Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama tare da tsare Tsohon Ministan Ƙwadago kuma Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Chris Ngige.

Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe ne, ya tabbatar da hakan da safiyar ranar Alhamis. bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewar an sace Ngige.

An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a Indiya Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC

Chukwuelobe, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige yana tare da EFCC. Ba a sace shi aka yi ba.”

Har zuwa yanzu EFCC ba ta bayyana dalilin da ya sa ta tsare Ngige ba.

Ana sa ran hukumar za ta fitar da sanarwa game da kama shi da kuma binciken da ta ke yi a kansa.

Ngige ya zama mutum na biyu daga cikin tsoffin ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da aka tsare a baya-bayan nan.

Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shi ma yana hannun EFCC.

Hukumar ta ce tana binciken Malami ne kan wasu kuɗaɗen dala miliyan 310, wanda aka dawo da su Najeriya.

Sai dai ya musanta tuhumar da ake masa, inda ya bayyana cewa zarge-zargen ba su da tushe.

Masu sharhi a shafukan sada zumunta sun nuna damuwa kan yadda ake tsare tsoffin ministoci ba tare da bayyana dalili ba.

A gefe guda kuma, masu sharhi kan harkar siyasa sun ce irin wannan mataki na EFCC na nuna yadda hukumar ke zage damtse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Duniya Tana Bukatar Amintaccen Madogara, Zaman Lafiya Da Kuma Hadin Kai
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa
  • ‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’
  • Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi AkanDoron Ruwa
  • Manchester United ta shiga zawarcin Sergio Ramos
  • Hamsa: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjeniyar Tsagaita Bude Wuta A Yankin
  • EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige
  • Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu