan Alexander Isak daga Newcastle. Sai dai Newcastle ta ƙi karɓar tayin fam miliyan 110 daga Liverpool, saboda tana so ta siyar da Isak ne abkan fam miliyan 150. Liverpool ta riga ta siyo Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen a kan fam miliyan 116 da kuma Hugo Ekitike daga Frankfurt a kan fam miliyan 79. Hakan ya sa Liverpool ta kashe kusan fam miliyan 250 a wannan kakar kasuwanni. Ta kuma siyar da Luis Diaz ga Bayern Munich ankan fam miliyan 65.5 da Tyler Morton ga Lyon a kan fam miliyan 15. Ɗan wasan Ingila Harvey Elliott ma na iya barin ƙungiyar a bana. A watan Janairu da ya wuce, Liverpool ta ƙi...
“Ko da yake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’a, Hukumar Gudanarwa ta jami’ar na cikin jimami matuƙa da wannan mummunan lamari, kuma tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai,” in ji sanarwar. Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin a kama waɗanda suka aikata wannan laifi. An binne marigayin a garinsu da ke Zariya a Jihar Kaduna. Jami’ar ta buƙaci ɗalibai su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a tare da su. Haka kuma ta roƙi jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen gudanar da bincike. Daga kanmu,...
Gwamnan ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron girmamawa ga Nafisa a faɗin jihar, sannan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da gyaran makarantu da ɗaukar malamai domin ganin kowanne yaro a Yobe ya samu ingantaccen ilimi kamar Nafisa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu. Jami’in Sadarwar Zamani na Gwamnatin Jihar Yobe, Yusuf Ali, ya bayyana cewa Rukayya ta samu kafa wannan tarihi ne a dalilin zurfin tunani da kuma kaifin basirarta da kuma fahimtar al’amuran duniya, duk kuwa da ƙarancin shekarunta. Ɗalibar daga Kwalejin Nigerian Tulip International (NTIC), Rukayya, ta ɗauki hankalin alƙalan gasar da sauran jama’a saboda ƙarfin hujjojinta da ta gabatar da kuma iya bayani mai ganawarsa...
Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na da nufin inganta lafiyar mata da yara tare da rage mace-macen da za a iya kauce wa ta hanyar samar da dama ga ayyukan kiwon lafiya. Cibiyoyin lafiya a fadin karamar hukumar, ciki har da Asibitin Gwamnati na Gwarzo da Asibitin ‘Yar Kasuwa, sun bayar da rigakafi kyauta, shawarwari kan abinci mai gina jiki, kulawar haihuwa da sauran muhimman ayyuka na kiwon lafiya. Jami’in...
A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki. Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP). Ya ce: “Kwarewa da haɗin gwiwa su ne manyan abubuwan da muka a gaba, idan aka yi la’akari da saurin ci gaban fasaha a cikin gine-ginen gidaje, samar da kudaɗe da kuma inganta tsarin.” Ya ce taken taron na wannan shekara, Maimaita Gidaje Ta Hanyar Sabuntawa, wanda daidai yake da ainihin darajar kamfanin. Barista Adebayo ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa haɗin gwiwa da kamfanin Simintin dangote...
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya yi nuni da cewa; yanzu mafi akasarin mutane, ba sa son abin da zai taimaka musu; kawai dai sun fi mayar da hankali wajen sharholiya iri-iri. da yake amsa tambaya a kan me yasa ya fi mayar da hankali wajen ɗora bidiyo, musamman na jarumai mata a Masana’antar Kannywood a shafukansa na sada zumunta, musamman kuma ‘Facebook’? Sai Baba Sadiƙ ya ce; ba komai ba...
“Saurayin nata ne ya kashe marigayiyar a ranar Talata kuma ya kulle ta a cikin dakinsa, maƙwabta ne suka ja hankalin daliban a lokacin da suka fahimci wani wari daga dakin. “Har yanzu ba mu san dalilin da ya sa saurayin ya kashe ta ba, dalibar tana sana’ar POS a yankin, amma tun ranar Talata, ta ɓace kuma babu wanda ya san inda take sai jiya, lokacin da maƙwabta suka ji wani wari daga dakin saurayinta. “Shi yaron, bayan sun kashe ta, ya tafi da cinikin da yi a wajen sana’ar ta ta POS. “Lokaci ya yi da gwamnatin jihar za ta yi wani abu game da kashe-kashen da ƴan asalin garin suke yi wa dalibanmu, idan ba a yi...
Jami’an tsaro sun tabbatar da kuɓutar wasu ɗalibai shida na Makarantar Horon Ilimin Shari’a ta Najeriya da aka sace. Rundunar ’yan sandan Jihar Binuwai ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a. ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Kakakin ’yan sandan, Udeme Edet, ya ce ɗaliban sun taso ne daga Jihar Anambra, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makarantar horon ilimin shari’a da ke Yola, a Jihar Adamawa. ’Yan bindiga ne suka tare su a iyakar Binuwai da Taraba. “An ceto ɗalibai shida da aka sace a ranar 26 ga watan Yuli, 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Anambra zuwa Adamawa. “An...
Gwamnan Jihar ta Gwambe, ya tunatar da cewa; a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a gabanmu a matsayin ɗan takara a yaƙin zaɓen 2023, ya yi wa Arewacin Nijeriya alƙawura na musamman. Kazalika, Arewa ta amince da manufofin shugaban ƙasar, ta kuma yi tsayin daka wajen zaɓensa, inda suka bayar da gudunmawa na kimanin kashi 60 cikin 100 na ƙuri’un da Tinubun ya samu. “A yau, ga shi mun taru, domin yin nazari a kan waɗancan alƙawuran tare kuma da tantance irin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, abubuwan da muka samu su ne; sauye-sauyen da aka samu duk kuwa da irin ƙalubalen da ake fuskanta a wannan ƙasa. Wannan na nuna cewa, demokuraɗiyyarmu za ta...
Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun sojin. ɗuba da sashe na 217 na kudin tsarin mulikin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, wannan sashen, ayyukan soji tun daga na matakin rundunar sojin kasa da ta ruwa da kuma ta sama shi ne tabbatar da bai wa Nijeriya kariya, daga duk wani nau’in hare-haren, da ka iya zuwa, daga ketare, musamman ta hanyar, bai wa iyakokin kasar kariya, musamman bayan shugban kasa,...
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya ji ciwo mai tsanani a wajen. An garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Panorama inda aka ɗinke masa raunin da ƙwayoyin da suka kai guda shida. Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa Barcelona Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aris FC, wacce ta karɓi Perez aro daga Celta Vigo, ta tabbatar...
Sai dai ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a 2023, amma yanzu lokaci ya yi ne da zai yi gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa
Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane. Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce rasuwar Dakta Usigbe babban rashi ne ba kawai ga kamfanin jaridar Tribune da fagen aikin jarida ba, har ma da ƙasar nan baki ɗaya. “Nijeriya ta yi rashi matuƙa — mun rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jarida, wanda ilimin sa, jarumtar sa, da himmar sa ta sa kowa yana girmama shi.” A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga shugabanni da ma’aikatan Tribune, da gwamnati da al’ummar Jihar Edo inda marigayin ya fito, da kuma iyalan sa, da abokan sa, da ma dukkan masu mu’amala da shi. “Allah ya jiƙan sa, ya ba duka waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi,” inji Ministan. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Sanata Dickson ya ƙara da cewa duk da wasu jami’an gwamnati ba su bi umarnin shugaban ƙasa ba, amma shi ya lashe zaɓen, kuma ya gode wa Buhari. Hakazalika, ya ce bayan ya kammala wa’adinsa a 2020, a lokacin da APC ke shirin karɓar mulki a Bayelsa, kotun ƙoli ta yanke hukunci cewa ɗan takararsu bai cancanta ba, amma Buhari bai matsa lamba kan kotun ta sauya hukuncin ba. “A lokacin mutane sun shirya rantsar da ɗan takarar APC a Bayelsa, amma cikin ƙasa da awa guda, kotun ƙoli ta soke nasararsa. Duk da haka Buhari ya karɓi hukuncin,” in ji shi. Ya ce Buhari shugaba ne na gari, wanda duk da bambancin siyasa da ra’ayi, bai taɓa nuna bambanci...
Kayan da aka gano a wajen samamen sun haɗa da wayoyin salula da dama, kwamfutoci, na’urorin haɗa Intanet da mota ƙirar Honda Accord. Sunayen waɗanda aka kama sun haɗa da: Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh, Jafar Abubakar, Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan da Abubakar Abusufyan. Sauran sun haɗa da Abdulmalik Ibrahim, Abubakar Sadiq, Daniel Masamu, Abdulrasheed Abdulsamad, Issac Dosunu, Nuraddeen Ogunbiyi, Onyeyemi Kaleem, Miracle Joseph, Danjuma Musa, Ibrahim Mubaraq, Yusuf Salihu, Lawal Ibrahim Edebo, Abdulmajeed Suleiman da Dauda Abdulhamid. EFCC ta ce za a gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
An miƙa batun zuwa Rundunar ‘yansandan Jihar don ci gaba da bincike kafin gurfanar da wanda ake zargin a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
– Emmanuel Adegbola Aina – AIG na wucin gadi, sashen leƙen asiri – Omolara Ibidun Oloruntola – Hassan Abdu Yababet – CP, Kwalejin ‘Yan Sanda Jos – Bretet Emmanuel Simon – CP Jihar Taraba – Enyinnaya Inonachi Adiogu – CP, FCID, Gombe – Aminu Baba Raji – CP, FCID Alagbon – Mohammed Mu’azu Usman – CP, Tashoshin Gabas, P/Harcourt – Festus Chinedu Oko – AIG na wucin gadi, sashen DLS, Hedkwatar – Ronke Nurat Okunade – CP, SFU FCID Annex, Lagos Kazalika, PSC ta amince da: – Ɗaga darajar DCP 16 zuwa CP – Ɗaga darajar ACP 27* zuwa DCP – Ɗaga CSP 145 zuwa ACP, ciki har da likitoci, ma’aikatan lafiya, injiniyoyi na jiragen sama, da limamai – Ɗaga...
Wasu da ake zargin Jami’an Hukumar Farin Kaya (DSS), sun kama fitaccen mai barkwancin nan a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Sun kama shi ne bayan isowarsa filin jirgin saman, wanda hakan ya jawo hankalin mutane da dama, ciki har da fasinjoji da ma’aikatan filin jirgin. DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m a hanyar Jos Sai dai Ɗan Bello cikin wata hira ta wayar tarho da ya yi da kafar DCL, ya bayyana abin da ya faru, inda ya ce: “Dana sauko wasu mutane wanda kana ganinsu ka san hukumomi ne...
Hukumar Tsaro ta DSS ta saki matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, jim kaɗan bayan sun kama shi a Jihar Kano. Jami’an DSS sun kama Dan Bello ne a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kuma wasu majiyoyi na zargin daga Abuja jami’an suke. Aminiya ta gano saukar matashin da ke zaune a ƙasar China a Najeriya ke da wuya jami’an DSS suka yi awon gaba da shi. Sai dai kuma rahotanni da muka samu daga bisani sun nuna cewa jami’an tsaron sun sake shi, bayan ya yi ’yan mintoci a hannunsu. Bayan nan ne Ɗan Bello ya wallafa hotonsa da tare da matashin lauya ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima a cikin mota. A ƙarƙashin hoton da ya wallafa...
Hukumar Tsaro ta DSS ta saki matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, jim kaɗan bayan sun kama shi a Jihar Kano. Jami’an DSS sun kama Dan Bello ne a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kuma wasu majiyoyi na zargin daga Abuja jami’an suke. Aminiya ta gano saukar matashin da ke zaune a ƙasar China a Najeriya ke da wuya jami’an DSS suka yi awon gaba da shi. Sai dai kuma rahotanni da muka samu daga bisani sun nuna cewa jami’an tsaron sun sake shi, bayan ya yi ’yan mintoci a hannunsu. Kawo yanzu dai babu bayani daga hukumomin tsaro ko Ɗan Bello game da dalilin tsarewar da aka yi masa da kuma abin da ya wakana tsakaninsu....
Jami’an tsaro sun kaman matashin nan mai barkwanci, Bello Galadanci a Kano.
Ana zargin wani ɗalibi da ke shekarar ƙarshe a jami’a da ƙona budurwarsa mai ɗauke da tsohon ciki a Jami’ar Fatakwal da ke Jihar Ribas. Wanda ake zargin da budurwar tasa mai suna Cynthia Chukwundah, dukkansu ɗaliban ajin ƙarshe ne a jami’ar. Ana zargin matashin ya ƙona Cynthia mai shekara 32 ne ta hanyar wata mata ruwan batir, daga bisani ta ce ga garinku nan. Cynthia ta gamu da ajalinta ne bayan saurayinta Sunny Amadi ya yi mata wannan aika-aika a gidansu da ke layin Okoro unguwar China da ke Birnin Fatakwal. Sojoji sun kama mai garkuwa da mutane da bindigogi Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCL Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida...
A nata bangaren, Mrs. Adeniji ta bayyana cewa akwai yawaitar yara marasa zuwa makaranta a ƙananan hukumomi 14 na jihar, tare da tabbatar da cewa ta hanyar wannan shirin zai taimakawa ɓangaren ilimi a jihar Zamfara. “Muna aiki tare domin tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari s baya,” Cewar ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗangote Ya ƙara da cewa “A yau, bayan kashe sama da dalar Amurka biliyan 18 wajen gudanarwa tare da gyara matatun man har yanzu basa aiki. Kuma bana tunanin nan gaba za su iya ci gaba da aiki. Ƙoƙarin zamanantar da su kamar misalin zamanantar da tsohuwar motar da ta yi shekara 40 ne, ko an canja inji ba zai sa ta koma dai-dai da ta zamani ba”. Alhaji Aliko Ɗangote ya ce ya yanke shawarar gina matatar man fetur ne mai fitar da ganga dubu ɗari shida da hamsin a rana bayan da marigayi Umaru Musa Yar’adua ya yanke shawarar ƙin siyar masa da matatun man fetur ɗin ƙasar nan. Sabuwar matatar man fetur ta Ɗangote ana saran za...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce yana da shakku a kan ko matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya za su ƙara aiki a nan gaba. Najeriya dai na da matatun mai guda hudu mallakinta a biranen Fatakwal da Warri da Kaduna. Amma attajirin ya ce matatun man waɗanda ke ƙarƙashin kulawar Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), sun laƙume sama da Dalar Amurka biliyan 18 wajen gyaransu, amma har yanzu sun ƙi aiki. Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC Ɗangote ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin shugabannin kamfanoni wadanda ke Karatu a Lagos...
A harin, mutane 13 daga cikin baƙin suka rasu, ciki har da mata da yara. Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin. Daga baya kuma, Kwamishinan ‘Yansandan zai yi jawabi a hedikwatar rundunar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ziyarci iyalin marigayi, Alhaji Aminu Dantata a Jihar Kano, don yi musu ta’aziyya. Obi, ya bayyana cewa ya yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar Alhaji Ɗantata, inda ya bayyana shi a matsayin “uba ga kowa.” An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN 2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Ya yaba yadda Ɗantata ya zama babban attajiri kuma ya taimaka wa mutane da dama suka samu nasara a rayuwarsu. Ya ce Ɗantata ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya. “Mun zo nan yau don jimami tare da iyalinsa da kuma ɗaukacin ‘yan Najeriya, saboda...
Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A CPC, Haruna Sa’eed Kajuru, Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Kisan ‘Yan Zariya A Filato
Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan. Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa. Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe...
Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da ita daga aikin da ta sa a gaba ba.” Ministan ya ce ko da yake ana ta raɗe-raɗi a kafafen yaɗa labarai game da sabuwar haɗakar siyasar adawa da ke tasowa, Shugaban Ƙasa Tinubu yana ci gaba da maida hankali ne kan Shirin Sabunta Fata domin ciyar da ƙasa gaba. “Hayaniya a kafafen yaɗa labarai kan fitowar wata sabuwar haɗakar siyasa abin fahimta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine. Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye wurin aikin ne da safe, inda suka yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a wurin. An bayyana cewa bayan harin, maharan sun ajiye motarsu a kusa da tashar watsa shirye-shiryen Radio Kogi da ke Otite, da nisan ‘yan mitoci kaɗan daga inda suka sace ɗan Chinan. CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An fara tuhumar tsohon ɗan ƙwallon Arsenal, Thomas Partey da laifuka biyar da suka haɗa da fyaɗe da kuma cin zarafi, an bayar da rahoton cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarar 2021-2022, cewar ‘yansandan Birtaniyya. Daga cikin laifukan akwai fyaɗe akan wasu mata uku waɗanda ake tuhumarsa da cin zarafinsu ta hanyar tursasawa kan mace ta farko da ta biyu sai kuma laifin lalata da mace ta uku. ‘Yansanda a ƙasar Birtaniya sun ce ya kamata Thomas ya bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar 5 ga watan Agusta, tuhumar ta biyo bayan binciken da jami’an tsaro suka gudanar, wanda ya fara a watan Fabrairun 2022 bayan da ‘yansanda sun samu rahoton fyaɗen. Partey dai ya bar...
Wata Kotun Majistare da ke jihar Kano ta yanke wa fitaccen ɗan TikTok, Umar Hashim da aka fi sani da Tsulange, hukuncin ɗauri na shekara ɗaya bisa laifin aikata abinda ya saɓa da tarbiyya a bainar jama’a. Alƙaliyar kotun, Hadiza Muhammad Hassan, wadda ke zaune a Gyadi Gyadi, ta samu Tsulange da laifi na zubar da mutunci a idon jama’a bayan gabatar da hujjoji da shaidu. Ta bayyana cewa an tabbatar da cewa ɗan TikTok ɗin ya aikata laifin ne cikin gangan. Ɗan TikTok Tsulange Ya Shiga Hannu Bisa Wanka Da Rigar Mama A Titi Kotu Ta Tura Ɗan Tiktok Gidan Yari Kan Shigar Mata Da Kalaman Batsa A Kano A hukuncin da ta yanke, ta ba da umarnin da...
Magoya bayan Liverpool da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cikin jimami bayan ɗan wasan Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani hatsarin mota. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis a yankin Zamora na ƙasar Spain. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta Jota ya rasu yana da shekara 28 a duniha. Hatsarin ya faru ne a hanyar A-52, kusa da garin Palacios de Sanabria. Jota yana cikin motar tare da ɗan uwansa, André Silva, wanda shi ma ya rasu. Silva ɗan wasa ne da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon kafa ta Penafiel a ƙasar Portugal. Rahotanni sun...
Wani ɗan Ghana da aka yi ƙoƙarin yaudararsa shi ma ya tsere, ya koma Ghana, inda ya kai rahoto ga hukumomi, abin da ya haifar da haɗin gwiwar ƙasashen biyu don ceton Sammed. Sakamakonhaɗin gwiwar da ’yansanda suka yi a Abuja, an ceto Sammed. Adejobi ya ce an ɗauki matakai don kama waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki domin su fuskanci hukunci. A wani samame daban, ’yansanda sun kama wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma ta’addanci a Abuja da Jihar Kaduna. An kama su ne a ranar 29 ga watan Yuni, 2025, bayan samun sahihin bayani da kuma haɗin kai ƙarƙashin jagorancin ACP Victor Godfrey. An kama su a wurare daban-daban ciki har da...
Cikin tawagar akwai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; a Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Ƙaramin Ministan Harkokin Gidaje da Cigaban Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata; da kuma Hassan Abdullahi, Daraktan Tsaro na Cikin Gida a ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), wanda ya wakilci NSA. Wasu fitattun malamai na addinin Musulunci da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Dakta Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Jami’an Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jiddah sun haɗu da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Ibrahim Modibbo, tare da Ambasada Mu’azzam Ibrahim Nayaya, da Manjo Janar Adamu Hassan,...
A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahoton LEADERSHIP ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne. Bincike ya nuna cewa ba wanda aka sace daga cikin mutanen da ke bidiyon yana da alaƙa da Gwamna Dauda Lawal. Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƴar uwar Gwamnan da aka sani mace ce, ba namiji ba. Hakanan, mutumin da ke cikin bidiyon na bayyana cikin tsananin firgici da damuwa, alamar cewa yana fuskantar tilas daga barayin daji da suka umurce shi da ya faɗi abin da suke so. Da yake martani kan bidiyon, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa wannan wata sabuwar dabara ce da ɓarayin suka bullo da ita don jawo hankali. Ya ce, “Idan aka kalli bidiyon da kyau,...
Ya samu munanan raunuka a harin da aka kai masa, wanda daga baya ya mutu. Janar Kangye ya ƙara da cewa Danbokolo ya fi Bello Turji tsabibanci, shi ne ya jagoranci harin watan Disamban 2021 a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, inda ya ƙone fasinjoji da ransu a cikin mota. Hakazalika, ya bayyana cewa Danbokolo na amfani da wata ƙwaya mai suna ‘pentazocine’ domin ci gaba da aikata miyagun laifuka. Yanzu haka, sojojin Operation FASAN YAMA suna ci gaba da neman Bello Turji wanda ya ɓuya. Janar Kangye ya tabbatar da cewa rundunar sojin Nijeriya tana da ƙwarin gwiwar samar da zaman lafiya a dukkanin sassan ƙasar nan. Ya kuma roƙi haɗin kan ‘yan Nijeriya don cimma wannan buri....
Wani ɗan Fashi da makami ya rasa ransa bayan da yayi yunƙurin yin fashi a unguwar Dorayi Babba, Unguwar Jakada, Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarawon, wanda aka gano sunansa Musa Nuhu, ya kutsa cikin wani gida riƙe da makami, wata wuka da nufin yin fashi a wani gida. Bayan shiga cikin gidan, ɓarawon ya kai hari kan wasu mata biyu tare da jikkata su. Sai dai wani namiji daga cikin iyalan gidan yai taho mu gama da ɓarawon a cikin wata fafatawa mai zafi da ta jawo raunika a tsakaninsu duka biyu. Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari Kakakin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.” Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar. Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi...
Rahotanni na cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa. Gwamnatin Nijeriya ce ta sanar da hakan ta bakin Ministan Labarai, Mohammed Idris yayin ganawa da da BBC. APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje An kashe ubangidan Turji, Kacalla Ɗanbokolo a Zamfara Ministan ya ce an ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina. A cewarsa, “akwai ƙa’idoji da Gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar. “Saboda haka yanzu ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin Gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,” in ji Ministan. Mohammed Idris ya...
Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan jihar mai suna Kacalla Ɗanbokolo. Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro. “Ɗanbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai,” in ji Ahmad Manga. “Mutanensa da aka kashe sun haura 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu,” in ji Manga. Ya bayyana cewa Kacalla Ɗanbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa-kai na Gwamnatin...
Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini. Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa...
Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus. Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano. Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan. Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari. Ya ce, kafafen yada labarai sun...
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata. Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ƙarshen mako. Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawaki tofa ne ya sanar da haka a safiyar Litinin. A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa hukumomin Saudiyya sun amince da yin jana’iza da binne Alhaji Aminu, Ɗantata a Madina, kamar yadda ya bar wasiyya.
Ya ce yana matuƙar daraja lokutan da suka gudanar tare. Ya roƙi Allah ya bai wa iyalan Dantata da Dangote, Masarautar Kano, da al’ummar jihar da ƙasar baki ɗaya haƙuri da juriyar rashin wannan babban mutum. “Allah Ya jikan shi Ya sa Aljannatul Firdaus makomarsa,” in ji Buhari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano. An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi. Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar. Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane. Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina...
Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi. Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Abu ɗaya da za ka iya bayyana Alhaji Aminu Dantata shi ne dogo a siffa da kuma shekaru da kuma tsawon shekarun da ya ɗauka yana tara dukiya da kuma ilimin rayuwa. Ya ɗauki tsawon shekara 70 yana gudanar da kasuwancin da ya shafi fatauci da gine-gine da harkar banki da abin da ya shafi muhalli da man fetur da iskar gas. A ranar Asabar 28 ga Yuni, 2025, Allah Ya yi masa rasuwa ya da a shekaru 94 a duniya. A kan haka ne muka kawo muku tattaunawarmu ta shi ta ƙarshe wanda muka fara wallafa a ranar 18nga watan Oktoba, 2024. A cikin tattaunawar, Alhaji Aminu Ɗantata ya yi bayani kan gwagwarmayar rayuwarsa kamar haka: Kasancewarka mutumin...
– Lokacin: Asabar 2:00 na rana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa. Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziki a nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE.)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Wannan ya nuna dalibai, 96,838 zasu rubuta jarabawa a fadin Nijeriya gaba daya duk ta wannan shekarar ce, 2025,a cibiyoyin rubuta jarabawa,183,yayin da wasu kuma za su jira.” Hakanan ma Hukumar tace tana nan tana bankado cibiyoyin rubuta jarabawa da ake yin cuwa- cuwa, da kuma wadanda basu cancanta, ace n arubuta jarabawar a wuraren ba, saboda rashin ingancin abubuwan da ake amfani da su lokacin jarabawar. Akwai wuraren/ cibiyoyin rubuta jarabawa wadanda aka tantance hakan kuwa ya biyo baya binciken kwakwaf da aka yi lokacin da aka yi jarabawar ta gwaji, jarabawar ta sosai,da wadda aka sake rubutawa.Kamar yadda aka bayyana, kuma kamar yadda sakamakon bincike-binciken da aka yi, akwai cibiyoyin rubuta jarabawa,113 wadanda yanzu an dakatar da amfani...
Jaridar LEADERSHIP ta kuma ruwaito cewa rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta taɓa gargaɗin masu ɗaukar bidiyo da su daina tare hanya da sunan yin fim. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba. Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin. Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori. Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13. Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci...
Wasu kuma sun jikkata a harin. Gwamna Sani ya ce kisan rashin imani ne, kuma ya bayyana cewa ya tattauna da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu don tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika. Ya kai ziyara ga waɗanda suka tsira daga harin a Asibitin Rundunar Sojin Naieriya na 44 da ke Kaduna, sannan ya yaba wa jama’ar Kaduna kan zaman lafiya da kaucewa fitina. Ya kuma roƙi shugabannin Filato da su hana faruwar irin wannan mummunan lamari. Gwamnan ya buƙaci hukumomin tsaro da su hanzarta kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Haka kuma wasu ƙungiyoyi a Turai sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan. Majiyoyi sun bayyana cewa Brentford na son a ce darajar Mbeumo ta kai irin kuɗin da United ta biya wajen ɗauko Cunha kafin su yarda su sayar da shi. Mbeumo ya zura ƙwallaye 20 a kakar wasan da ta gabata, kuma ya taimaka aka zura wasu tara. Sai dai akwai yiwuwar shi da abokin wasansa na tawagar Kamaru, Andre Onana, ba za su buga wasannin farko na sabuwar kakar wasa ba saboda za su wakilci Kamaru a gasar cin kofin ƙasashen Afirka da za a buga a Maroko. Kamaru za ta fara buga wasa da Gabon ranar 24 ga watan Disamban 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Bayan faruwar lamarin ne, wasu fusatattun dalibai matasa suka tare hanyar Agaie-Lapai, suna nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa abokin su. Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Yau 23 ga watan Yuni, 2025 da misalin karfe 3 na dare, rundunar ta samu labarin cewa, da misalin karfe 2:30 na dare wasu ‘yan daba sun kai hari a wasu dakunan kwanan dalibai dake unguwar Ndakitabu ta Lapai, amma maharan sun tsere a lokacin da jami’an ‘yansandan suka isa wurin”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu a daren ranar Juma’a bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari da bam a wani wsjen cin abinci da ke garin Konduga, a Jihar Borno. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin. ’Yan Najeriya da suka maƙale a Isra’ila na neman ɗauki Bam ya kashe mutum 5, 15 sun jikkata a Kano Ya ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sojoji na gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Ya ce, “Wani mutum ya kutsa cikin taron mutane da misalin ƙarfe 10 na dare tare da bam, wanda ya tarwatsa...
Alhaji Hassan ya ce duk da matsalolin tsaro da aka samu a kananan hukumomin, Jihar Kaduna ce kan gaba a noman shinkafa a daukacin jihohin da suke Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar tantance fina-finai ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta ce za ta ci gaba da sa ido tare da ɗaukar matakin shari’a kan duk wani da ya yi amfani da sunan barkwanci don yada abin da ya kira da “nishadi mai tada zaune tsaye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yayin shari’ar, jami’in ‘yansanda ASP Luka Sadau, ya bayyana cewa wasu daga cikin kwamitin Masallacin ne suka kama Usman a ranar 13 ga watan Yuni, sannan suka kai shi ofishin ‘yansanda. Ya ce bayan sallar Juma’a, Usman ya sace takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000. Usman ya kuma amsa cewa yana yawan zuwa Masallaci a ranakun Juma’a domin satar takalma, sannan ya sayar da su a kasuwannin Monday Market da Maraban Rido. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Karfafa hulda da al’umma da shugabannin yankuna don samun shawarwari kan inganta tsaro. Ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki don samun nasara a yaki da daba. Kwamishinan ‘Yansanda ya tabbatar wa mazauna Kano cewa hukumar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu, inda ya ce za su ci gaba da more zaman lafiya ba tare da fargaba ba. Haka kuma, hukumar ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani abin da suka gani na zargi ta layukan gaggawa: 08032419754, 08123821575, ko 09029292926. Rahotanni sun nuna karuwar ayyukan daba a Kano, musamman a cikin birnin, wanda ke janyo asarar rayuka da raunuka ga ‘yan daba da fararen hula. ...
Rundunar Ƴanandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Umar Yau, wanda aka fi sani da “Snake,” bisa zargin damfara ta yanar gizo da satar bayanan wasu mutane. An kama Yau, mai shekaru 25 daga unguwar Yelwan Makaranta a Bauchi, bayan binciken da aka fara sakamakon ƙorafi daga wata mata da ya damfara. Fatimah Faiz Ali Bawahab, wata ’yar kasuwa ta yanar gizo, ta kai ƙorafin cewa wani ya ƙirƙiri asusun bogi a Facebook da sunanta da hotunanta don damfarar mutane. CSP Ahmed Wakil, kakakin rundunar, ya ce wanda ake zargin ya ƙirƙiri asusun “Amizeebaby Muhd” inda ya ke tallata kasuwancin ƙarya, yana karɓar kuɗi daga mutane ta asusun banki. Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da...
Baya ga haka, Sojojin sun kashe ƙarin ‘yan ta’adda goma da suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga, waɗanda ake zargin sun kasance cikin wata tawagar da Dogo Sule ya tara domin kitsa hari. Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar Soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tinubu ya bayyana cewa, aikin titin, wanda aka yi watsi da shi tuni duk da muhimmancin titin a cikin taswirar Abuja, amma yanzu ya kammalu a karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya. Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya bai wa babban birnin tarayya zaman lafiya, da ci gaban Nijeriya, da kuma bai wa sojojin Nijeriya aminci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayanai sun nuna cewa, harin na faruwa, aka sanar da jami’an tsaro. Sun isa cikin gaggawa da motocinsu da jirgin sama mai saukar ungulu. Amma maharin ya ƙi miƙa wuya, hakan ya sa aka bindige shi. Daga cikin waɗanda suka mutu, mata shida ne, maza uku, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harbin bindiga. Hukumomi sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike don samo ƙarin bayani game da wannan mummunan al’amari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025. Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro, tare da haɗin guiwar sauran jami’an tsaro inda suka nufi wurin da nufin daƙile fashin. Da isarsu wurin, suka fara musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu wanda hakan ya janyo da dama daga cikin ‘yan fashin suka gamu da raunuka na harbin bindiga sannan an harbe daya ya mutu nan take. LEADERSHIP ta rawaito cewa, an miƙa gawar Shagari ga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da ɗaukar ɗan wasan gaban ƙasar Brazil Matheus Cunha daga Wolverhampton Wanderes akan kuɗi fam miliyan 62.5, Cunha zai zama ɗan wasa na farko da Ruben Amorim zai saya a wannan bazarar yayin da yake ƙoƙarin sake gina ƙungiyar da ta ƙare a mataki na 15 a gasar Firimiya, Manchester United za ta kammala yarjejeniyar ɗaukar Cunha da zarar an buɗe kasuwar saye da sayarwar yan ƙwallo a ƙasar Ingila. Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a United tare da zaɓin ƙarin shekara, Cunha ya bar Wolves a matsayin ɗan wasa mafi tsada da ta taɓa sayarwa a tarihinta bayan da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan ta...
Sai dai kwanaki uku kafin zaben mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya ya rushe shugabancin hukumar zaɓen tare da dakatar da su wajen shirya zaɓen. Sai dai duk da hukuncin da kotun ta bayar, hukumar zaɓen ta shirya zaɓe a ranar 26 ga watan Oktoba na shekarar 2024. Sai dai tun a wancan lokacin jam’iyyar APC ta yi fatali da zaɓen, inda ta bayyana shi a matsayin wanda bai inganta ba sakamakon saɓawa hukuncin kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
Daga baya, hukumar WAEC ta fitar da sanarwa tana mai bada hakuri, inda ta ce wasu ƙalubale ne suka hana isar da kayayyakin jarrabawa akan lokaci. Wannan lamari ba sabon abu ba ne, domin a watan Afrilu, LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu masu rubuta jarrabawar UTME sun bar gida da asuba domin isa cibiyoyin jarrabawa kafin ƙarfe 6:30 na safe, ba tare da wadataccen tsaro ko sufuri ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayan an bari Amer, ya shiga jirgin, suka kama hanyarsu ta tafiya har suka sauka lafiya wanda hakan ya sa ma’aikatan jirgin suka ɗauki hoton da shi don tarihi, inda a ɗayan ɓangaren mutane da dama ke suffanta lamarin a matsayin hujjar ƙarfin niyya da ikon Allah. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp