An Gabatar Da Motar Asibiti Ta Farko Mai ISO Na Matsayin Kasa Da Kasa A Hukumance
Published: 10th, March 2025 GMT
A kwanan nan ne aka fitar da motar daukar mara lafiya ta farko mai ISO na ma’auni na kasa da kasa, wanda tawagar bincike karkashin jagorancin kwararrun Sinawa suka tsara, mai suna motar asibiti mai dakin kebance mara lafiya wato “Negative Pressure Ambulance Medical Cabin Technical Specifications”.
Wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya suna da kayan aikin jinya masu muhimmanci, galibi ana amfani da su don kebe mara lafiya cikin aminci yayin da ake jigilarsu, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen kula da cututtuka daban-daban na numfashi.
Fitar da wannan ma’auni ya gabatar da kayyadaddun kayayyakin aiki da ake bukata a cikin wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya, wanda zai zama abin koyi ga kasashen duniya, kuma zai yi tasiri mai kyau a kan rigakafi da kula da cututtukan numfashi a duniya. Kwararru daga kasashen Sin, Faransa, Italiya da sauran kasashe suka yi hadin gwiwa wajen bincike da tsara wannan ma’auni. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: dakin kebance mara lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da babura a fadin jihar.
Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya da babura a cikin birnin Kano, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya a jihar.
Danladi Karfi ya jaddada cewa dokar da ta haramta zirga-zirgar babura a matsayin sufuri na haya har yanzu tana nan daram, kuma za a aiwatar da ita sosai, inda ya gargadi masu karya doka da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya kara da cewa Kano na daga cikin jihohi mafi zaman lafiya a kasar nan, kuma gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya tayar da hankalin jama’a ba.
Ya kuma yi kira ga jama’a su kasance masu lura da kai rahoton duk wani abin da suke shakku ga hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.