Burtaniya Ta Soki Gwamnatin Netanyahu Kan Hana ‘Yan Majalisarta Biyu Shiga Cikin Isra’ila
Published: 6th, April 2025 GMT
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne.
Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a amince da shi ba ne, bai dace ba, kuma babban abin damuwa ne,’ in ji Sakataren Harkokin Waje David Lammy, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.
Lammy wanda ya bayyana cewa Birtaniya tana tuntuɓar ‘yan majalisar domin ba su goyon baya, kuma ya bayyana wa hukumomin Isra’ila ƙarara cewa “ba haka ake yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Birtaniya mu’amala ba.”
“Abin da gwamnatin Birtaniya ta sa a gaba shi ne tabbatar da dawowar tsagaita wuta da tattaunawa domin dakatar da zubar da jini, da ‘yantar da waɗanda aka yi garkuwa da su, da kawo ƙarshen rikicin Gaza,” in ji sanarwar.
Jaridar Times ta Israel ta bayyana sunayen ‘yan majalisar da aka hana shiga a matsayin Abtisam Mohamed da Yuan Yang, tana ambato hukumomi na cewa an hana su shiga ne saboda ƙoƙarin su na “yaɗa kalaman kiyayya kan Isra’ila.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a cikin jihar da ƴan ta’adda ko ƴan bindiga ke da iko da ita. Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a ranar Talata.
Gwamna Mutfwang ya ce gwamnatinsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro, musamman ta hanyar farfaɗo da rundunar tsaron cikin gida ta jihar wato Operation Rainbow, domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ana Ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Malam Adamu Fika Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A FilatoYa ƙara da cewa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an dawo da zaman lafiya a sassan jihar da rikice-rikicen ƙabilanci ko na addini suka taɓa. Ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya domin tabbatar da fahimtar juna da daidaiton al’umma.
Gwamnan ya sake jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya. Ya ce kafa ƴansandan jiha zai bai wa gwamnatocin jihohi damar yin tsari da ɗaukar matakan da suka dace da yanayin tsaron yankunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp