HausaTv:
2025-04-18@07:36:01 GMT

Sharhi: Tattaunawa Zagaye Na Farko Tsakanin Iran Da Amurka A Oman

Published: 13th, April 2025 GMT

Sharhin zai yi dubi ne game da tattaunawar da aka fara gudanarwa zagaye na na farko tsakanin Iran da Amurka a birnin Mascut fadar mulkin kasar Oman, inda gwamnatin kasar Oman din take shiga tsakani a wannan tattaunawa wadda aka fara gudanarwa.

Tun da safiyar Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka.

Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa  Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran.

A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya.

Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai  mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa Kazim Garib Abadi, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ambata.

Iran da Amurka suna tattaunawa ne ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman ba ta gaba da gaba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, kwana guda gabanin tattaunawar a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, akwai damammaki da dama na diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu

Baqaei ya rubuta a dandalin  X cewa, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.”

“Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan tattaunawa,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.”

A ranar Litinin din makon da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya ba da sanarwar cewa gwamnatinsa za ta shiga tattaunawa da Iran.

Kafin zuwa ga wannan tattaunawar dai bangarorin biyu  sun yi musayar kalamai masu zafi, inda Trump ya yi barazanar daukar matakin soji idan tattaunawar ta ci tura.

Dangane da gargadin na Trump, wani babban mataimaki ga jagoran Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya ce Iran za ta iya daukar dukkanin matakan da ta ga sun dace a kan wannan lamari.

Ganawar ta ranar Asabar na zuwa ne biyo bayan wata wasika da Trump ya aikewa Sayyed Khamenei a watan da ya gabata, inda ya bukaci Tehran da ta shiga tattaunawa, tare da yin gargadin cewa matakin soji na kan teburi idan Iran ta ki amincewa.

Tehran ta bayyana aniyar ta na shiga tattaunawar kai tsaye amma muddin Washington ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na matsin lamba mafi tsanani a kan Iran, to kuwa tabbas wannan tattaunawa ba za ta iya haifar da da mai ido ba.

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce Amurka na da masaniya kan irin karfin kare kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi, yayin da ya ce kasar ta shirya tsaf domin kare kanta.

Ya kuma jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta yarda da Washington ba, amma duk da haka za ta gwada ta yayin tattaunawar,” in ji Abbas Araghchi.

Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta neman yaki, amma idan ya zama dole ta san yadda za ta kare kanta. »

“Muna da shaku kan aniyar Amurka kuma ba mu da tabbacin cewa suna da niyyar gudanar da tattaunawa ta gaske, amma za mu gwada su.”

Haka nan kuma jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi watsi da zargin kasashen yamma – karkashin jagorancin Washington – cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na neman mallakar makamin nukiliya.

Ya ce zargin da ake yi wa Iran na neman mallakar makamin nukiliya, zargi ne mara tushe balantana makama.

Dangane da bayanan da aka yi ta yadawa musamman daga bangaren mahukuntan Amurka na cewa tattaunawar za ta gudana ne tsakanin Iran da Amurka gaba da gaba, Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan dangane da wannan tattaunawa wani babban yunkuri ne na diplomasiyya.

Ya fayyace cewa sabanin wasu fassarori da aka yi a baya-bayan nan a game da batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kokarin bayyana ra’ayi ne na gaskiya da bude hanyar diflomasiyya.

Dangane da kalaman Trump da ya yi a ranar litinin, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take domin ganin an cimma matsaya, inda za ta halarci tattaunawa a kasar Oman a ranar Asabar.

Ya kuma kara da cewa, wannan ba sabon lamari ba ne, domin ita kanta Amurka tana tsakiyar yin shawarwari kai tsaye game da batun Rasha da Ukraine, batun da ya fi zafi da sarkakiya ta fuskar siyasa da tattalin arziki a mataki na kasa da kasa.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ministan harkokin wajen a wannan tattaunawa Iran da Amurka

এছাড়াও পড়ুন:

An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya

An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya.

Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu.

An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano

Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki.

Shekaru sama da 50 ke nan da kafa rundunar sojin Nijeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami.

Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shi ne karon farko.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha
  • Iraki Ce Zata Amfana Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka: Inji Sayyed Ammar Hakim
  • Araghchi: babu tattaunawa kan batun tace sinadarin uranium
  • Rasha ta ce tana bibiyar tattaunawar Iran da Amurka matuka
  • An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya
  • Kakakin Sojojin Kasa Na Dakarun IRGC Ya Ce Butun Tsaron Kasar Iran Da Karfin Sojojin Kasar Ba Abinda Tattaunawa Da Makiya Bane
  • Jagoran Ya Ce: Iran Ba Ta Kallon Tattaunawan Iran Da Amurka A Matsayin Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu
  • Iran Ta Sanar Da Kasar Oman A Matsayin Wajen Tattaunawa Na Gaba Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
  • Kokarin Da Iran Take A Tattaunawa Da Amurka Shi Ne Dage Mata Takunkuman Zaluncin Da Aka Dora Mata
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Zanta Da Tokwaransa Na Kasar Kuwait