Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe
Published: 24th, August 2025 GMT
Amina Yakubu, ɗaliba a ajin farko a Sashen Ilimin Halittu na Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta rasu a wani hatsari da ya rutsa da ita a Damaturu.
Sanarwa daga ofishin mataimakin shugaban jami’ar da Abdulmumin Kolo Gulani, ta fitar ta tabbatar da rasuwar ɗlaibar.
Babban malamin Tijjaniyya, Sheikh Umar Bojude, ya rasu Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a GombeƊalibai da malaman jami’ar sun bayyana jimaminsu game da rasuwarta.
Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Asabar a kan titin Gujba daura da ƙofar jami’ar.
Keke Napep da ɗalibar ke ciki ne ya yi taho mu gama da wata mota wadda ta murƙushe su.
A cewar sanarwar, wasu mutum huɗu sun samu raunuka.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
“Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.
“Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp