Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya.

 

Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan ci gaba da bude kofarta, da aiki tare da abokan hulda irinsu Sifaniya wajen goyon bayan tsarin cudanyar sassa daban daban, da goyon bayan dunkulewar salon raya tattalin arziki da cinikayya marar shinge, da samar da karin hidimomi, da kayayyaki masu inganci ga kasashen biyu ta hanyar hadin gwiwa da juna, da mutunta juna, da amfanar da al’ummunsu.

(Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yaƙin M23 Ya ci Gaba a Congo Duk da Sulhu da Rwanda

Bayan da ƙasashen biyu maƙwabtan juna na Congo da Rwanda suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da Donald Trump ya bayyana a matsayin mai cike da tarihi, jagoron na Amurka ya jinjinawa shugabannin ƙasashen biyu waɗanda ya ce sun yi hangen nesa wajen amincewa da kawo ƙarshen zubar da jinin dubban mutane tsawon shekaru.

An dai haska wannan zaman sanya hannu kai tsaye ta gidajen talabijin, inda shugabannin biyu wato Felix Tshisekedi na Jamhuriyyar Congo da Paul Kagame na Rwanda suka rattaɓa hannu a yarjejeniyar a gaban idon Donald Trump can a birnin Washington.

A cewar Trump shugabannin biyu sun ajje banbance-bambancen da ke tsakaninsu wajen rungumar zaman lafiya don jama’arsu.

Sai dai an sanya hannu a yarjejeniyar can a Washington dai dai lokacin da ake ganin ci gaban yaƙi tsakanin Sojin Congo da mayaƙan M23 da Rwanda ke marawa baya a kudancin lardin Kivu.

Babu dai wakilcin M23 a wannan tattaunawa ta Washington, hasalima basu aminta da yarjejeniyar da ka cimma a zaman ba, maimakon haka suna halartar nasu taron na daban wanda Qatar ke jagorantar sulhunta su da Congo a birnin Doha.

Masu sharhi na ganin  abu ne mai matuƙar wahala, yarjejeniyar ta birnin Washington ta yi tasiri wajen kawo ƙarshen wannan yaƙi na shekaru.

Yarjejeniyar na zuwa a dai dai lokacin da Amurka ke son zuba jari a ɓangaren haƙar ma’adinai a Congo inda a gefe guda itama Qatar ke faɗaɗa shirinta na zuba jari a ƙasashen Afrika.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
  • Yaƙin M23 Ya ci Gaba a Congo Duk da Sulhu da Rwanda
  • Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda 20, kwangilolin haɗin gwiwa na fasaha guda biyar
  • Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
  • Akwai hannun ƙasashen waje a rashin tsaron Najeriya —Sheikh Gumi
  • Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump?
  • Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron  Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha