Jigon APC Ya Fara Yunkurin Sulhunta Kwankwaso, Ganduje Da Shekarau
Published: 8th, March 2025 GMT
Ba Zaura kadai ba ne yake kokarin ganin a samu zaman lafiya a tsakanin ‘yan siyasar guda ukun. Sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da suka hada da dan takarar mataimakin gwamnan jam’iyyar a zaben 2023, Murtala Sule Garo da kuma fitaccen dan siyasa, Baffa Babba Danagundi, sun yi irin wannan kira.
Kwankwaso, Ganduje, da Shekarau, wadanda dukkansu sun yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan Kano, suna jam’iyyun siyasa daban-daban, kuma sun ci gaba da yin tasiri sosai a matakin kananan hukumomi, jiha, da kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Kaduna Ya Sauke Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ya Maye Gurbinsa Da Maiyaki
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sauke Farfesa Muhammad Sani Bello daga matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai kuma memba na majalisar zartarwa ta jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa Ahmed Maiyaki, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Yaɗa Labarai na Kaduna (KSMC), ne za a maye gurbinsa.
Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna MutfwangGwamna Sani ya gode wa Farfesa Bello bisa ayyukan da ya gudanar, inda ya ce shi ne kwamishinan ilimi na farko a gwamnatinsa, kafin daga baya ya zama kwamishinan yaɗa labarai.
Ya kuma yi masa fatan alheri a sauran harkokinsa na gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp