Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya
Published: 6th, April 2025 GMT
Jirgin da ke ɗauke da mutane sama da 200 daga Bali a ƙasar Indonesia zuwa Ostireliya, ya yi juyawar dole bayan wani fasinja ya yi yunƙurin buɗe ƙofarsa yayin da jirgin kamfanin Jetstar ke shawagi a tekun Indiya.
“Mun samu wani jirgin sama ya koma Denpasar (filin jirgin sama na Bali) a daren Talata bayan wani ruɗaɗen fasinja ya yi yunƙurin buɗe ɗaya daga cikin kofofin jirgin kuma ya ci zarafin ma’aikatanmu,” a cewar wata sanarwa da kamfanin jirgin sama ya fitar game da lamarin a daren Litinin, 31 ga Maris.
Hukumomin yankin Bali ne suka fitar da fasinjan daga cikin jirgin.
A wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, wata mata a bayan jirgin ta yi nasarar daga hannun kofar kafin sakon gargadi ya sanar da ma’aikatan jirgin, in ji kyaftin a amsa kuwwa jirgin (sifika).
Bayanai daga shafin sa ido na jirgin na Flightradar24 sun nuna cewa jirgin ya bi ta kan tekun Indiya kimanin sa’a guda a cikin jirgin.
Jetstar bai bayyana ainihin adadin fasinjoji da ma’aikatan jirgin da ke cikin jirgin da ya taso daga Bali zuwa Melbourne ba.
A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce “Tsaro da walwalar abokan cinikinmu da ma’aikatan jirgin shi ne babban abin fifikonmu kuma muna gode musu kan yadda suka amsa lamarin.
“Ba za a taɓa yarda da irin wannan dabi’ar ba, ba za a amince da ita ba a cikin jirginmu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sawagi
এছাড়াও পড়ুন:
‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.
BBC