Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba ɗaya.

Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya.

Da yake jawabi kan taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shigar Malamai a Siyasa da Tasirinta,” Ministan ya yabawa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen ci gaba da gudanar da wannan muhimmin taro, wanda ya bayyana a matsayin wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa a kasa.

“Ina da yakinin cewa wannan jerin laccoci zai ci gaba da haifar da canji mai kyau a kasarmu.

“Duk da haka, a wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda iyalai ke haduwa don yin addu’a, yin nazari, nuna jituwa da jinƙai ga juna, babu shakka, batutuwan imani da, siyasa da kuma mulki suna da dangantaka da jiya, yau da kuma gobe. Wajibi ne mu ci gaba da fahimtar yadda za mu tafiyar da su yadda ya dace.

“Sai dai, yayin da muke kokarin fahimtar alakar imani da siyasa da kuma mulki, muna kuma fuskantar kalubalen siyasa na ciki da waje, waɗanda ke tasiri ga yadda muke kallon hadin kan kasa a matsayin dunkulalliyar ƙasa,” in ji shi.

Ministan ya yaba da halartar manyan baki, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Ministan Cigaban Kiwo Dabobi, Malam Idi Mukhtar Maiha; da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Jakadan Najeriya, Ahmed Nuhu Bamalli. Haka nan, ya gode wa fitattun malamai, Sheikh Morufu Onike Abdulazeez da Farfesa Ismaila Shehu, bisa gudummawar da suka bayar a wannan muhimmin tattaunawa.

Da yake yin tsokaci kan muhimmancin Ramadan, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan wata mai alfarma domin yin nazari da inganta hadin kai, da sabunta aniyar su ta bada gudunmawa ga ci gaban kasa.

Ya jaddada irin nasarorin da aka samu a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman sanya hannu kan kasafin kudi na Naira Tiriliyan 54, wanda ya ba da fifiko kan tsaro, ilimi, ci gaban ababen more rayuwa, kiwon lafiya da noma.

Haka nan, Ministan ya yaba wa Shugaban Kasa kan kirkirar Ma’aikatar Bunkasa Kiyo Dabobi ta Tarayya, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin mataki da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da inganta zaman lafiya a kasa.

“Yayin da muke tafiyar da harkokin siyasa da mulki, tare da tasirin da suke da shi kan shawarwarin da muke yanke, yana da matukar muhimmanci mu zabi hanya madaidaiciya,” in ji shi.

A karshe, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi dabi’un soyayya, jinƙai, da jajircewa a lokacin Ramadan da bayan sa.

“Allahu ya albarkaci iyalanmu, ya shiryar da matakanmu, ya kuma ba mu hikima a dukkan al’amuranmu. Ramadan Kareem,” in ji shi.

Rel/Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Ramadan siyasa Yada Labarai Ministan ya

এছাড়াও পড়ুন:

Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi 

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu.  “A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ni da mataimakin shugaban kwamitin tattaunawa na gwamnatin tarayya, mun tattauna da ASUU, zan iya gaya muku a yau, a zahiri, an biya kusan dukkan bukatun ASUU, don haka ban ga dalilin da ya sa ASUU ta fara yajin aikin ba.” In ji Ministan ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano October 13, 2025 Ra'ayi Riga Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang October 13, 2025 Labarai Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista October 13, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya
  • Yadda Najeriya ta casa Jamhuriyar Benin 4-0
  • PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai
  • Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan
  • NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?
  • Kamaru: Jam’iyyun adawa sun ayyana Bakary a matsayin wanda ya lashe zaɓe
  • Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba
  • Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi 
  • Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki