2025-11-03@17:23:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 335
«Sheikh Ɗahiru Bauchi»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya. “Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara. “Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan...
Kafin wasan ƙarshe na bana da za su kara da Crystal Palace a ranar Lahadi, Salah ya riga ya ci ƙwallaye 28 a Firimiyar bana kuma ya taimaka a ci wasu 18. Kusan taimako biyu kawai suka rage masa ya kai tarihin taimako 20 da Thierry Henry da Kevin de Bruyne suka kafa. A wannan kakar, Salah ya zama ɗan wasan da ba na Ingila ba da ya fi zura ƙwallaye kwallaye a tarihin Firimiyar Ingila, inda ya zarce ƙwallaye 184 da Sergio Aguero ya ci. Haka kuma ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool har zuwa shekarar 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
“Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran ilimi” cewar Dr. Almajir. Taron ya samu halartar Dr. Maimuna Isma’il da ke koyarwa a sashen da sauran mambobin ƙungiya da ‘yan uwa da abokan arzikin Dr. Sani Dauda Ibrahim da aka karrama a wajen taron. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
“Tsohon abin da ake zargin Sanata Natasha – duk karya ne,” in ji Obinna a fili. Har yanzu babu wata sanarwa daga ‘yansanda kan lamarin kama Obinna ya haifar da fushi a tsakanin masu fafutukar kare ‘yancin kafofin watsa labarai, waɗanda ke ganin harin ne kan ‘yancin faɗin albarkacin baki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayan haka, ‘yansanda sun hanzarta daƙile harin, inda suka kama su a ranar 15 ga watan Mayu, 2025. Da ‘yan fashin suka hango ‘yansanda, sai suka fara harbi. A lokacin musayar wutar ne, Babanle ya mutu. ‘Yansanda sun kama sauran tawagar ƙungiyar guda bakwai a wajen. Wasu daga cikinsu tsoffin fursunoni ne, yayin da ɗaya daga cikinsu fursuna ne da ya tsere daga gidan yari. Hakazalika, ‘yansanda sun ƙwato wasu kayayyaki ciki har da mota ƙirar Toyota Camry, babur ƙirar boxer, harsasai, bindigogi ƙirar AK-47 da kuma wata bindiga ƙirar gida. SP Adeh, ta ƙara da cewa shugaban ƙungiyar, Solomon Bawa wanda aka fi sani da Fasto Mogu, ya tsere tare da wani mutum bayan sun samu rauni. Ta roƙi...
Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen matan da aka kama ba, amma jami’an leƙen asirin Nijeriya sun ce matan na da muhimmanci wajen binciken hanyoyin samun kuɗaɗe da tallafin da ‘yan ta’adda ke samu. Wani masani kan yaƙi da ta’addanci ya ce wannan ci gaba ya ƙara bayyana yadda matsalar tsaro a Nijeriya ta fara ɗaukar salo na ƙasa da ƙasa. Ya kuma bayyana irin yadda ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga Nijeriya...
Ya ce, “Eh, an kama Galadi yau yayin da ake tantance shi da nufin zuwa Saudiyya.” Kama Galadi na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan kama wani riƙaƙƙen ɗan bindiga a sansanin alhazai da ke Abuja. Ana zargin mutumin da hannu a wasu manyan sace-sacen mutane a Jihar Kogi da Abuja. An shiga ruɗani yayin da wasu ke tambayar yadda mutanen da ake nema ke samun damar mallakar takardun tafiye-tafiye da wuce matakan tsaro ba tare da an gano su ba. Amma jami’in DSS ya ce wannan tambaya ta shafi sauran hukumomi da ke bayar da fasfo da kula da tafiye-tafiye. Ya ƙara da cewa, “Galadi yana hannunmu yanzu kuma yana amsa tambayoyi. Za a gurfanar da shi a kotu bayan...
Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Kin san komai a rayuwa akwai abin da Allah ya tsara maka kuma duk abin da Allah ya tsara maka za ka ga sai ya tabbatu, ni dai farko mahaifiya ta zan iya ce miki tsohuwar furodusa ce ta taba ‘producing film’ a da’, Momi Jamila Haruna Allah ya ji kanta kawar ta ce tare suke tun muna yara ba mu san za mu shiga harkar ba, har muka shiga harkar. Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance? Eh! to, kin san ita rayuwa ba za ka ce baka samu irin akasi ko damuwa da wannan ba, amma ni dai gaskiya zan iya ce miki Alhamdulillahi ni dai...
Samar da kyakkyawar sadarwa a tsakaninku Yawan magana da sadarwa mai kyau na hana matsala girma. Idan wani abu ya dame ku, kada ku boye, ku gaya wa juna ta hanya mai dadi da girmamawa. Gujewa kwatanta rayuwarku da ta wasu Kowanne aure yana da nasa halin. Kada ku kwatanta rayuwarku da ta wasu, domin hakan yana iya jefa ku cikin damuwa ko rashin godiya. Hana magulmata samun damar shiga tsakaninku Magulmata da masu kyashi suna iya haddasa matsala a aure. Kada ku bari mutane su rarrashe ku da magana mara amfani ko su haifar da rashin fahimta. Bai wa Juna hakkoki Aure yana da hakkoki. Miji yana da nasa, haka ma mata. Ku rika bai wa juna hakkin da...
Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun. Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon. Kai tsaye sojojin suka kai hari kan sansanonin ’yan ta’addar da ke Garin Malam Ali da Garin Glucose da kuma da Ukuba, waɗanda ke cikin Dajin Sambisa. Wannan matakin da aka ɗauka ya biyo bayan jerin hare-hare da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Talata kan sansanonin sojoji guda uku a Rann da Gajiram da kuma da Dikwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu....
A ranar Talata ma, an sake kai hari a ƙauyen Kungurki. Jaji, wanda ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce bai dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa sama da jihohi 20 na fama da irin wannan matsalar. “Ina ganin idan za a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, to ya kamata a yi hakan a wasu jihohi sama da 20. Matsalar tsaro ta zama ta ƙasa baki ɗaya, ba na yanki guda ba. Wannan ba siyasa ba ce. Idan ba mu ɗauki mataki yanzu ba, lamarin na iya shafar ƙasa gaba ɗaya,” in ji shi. Dangane da kiraye-kirayen amfani da dakarun haya daga ƙasashen waje...
Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum. Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar. Rashin kyawun sakamakon jarabawar, wadda sama da ɗalibai miliyan 1.5 suka kasa samun mako 200 ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. A yayin da wasu suka ɗora laifin a kan matsalar na’ura, wasu kuma sun zargi rashin kyakkyawan shiri da kuma rashin iya kula da lokaci daga ɓanagaren dalibai. NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar za ta sake shirya musu wata jarabawar. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan dalilan Hukumar ta JAMB. Domin sauke shirin, latsa nan
Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki. Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Rayuwar Ɗalibai ya wallafa. Ta gargaɗe su cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai faru a wajen da ba ta amince da shi ba ba. Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an rufe ɗakunan bisa doka da oda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero. Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya. NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar s unguwar Kaura da ke cikin birnin Zariya, a Jihar Kaduna. Masarautar ta aike da ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC. A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa. Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido Shugaban majalisar ya karanta wasiƙar a zaman majalisa na ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Masu ya fice daga NNPP tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, kuma ya samu amincewa ga shugabannin APC a dukkan matakan da suka dace su karɓe shi. Ɗan majalisar ya...
A yayin da ta bayyana cewar a shiri na gaba za a zakulo matan karkara sosai ta ce ta jagoranci shirin ne ba wai a matsayin kashin kan ta ba, sai dai domin ta karfafawa mutum mai kishin al’umma da hangen nesan inganta rayuwar su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce: “A yau ni ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya. Ba kawai ɗan watsa shirye-shirye ba ne ni, ni ne babban mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya. “Don haka za ka ga yadda burin da ake ganin kamar an kashe shi shekaru da dama da suka wuce, ya dawo ya amfanar.” Ya ce kafin ya zama minista, ya mallaki tashar rediyo da talbijin har ma da gidan jarida. Ministan ya buƙaci matasa da kada su yi watsi da burin su ko da ba sa ganin damar cimma buƙatar su. Ya ce shauƙin sa ne yake motsa shi wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya ta hanyar ƙarfafa fahimtar kafofin sadarwa. Idris ya kuma bayyana cewa...
Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar. Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello. An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57 Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya...
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
Eze na cikin jerin da rundunar tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu da yake da shi wajen kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Kudu maso Gabas. Manjo Janar Kangye, ya ƙara da cewa, a watan Afrilu, sojojin sun ceto mutane 173 da aka yi garkuwa da su, sannan sama da ‘yan ta’adda 204 da iyalansu sun miƙa wuya. Haka kuma, sun kama mutane 430 da ake zargi da satar mai da wasu laifuka daban-daban. A ƙarƙashin Operation DELTA SAFE, an daƙile satar mai da darajarsa ta haura Naira biliyan 1.9 a cikin mako guda. Sun ƙwato sama da lita miliyan ɗaya ta ɗanyen mai da kuma dubban litoci na man fetur da wasu nau’inkan haramtattun mai....
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.” Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta don yada tsoro, yada labaran karya, domin samun sabbin mabiya. A saboda haka, ya bukaci ‘yan jarida da editoci da su rungumi dabi’ar kishin kasa wajen bayar da rahoto ta hanyar guje wa kanun labarai masu daukar hankali ga farfagandar ta’addanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka zauna jarabawar bana, kusan miliyan 1.53 — wato kashi 78 cikin 100 — ba su samu maki 200 ba. Sai dai ɗalibai 12,414 kacal suka samu maki 300 ko sama da haka. Ministan ya jaddada cewa wannan mataki na hana satar amsa zai taimaka wajen samar da ƙaimi na ɗalibai masu ƙwazo da amana, tare da ƙarfafa ingancin ilimi a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ƙara da cewa Ganduje mutum ne da kullum yana cikin yi wa ma’aikatansa fara’a. Ya ce masu yaɗa bidiyon na ƙoƙarin tada rikici ne domin dalilan siyasa. “Wannan ba zai rage farin jinin Ganduje ba,” in ji shi. “Ya yi wa Jihar Kano aiki tuƙuru, yanzu kuma yana yi wa ƙasa. ‘Yan adawa ba sa jin daɗin yadda APC ke ƙara ƙarfi a ƙarƙashin jagorancinsa.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar tsaron dake lura da aikin Hajji ta kama wani ɗan ƙasar Ghana bisa zargin ƙoƙarin fitar da mata huɗu daga ƙasashen waje zuwa Makkah ba tare da lasisin Hajj ba. Matan, waɗanda ke cikin mota, an yi amfani da ɗakin kaya na motar domin ɓoye su don gujewa dokokin Hajj. Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025 Rundunar tsaron ta kama direban motar tare da mata huɗun, sannan aka miƙa su ga hukumar da ta dace don aiwatar da hukuncin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Khalifa Aminu, matashi ne mai shekaru 19 wanda ya ƙirƙiri na’urori da abubuwan ban mamaki waɗanda hatta mutanen da suka zurfafa karatu a fannin kimiyya da kere-kere ba su sami irin wannan nasarar ba. A tattaunawarsa da Aminiya, Khalifa wanda ya ce da kyar ya iya kammala karatunsa na sakandare, ya bayyana yadda ya kirkiro wata sabuwar na’ura da ke iya gano ma’adinan karkashin kasa ko bam a cikin dakika guda, da kuma tabarau da ya kirkiro mai taimaka wa makafi wajen yin tafiya ba tare da sun yi karo ko sun fada cikin wani hadari ba. Hajjin Bana: Gwamnatin Jigawa ta aika wa NAHCON Naira biliyan 6 ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe Ɗan asalin Jihar Kano,...
A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai. Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji. Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.” Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya...
Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Miliyoyin mutane sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a ƙasar Sifaniya da wasu sassan Portugal. Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama. Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Sai dai asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto. Shugabar gwamnati a yankin Madrid ta ce “abin da za mu yi shi ne mu nemi gwamnatin tarayya ta ayyana shiri na gaggawa don sojoji su kare doka da oda.” Kamfanin lantarki na Sifaniya ya ce an gyara matsalar a yankunan arewaci da kudancin ƙasar. Har yanzu dai ba a san abin...
Wannan naɗi ya zama wani babban mataki a cikin mulkin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiyaye al’adun masarautar tare da haɗa kan al’umma. Sai dai kuma a cikin wannan wata ne Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido Sanusi II, ya fara naɗa Alhaji Mannir Sanusi (Hakimin Bichi) a wannan muƙami bayan rasuwar tsohon Galadima. Za a iya cewa dai yanzu bayan Sarakuna biyu Kano na da Galadima biyu da aka naɗa a wata guda sakamakon Sarkuna biyun dake da’awar zama halattaccen Sarki, duk da dai Sarki Sanusi Lamido II shi yake gidan Rumfa yayin da Sarki Aminu ke gida masauƙin baƙi da na Nassarawa da ya mayar da shi sabuwar fadarsa. Daga kanmu, magana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti. “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar. Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin. Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar. ...
Haka kuma, ya soki jam’iyyar Galadima wato NNPP, yana mai cewa tana cike da rikice-rikice, saɓanin APC a ƙarƙashin shugabancin Ganduje wadda ke tafiya cikin daidaito. Okpala ya kammala da cewa Ganduje ya mayar da hankali wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba, kuma ba zai tsaya sauraren “maganganun marasa tasiri” kamar na Galadima ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...
An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
A sakamakon haka, an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya bisa tuhumarsa kan wannan laifin wanda kuma ya amsa laifin lokacin da aka karanta masa tuhumar. A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun, Mai shari’a Nasir Ahmad ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, da tarar Naira 20,000, da karin ɗaurin watanni shida a gidan yari, da kuma bulala arba’in. Kotun ta ce, an yanke wannan hukuncin ne don ya zama izini ga masu shirin aikata irin wannan laifin a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2025, domin samun rahoto kan sulhun, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya. Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar. Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai...
Matatar Mai ta Ɗangote ta rage farashin litar man fetur zuwa Naira 865 ga dillalai masu saya daga wurinta. A safiyar Alhamis hukumomin Matatar Ɗangote suka sanar da dillalai dangane da ragin naira 15 daga tsohon farashin man na naira 880.
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin. Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar. “Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a Katsina. Za mu yi amfani da duk wata hanya da albarkatu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Kwamishinan. Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
An yi nasarar kashe wani ɗan bindiga yayin da jami’an tsaro suka kuɓutar da mutane 10 da aka sace a wani samame na haɗin gwiwa a karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina. Waɗanda aka ceton da suka haɗa da mata shida da maza huɗu, an yi garkuwa da su ne daga kauyukan Kiroro, Kabbi, da Dogon Marke da ke karamar hukumar ta Musawa. Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 A Katsina Sin Ta Fitar Da Takardar Matsayarta Kan Alakar Tattalin Arziki Da Amurka A cewar sanarwar da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na Katsina, Nasir Mua’zu ya fitar, an kai samamen ne da misalin karfe 10 na daren ranar 8 ga watan Afrilu a...
Da ya ke magana kan ziyarar tawatar NBTE, Rector ɗin ya ce aikin sahalewa na da matuƙar muhimmanci domin gano irin ƙoƙari da azamar makaranta a cikin shekaru biyar da suka gabata da nufin tabbatar kayan koya da koyarwa da malamai suna nan kan tsarin da aka amince da tafiyar da su tun da farko. Ya tabbatar da cewa kwasa-kwasai har guda 78 ne jami’an NBTE suka nazarta a yayin wannan ziyararz, “Tawagar sun gama aikin su na ziyarar, yanzu haka muna zaman jiran sakamakon bincike da bin sawun nasu ne,” ya ƙara shaida. A nata ɓangaren, Dakta Fatima Umar, daraktan shirye-shiryen kwalejoji kuma jagorar tawagar na NBTE, ta buƙaci kwalejin Kimiyya da fasaha na gwamantin tarayya da ke Bauchi...
Babban kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya amince cewa zai yi wuya a shawo kan matashin dan wasan gaban Arsenal Ethan Nwaneri ya buga wa Nijeriya wasa, an haifi Nwaneri a Kasar Ingila amma kuma mahaifinshi dan Nijeriya ne yayin da mahaifiyarsa ta ke ‘yar Ingila. Dan wasan mai shekaru 18 ya riga ya bugawa Ingila wasa amma har yanzu yana iya sauya sheka zuwa Nijeriya, Chelle ya yi ikirarin cewa kocin tawagar Ingila da ake wa lakabi da Three Lions, Thomas Tuchel, shi ma ya na sha’awar ya yi amfani da dan wasan mai buga gaba a matakin kasa. Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Legas, Mutane 10 Sun Kamu CMG Ya Nuna Fina-Finan “Documentary” Bisa Jigon “Kama Hanyar Samar...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama. Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin. An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a shekarar 2017 ba tare da sanin dangin da ya kashewa ‘yan uwa ba. Bayanan kotun sun nuna cewa mai shari’a O.A. Taiwo na Kotun 26, Babban Kotun Ikeja, ya bayar da belin Musiliu a kan Naira miliyan 1 tare da mutane biyu. A hukuncin kotun, Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, “Sashe na 115(1) na dokar shari’a ta shekarar...
Da suka ga cewa ba za su yi nasara ba, sai suka tsere suka bar waɗanda suka sace. An kama mutum ɗaya, Ibrahim Musa, mazaunin ƙauyen Abuni a Ƙaramar Hukumar Awe. Ya ya bayar da muhimman bayanai da ke taimakawa wajen bincike. Kwamishinan ya jinjina wa jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane bisa ƙoƙarinsu kuma ya jaddada aniyar ‘yansanda na yaƙi da aikata laifuka. Ya buƙaci jami’ansa da su ci gaba da jajircewa don tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu. Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 20, Usman Sagiru, bisa zargin kashe wani ɗan Bijilanti a tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II bayan Sallar Eid. Iftila’in ya faru ne da ƙarfe 12:40 na rana a Lahadi, lokacin da ayarin Sarkin Kano ke watsewa daga filin Sallar Idin. A cewar kakakin Ƴansanda SP Haruna Kiyawa, ana zargi Sagiru da wasu da suka tsere da soka makami ga wani ɗan sa kai mai suna Surajo Rabiu daga unguwar Sabon Titi Jaba, wanda ya mutu sakamakon raunin. Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II Wani ɗan Bijilanti, Aminu Suleman daga...
Ku kasance masu tausasawa da rahama, ku sadar da zumunta, ku sanya farin ciki azukatan al’umma kuma ku yada farin ciki, sannan ku nemi kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ji da ɗa’a ga umarnin shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum. 2-Maganin Hawan Jini (Hypertension) Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini. Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma yamma. 3-Maganin Basir Sadidan Idan ana fama da basir, za a iya amfani da ganyen mangwaro don rage kumburi da ciwo. Bayan an samu wannan ganye na mangwaro, sai a busar da shi a kuma daka shi har sai ya zama gari. kana sai a dauki cokali daya na garin a hada da rabin kofi na ruwan dumi, sannan a zuba zuma a ciki...
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da kewaye. Rundunar ta ce a jiya Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar DSP Yazid, a yayin daƙile harin ne ’yan sanda suka kashe gomman ’yan bindigar ciki har da Ɗan Mudale wanda ya addabi al’ummar yankin. Ya ce rundunar haɗin gwiwa da ta haɗa da ’yan...
Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta. danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun 2025, wanda ya kai yawan Ganga 1,465,006 da ake hakowa a kullum. A yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da bincike, domin a gano musababbin abinda ya janyo fashewar man Bututun dan Man da irin asarar da aka tabka da kuma yawan adadin wadanda suka samu raunuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Babu wata ɗaliba da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, domin tuni aka sauya wa ɗaliban masauki bisa umarnin jami’ar. Har yanzu dai hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Lokacin da aka samu rahoton faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagoranci babban baturen ɗansanda (DPO) sun ziyarci wurin inda suka ɗauki gawar zuwa babban asibitin Darazo, a nan ne likita ya tabbatar da mutuwarsa,” Wakil ya shaida. Yayin da bincike ya ci gaba da gudana, a ranar 20 ga watan Maris, ‘yansanda suka kama Yau Buba, ɗan shekara 25 mazaunin ƙauyen Minchika da ke Darazo a jihar Gombe tare da Mashin ɗin da aka sace daga hannun ɗan Achaɓan da aka kashe. Wakil ya ƙara da cewa, a yayin da ake masa tambayoyi, shi Yau Buba ya bayyana da kansa cewa ya sayi Babur ɗin ne a hannun wani mutum mai shekaru 22 a duniya wato Buba Muhammadu,...
Hukumar yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu, mai shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye a cikin ledojin da ke kama da kwallon alawar cakulati. An cafke ta ne a yayin binciken shigowarta daga jirgin Qatar Airways daga Bangkok ta Vietnam da Doha. Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd), ya ce wannan kamun ya sake nuna yadda masu safarar kwayoyi ke amfani da ‘yan ƙasashen waje don kutsawa da miyagun kwayoyi cikin ƙasar. A cewarsa, NDLEA na ci gaba da daƙile irin wannan yunƙuri ta hanyar bayanan sirri da fasahohin zamani....
Wani Sufeto Dansandan da ke aiki a Jihar Kuros Ribas, ya harbe matar abokin aikinsa har lahira tare da jikkata wasu mutane biyu a harbe-harben da ya yi a ranar Lahadi. Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Labarai a birnin Kalaba, inda ta bayyana cewa jami’an Dansandan ya nuna halayyar da ba ta dace ba kafin ya fara harbe-harben. Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A Ribas Ugbo, ta ƙara da cewa jami’in, naaiki ne a Cibiyar ‘Yansanda ta Atakpa, ya dawo daga aikin dare a wani bankin ‘Microfinance’ kafin afkuwar lamarin. Ta kuma bayyana cewa tuni an kama wanda ake...
An kama wani jami’in rundunar sa-kai ta JTF, Modu Mallam Gana mai shekaru 27 a garin Monguno, bisa zarginsa da harbin wasu gungun matasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da raunata daya. Wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na safiyar ranar 21 ga Maris, 2025, a lokacin da wasu matasa suka tsaya a gaban ofishin dakarun da ke Unguwar Bakin Kasuwa, a Karamar Hukumar Monguno. Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu Yadda ake noman gurjiya Majiyar ta ce wanda ake zargin Modu Mallam Gana ya harzuka da tsayarwar matasan a bakin ofishinsu, lamarin da ya bude musu wuta. Wadanda abin ya shafa — Ya’zainab Bum da...
Sai dai, bisa ladabi da girmamawa ga masarautu, Gwamna Bala Muhammad ya amince da roƙon ɗage Hawan Daushe. Duk da haka, gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda ba a tuntuɓe ta ba kafin yanke wannan shawara. Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tare da sarakuna domin kyautata zamantakewa da ci gaban jihar. Ga mutanen da wannan ɗagewa ta shafa, gwamnati ta fahimci damuwarsu, amma ta yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace a nan gaba don kauce wa irin wannan matsala. Gwamnan ya yi fatan jama’a za su yi bikin Sallah cikin lumana da farin ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Mzee Ernesto Muinuchi Kapinga, wani mutum ne daga wani karamin kauye a Tanzaniya, wanda yake da iyali na musamman. Ya auri mata 16, yana da ’ya’ya sama da 100 da jikoki 144. A kwanakin nan, maza da yawa suna ta kokarin samun iyali da neman haihuwa, duk da ana kallon karuwar iyali kamar karin matsin rayuwa ne mai yawa. DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas Kula da yara sama da biyu ko uku abu ne da ba za a yi tsammani ba ga galibin matasa, amma kuma akwai maza irin su Mzee Ernesto Muinuchi Kapinga wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen fadada...
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa. Ya ce, “Shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi,” yana mai cewa mahaifinsa ya ba da fifiko ga ci gaban tattalin arziki da samar da dama ga matasa. Ya kara da cewa, “Shi ne kawai shugaban da ya kiyaye mutanenku a gida, tun lokacin da ya kasance gwamna har ya zama shugaban kasa. Shugaban da ya dauki matasa da muhimmanci, ya samar da dandali don...
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa. Ya ce, “Shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi,” yana mai cewa mahaifinsa ya ba da fifiko ga ci gaban tattalin arziki da samar da dama ga matasa. Ya kara da cewa, “Shi ne kawai shugaban da ya kiyaye mutanenku a gida, tun lokacin da ya kasance gwamna har ya zama shugaban kasa. Shugaban da ya dauki matasa da muhimmanci, ya samar da dandali don...
Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Legas na jam’iyyar PDP, Dr. Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya sanar da koma wa jam’iyyar APC mai mulki. Wannan sanarwar ta zo ne bayan kwanaki biyu kacal da ya fice daga jam’iyyar PDP. Jandor ya ba da sanarwar koma wa jam’iyyar APC ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke Ikeja a ranar Litinin. Ya bayyana cewa ya yi shawarwari da shugaban ƙasa Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da wasu manyan mutane a fagen siyasa bayan ya fice daga PDP. El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Haɗa Abokan Hamayya Don Yaƙar APC A Zaɓen 2027 Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin...
Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu. Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu. An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da gidauniyar ta fitar, wadda Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya sanya wa hannu. A cewar takardar, dole ne El-Rufai ya fito ya yarda da laifinsa sannan ya nemi afuwar gidauniyar, ɗalibanta da jagoranta, Sheikh Ɗahiru Bauchi. Gidauniyar ta zargi tsohon gwamnan...
Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi (Sarkin Dawaki Babba) bai gamsu da wannan hukunci ba, don haka ya shigar da ƙara yana neman a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci. Ya shigar da Gwamnatin Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar NSCDC, da sauran hukumomin tsaro ƙara. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da buƙatar Dan Agundi, inda ta ce akwai hurumin shari’a a cikin ƙarar. Mai shari’a Abang ya bayyana cewa kotu dole ne ta yi adalci wajen yanke hukunci. Wannan hukunci yana nufin cewa dole ne dukkan ɓangarorin su ci gaba da zama yadda suke kafin Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci. Bugu da ƙari, kotu ta umarci Dan...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed a fadar gwamnati, inda suka yi wata ganawar sirri. Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Da Taɓarya A Bauchi Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters Duk da cewa dalilin ziyarar bai fito fili ba, ana hasashen cewa yana da alaƙa da shirin siyasar 2027, inda ake ta raɗe-raɗin haɗakar ‘yan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki. Taron ya ƙara hura...
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi. Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar da yanayin na zafi kan haifar a jihohi goma sha tara na ƙasar daga yankin arewa ta tsakiya da yankin gabashin ƙasar. Kan haka ne muka tuntuɓi likita domin ya yi mana ƙarin bayani game da cututtuka biyar da aka fi kamuwa da su a lokacin zafi da kuma hanyoyin kare kai. Sanƙarau – Dakta Hassan Ibrahim, likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya...
SP Adeh ta kuma ce jami’an ‘yansanda sun ceto wasu mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokacin farmakin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masana na gargaɗin cewa idan NNPC ta daina sayar wa matatar Dangote mai a naira, hakan na iya haifar da hauhawar farashin man fetur, maimakon rage farashin da ake tsammani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An haife shi a ranar 21 ga Fabrairu, 1949, kuma ya yi karatu a Jami’ar Ohio da ke Athens a Amurka, a 1981, da Jami’ar Leicester ta ƙasar Birtaniya a 1987. Ya yi aiki a kamfanin jaridun New Nigerian, da hukumar talbijin ta NTA, da Ofishin Yaɗa Labarai na Amurka (USIS). Haka kuma ya yi koyarwa a Kaduna Polytechnic, ya yi aiki a Bankin Arewa da kuma Bankin Union inda a nan ya yi ritaya a ranar 26 ga Yuni, 2005. A cikin saƙon ta’aziyyar sa a ranar Asabar, Minista Idris ya bayyana rasuwar Malam Kabir Ɗangogo a matsayin babban rashi ga Nijeriya da fannin sadarwa a nahiyar Afirka. Ya ce: “Mutuwa ta ƙwace mana ƙwararren ma’aikaci...
Haka nan, wasu manyan jiga-jigan NNPP daga ƙaramar hukumar Gwale, Mahmoud Salisu Gwale da Farouk Ahmed Gwale, su ma sun koma APC. Sanata Barau ya tabbatarwa da al’ummar Nijeriya cewa kofa a buɗe take ga kowa. “A matsayina na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ina yi wa kowa hidima. Ko da kai ɗan PDP ne, LP, Kwankwasiyya, ko wata jam’iyya, ina tare da kai. Idan kana son shigowa APC, jam’iyyar jama’a, muna maraba da kai. Ƙara yawa, ƙara daɗi!” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Daga ƙarshe sanarwar ta ƙara jaddada ingantattun ƙa’idojin karatu a BUK, wanda ta ce ba za ta lamunci satar jarrabawa ko laifuffuka makamantan haka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da ƙalubale – ba don sun shirya mishi ba kuma ba don sun gaza shiryawa ba. Wani rukunin waɗannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana. Domin sauke shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
Archbishop Okoh ya buƙaci jama’a da su zauna lafiya tare da bin hanyoyin doka domin shawo kan lamarin. Ya ce CAN ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an samar da daidaito a tsarin ilimi, ba tare da nuna bambancin addini ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamar yadda ba a lokaci guda a ke gina dabi’u ba, haka nan ba zai yiwu a rusa su a lokaci guda ba. mutum na gina dabi’a ne ta hanyar yin mu’amala da mutane. Gina dabi’un na farawa daga shekarun yarinta, saboda a sannan ne a ke koyon al’adu, tarbiyya da girmama manya. Har zuwa mutuwan mutum ya na mu’amala ne da mutane ya na gina sabbin dabi’u. Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da...
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta bai wa ilimi fifiko, wanda Kano ce a gaba wajen ware kasafin kudi mai yawa a shekarar 2024 da 2025 a fannin Ilimi. Bugu da kari, gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin tabbatar da matasa sun samu ingantaccen ilimi wanda zai ba su damar yin fice a tsakanin takwarorinsu. Da yake magana tun farko, Gautier Mignot, jakadan Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, kuma jagoran tawagar, ya bayyana cewa, sun zo Kano ne domin halartar bikin baje kolin karatu na Turai da aka shirya yi a ranar 27 ga Fabrairu, 2025 a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Sakamakon wannan ragin da aka samu, yanzu gidan mai na MRS zai sayar da man a jihar Legas a kan naira 860, sai mutanen da suke yankin kudu maso yamma kuma da za su saya a kan naira 870, sai kuma mutanen Arewa da za su saya a kan naira 880, sai mutanen kudu maso kudu da kudu maso gabas da za su saya akan naira 890. Kamfanin ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su taimaka wajen ganin sauƙin ya je inda ake bukata, domin an yi ragin ne don sauƙaƙawa al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Sakamakon binciken da kwamitin ya yi, zai tantance matakin da za a dauka na gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan ya yi zargin cewa, furucin Shugaban na daya daga cikin dalilan da suka sa Allah ya karbe mulki daga jam’iyyar duk da nasarar da ta samu a zaben gwamna na 2023. Amma da yake mayar da martani, Abbas ya yi zargin cewa Ata ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben 2023, kuma sun bayyana haka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Abdullahi Abbas ya ce, “A gare mu ‘yan APC Yusuf Ata ba dan jam’iyyar APC ba ne. Ba mu ma san dalilin da ya sa aka nada shi minista ba. Duk fadin jihar Kano a karamar hukumarsa ne muka zo na uku a zaben 2023. “Ba mu san cewa an nada shi minista ba. Mun...
Daga karshe, jarumin wanda ya shafe shekaru fiye da 10 a Masana’antar Kannywood, ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim, su tabbatar sun zama masu hakuri da biyayya ga na gaba da su, muddin suna son samun nasara a rayuwarsu ta jarumai. “Dole ne ka kasance mai hakuri a rayuwa, domin kuwa babu wanda ya zama wani abu ba tare da ya sanya hakuri a cikin al’amuransa na yau da kullum ba, duk wanda ka gani ya zama wani abu, ko ya samu wata daukaka ko shahara a rayuwa, to dole akwai kalubalen da ya fuskanta, domin kuwa ko a makaranta sai an ware wani lokaci da za a yi jarrabawa; domin gane masu fahimta da wadanda ba sa...
Ma’aurata da ke da tazarar shekaru 45 sun shawo kan masu zolayarsu da batun kiwon lafiya don samun farin ciki na musamman a baya kuma sun ce sun ki jin kunyar waɗansu ba su fahimci alakar aurensu ba. Ma’auratan sun shawo kan matsalar da za ta iya shafan huldarsu da wadanda ke son raba aurensu – amma duk da haka sun nace za su yi iya kokarinsu don hana su farin ciki a rayuwar auren. PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu Adrián Narbáez, mai shekara 43 yanzu ya hadu da matarsa Delia Lúkuez mai shekara 88, a wani baje kolin fasaha a shekara ta 1998, tun yana dan...
Dauda ya kara da cewa, babu wata waka da zai yi ba tare da an bukaci ya yi ta don isar da wani sako ba. Haka zalika, Shugaba Tinubu, ba shi da wani buri na tara dukiya a halin yanzu; illa kawai dai fatan barin tarihi mai kyau a matsayinsa na Shugaban kasa, kamar yadda sauran mazan jiya; irin su Sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa suka bari. Dangane da abin da wasu ke dauka cewa, ana biyana makudan kudade; don yin wakokin da za su kawar da hankalin mutane, su sani cewa; na fi mayar da hankali a kan noma fiye da yadda nake yi wa harkar waka, dalili kuwa; ni manomi ne wanda a yanzu haka duk...
Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu. A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci ta hanyar yin adalci. Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa “Mutumin nan Abacha—kullum sukarsa da cin amanarsa kuke yi a asirce. Tarihi zai tuna ka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun ci gaba da ƙoƙarin rage maka ƙima. “A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai. Lallai kai...
Sun ci gaba da cewa, tattalin arzikin ya karu zuwa kaso 3.5, a zango na uku a 2024, daga kaso 3.2 a zango na biyu a 2024. A cewarsu, Nijeriya ta samu wannan nasarar ce, saboda tsaurara tsare-tsaren hada-hadar kudade, inda kuma fannin da bai shafi Man Futur na kasar ba, ya bayar da gagarumar gudunmawa, tare da samar da tsare-tsaren sakuka yin hada-hadar kasuwanci a kasar. Sun kara da cewa, fannin Mai ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, musamman duba da yadda Matatar Man Fetur ta dangote ke samar da yawan Man a kasar, inda hakan ya kuma daidaita samar da Man da kuma rabar da shi, a cikin farashi mai rahusa. Sai...
Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu. An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a Gombe Gini ya faɗa kansu ne ba zato ba tsammani, lamarin ya haddasa mummunan tashin hankali tare da jefa ɗalibai da dama cikin baraguzan gini. Bayan aukuwar lamarin, an yi gaggawar ceto ɗaliban, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Ƙwararru na Potiskum domin ba su kulawa. Duk da an samu nasarar ceto da dama daga cikinsu, wata ɗaliba ta rasa ranta...
Yanzu-yanzu: Gini Ya Rufta Wa Ɗaliban GGTC Potiskum