Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da hakkin dan adam a matsayin abun matsin lamba na siyasa ko tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashe ba.

Abbas Araghchi, ya bayyana hakan ne a zaman kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya jaddada cewa, daya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga tabbatar da hakkin dan Adam a duniya shi ne amfani da matakan tilastawa kasashe.

Ya kara da cewa wadannan matakan suna da illa ga fararen hula kuma ba adalci ne ba ga marasa galihu kamar mata, yara, tsofaffi da masu nakasa.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya bayyana jin dadinsa a wannan zama inda Ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka assasa Majalisar Dinkin Duniya, a ko da yaushe tana mutunta daidaito da adalci a matakin koli. »

Araghchi ya bayyana cewa shekaru da dama da suka gabata al’ummar Iran na fuskantar manyan kalubale kamar takunkumin karya tattalin arziki da kuma ta’addanci, wadanda suka yi illa ga hakkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki, To sai dai kuma a cewarsa duk da wadannan kalubale, Iran ta samu ci gaba mai ma’ana A tsarin Musulunci da mutuncin bil’adama, da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya da ‘yancin mata da ci gaban masana’antu da tattalin arziki.

Muna bukatar a gaggauta soke duk wani takunkumi, saboda ba wai kawai take hakkin bil’adama na al’ummar Iran ba ne, har ma da haifar da wahala ga miliyoyin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai

Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu.

A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci.

Haka nan kuma ya ce; Daga cikin manufofin da HKI ta Shata cewa za ta cimmawa a yayin yakin, shi ne samar da sauyi a cikin wannan yankin, shi ya sa da dama daga cikin hukumomin kasashen larabawa su ka fahimci cewa raunana Iran yana nufin raunana kasashensu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5
  • Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa
  • Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF
  • Kwamitin Kolin JKS Ya Shirya Taron Bita Tare Da Wadanda Ba ’Yan Jam’iyyar Ba 
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  • Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
  • Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
  • Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan