Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Amurka da Iran
Published: 12th, April 2025 GMT
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka.
Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin
Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar ta ce “Hussein ya karbi bakuncin mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh a ranar Juma’a a gidansa da ke birnin Antalya na Turkiyya.
Sanarwar ta kara da cewa “a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen dake makobtaka da juna da kuma hanyoyin karfafa su a fannoni daban-daban.”
“Hussein ya yi maraba da tattaunawar ta tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka, yana mai bayyana fatansa na cewa a wannan shawarwarin za a samu sakamako mai kyau da zai taimaka wajen samun kwanciyar hankali a yankin.”
Shi ma babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Rafael Grossi ya bayyana fatansa na ganin an cimma yarjejeniyar nukiliyar tsakanin Iran da Amurka cikin gaggawa.
Grossi ya ce yana da kwarin gwiwar cewa bangarorin biyu za su iya warware sabanin ra’ayi a fannin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar yin shawarwari kafada-da-kafada da hadin gwiwa don cin moriyar juna.
Stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana fatansa game da tattaunawar ta tsakanin Amurka da kuma Iran.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: bayyana fatan
এছাড়াও পড়ুন:
Arakci: Mun Yi Tattaunawa Mai Kyau Da Mahukuntan Kasar China
Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar.
Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin wajen China, wacce take mai muhimmanci, kuma kusan dukkanin bangarorin da suka shafi alakar tsakanin kasashenmu biyu mu ka tattauna, haka nan kuma batutuwa da su ka shafi siyasar kasa da kasa.”
Arakci ya kara da cewa; Da akwai fahimtar juna a tsakaninmu, musamman abinda ya shafi batun makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, da tataunawar da ake yi da Amurka.”
Haka nan kuma ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da su ka tattauna da su ka hada siyasar Amurka da halayyarta ta nuna karfi, da kokarin da take yi na mamaye fagen siyasar kasa da kasa.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi Magana akan ziyarar da shugaban kasar Iran zai kai zuwa kasar China wacce za ta kasance ba da jimawa sosai ba.