An Bukaci Kafa Dokar Hukuncin Kisa Ga Masu Safarar Da Shan Miyagun Kwayoyi
Published: 25th, February 2025 GMT
An bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta kafa doka wacce za ta tanadi hukuncin kisa ga masu safarar da kuma masu shan miyagun kwayoyi, domin kare rayuwar ‘yan kasa.
Wannan kiran ya fito ne daga shirin KAKAKI na FRCN Kaduna FM, inda masu kira suka bayyana ra’ayoyinsu a yayin tattaunawa da mai gabatar da shirin.
Masu magana sun nuna damuwa kan illar safarar miyagun kwayoyi a kasar, musamman yadda yake shafar matasa, wadanda ake kallon su a matsayin shugabannin gobe.
Alhaji Gaddafi Rigasa da Hajiya Aisha Mando sun jaddada bukatar hukumomin tsaro su kara zage damtse wajen yaki da wannan matsala, domin inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Sai dai sun kuma ba da shawarar a farfado da masana’antu a yankin Arewa a matsayin hanya daya daga cikin hanyoyin rage rashin aikin yi, wanda ke haddasa lalacewar matasa da kuma tabarbarewar tsaro.
SULEIMAN KAURA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
A wani gagarumin ci gaba na inganta walwala da ci gaban yara da matasa wadanda suka isa makaranta, Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Nasarawa NSUBEB, Dokta Kasim Mohammed Kasim ya karbi tawagar Kids & Teens Resource Center K&TRC a wani taron bayar da shawarwari da aka mayar da hankali kan shirin Ilimi don Lafiya da walwala, wanda UNESCO ke tallafawa.
An gudanar da babban taron ne a hedkwatar Hukumar NSUBEB, inda ya samu halartar kwamishinonin hukumar su uku, da Daraktoci da dama, da kuma tawagar K&TRC karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma Shugaba, Mista Martin-Mary Falana.
Tattaunawar a yayin zaman ta tabo batutuwan da suka shafi rayuwar yara da matasa a jihar, wadanda suka hada da yawaitar cin zarafin mata kamar lalata da fyade, cin zarafi a makarantu, kananan yara da auren dole, kaciyar mata, da kuma yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Mahalarta taron sun amince da bukatar gaggawar samar da cikakken martani ta bangaren ilimi domin tunkarar wadannan kalubale.
Shugaban hukumar ya yi alkawarin ba da cikakken kudurin siyasa na hukumar tare da ba da tabbacin baiwa kungiyar K&TRC na NSUBEB goyon baya wajen samar da yanayi mai dacewa don samun nasarar aiwatar da aikin.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.