Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar.
A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci.
Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan ɗaya da muhimman kayayyakin amfanin gona kamar irin su iri, taki, famfunan ban-ruwa, maganin ƙwari da magungunan kashe ciyawa.
“Wannan dabarar ba kawai za ta inganta dogaro da kai ba ce har ma da rage kashe kuɗaɗen gwamnati,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, rabon kayan tallafin zai taƙaita ne ga ƙananan hukumomin jihar guda biyu kawai daga cikin 27 a shekarar 2025 saboda ƙalubalen da suke fuskanta.
“Ƙananan Hukumomin da za su sami tallafin abinci a shekara mai zuwa su ne: Ngala da Kala-Balge saboda yanayi na musamman.
“Waɗannan yankuna sun fuskanci mummunar ɓarna a gonakinsu daga giwaye kuma sun fuskanci ambaliyar ruwa. Don haka, a shekarar 2025, gwamnatin Jihar Borno za ta samar da kayayyakin tallafin abinci ga Ngala da Kala-Balge kaɗai,” inji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Umara Zulum Umara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci
Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta tarayya ta sanar da gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku domin neman taimakon Allah wajen kare ƙasar nan da kuma tabbatar da wadatar abinci. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da aka fitar a ranar 11 ga Yuni, 2025, wadda Daraktar Gudanarwa, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, dukkanin daraktoci, da mataimakan daraktoci, da shugabannin sassan sarrafa kayayyakin amfanin gona da sauran ma’aikatan ma’aikatar za su halarta. An sanya wa wannan shiri suna “Neman Taimakon Ubangiji Don Kariya da Cigaban Kasa.”
Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban Zangon Noma Da Kiwo Ɗauke Da Kasuwar Duniya A JiharModupe ta bayyana cewa manufar wannan addu’a ita ce neman jagorancin Allah da tallafinsa ga ƙoƙarin gwamnati wajen samar da ingantaccen tsarin abinci mai ɗorewar a fadin ƙasa. Za a gudanar da zaman addu’ar ne a shalƙwatar ma’aikatar da ke Abuja a ranakun Litinin: 16, 23 da 30 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta buƙaci dukkan ma’aikata su kasance cikin azumi domin samun tsarkakewa da shiri na musamman wajen roƙon Allah game da matsalolin da ke addabar fannin noma da tsaron abinci a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp