Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya
Published: 25th, February 2025 GMT
Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna.
Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa kusan sau uku mutmin yana ɗaukar sa.
Wanda ke zargin yana sana’ar sayar da rake ne a Bakin Dago Tudun Jukun a Karamar Hukumar Zariya Jihar Kaduna.
Aminiya ta ziyarci xibiyar da ke kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya domin samun sahihin bayani kan lamarin a likitance.
Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700 Luwaɗi: An yanke wa ɗalibai biyu hukuncin bulala a bainar jama’aManajar Cibiyar, Hajiya A’isha Ahmed ta ce a ranar 12 ga watan 2 2025 ofishin ’yan sanda da ke Gonar Ganye, gundumar Tukur Tukur ya kawo wani yaro ɗan shekara 5 kuma ɗan aji ɗaya a makarantar firamare da ake zargin mutumin da lalatawa.
Bayan likitoci sun duba sun gano cewa yaron duburarsa ta bude, wanda hakan ke nuni da an yi yunƙurin zakke masa ta duburarsa.
Hajiya A’isha Ahmed ta ce sun dora yaron a kan magani har na tsawon kwanaki 28 kuma za su rika bibiyar sa domin su tabbatar da cewa yana amfani da maganin yadda ya kamata.
Ta ci gaba da cewa za ta tura sakamakon zuwa ga Kwamishinan Lafiya na Jihar Kaduna, kuma ta tabbatar da cewa sun bai wa jami’an ’yan sanda kwafin binciken.
Hajiya A’isha Ahmed ta yi kira ga iyaye da su daina boye irin wannan mugun abin da ke faruwa da yaransu wai don gudun abin kunya ko halin da yaran za su shiga.
Ta kara da cewa zuwa asibitin da yaran da aka ci zarafinsu a kan lokaci yana taimakawa wajen kula da lafiyarsu.
Mahaifin yaron da aka ɓata ya koka kan yadda ya ce wasu makusantan wanda ake zargin suke ƙoƙarin ɗanne shi da kuma kare shi wanda ake zargin.
Ya ce “abin mamaki shi ne ta yadda suka bi ta hannun mai anguwa wai a bani kuɗi na bar maganar,” DOn haka ya ce a shirye yake da ya bi haƙƙin ɗan nasa domin daƙile irin hakan a nan gaba ga ’ya’yan wasu.
Duk ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ci tura, domin layin wayarsa ta ƙi shiga, kuma har rubutaccen sakon da aka aika masa bai amsa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Luwadi yaro Jihar Kaduna
এছাড়াও পড়ুন:
Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
“Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faɗi gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na ƙalubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi.
El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa fushinsa da gwamnatin Shugaba Tinubu ne ya sa ya fice daga APC.
Ya ce yana da shekaru 65, kuma babu wani abu da ya rage masa a siyasa da zai nema, sai dai kawai yana jin cewa matsalolin Nijeriya sun yi tsanani sosai wanda ba zai zauna ya yu shiru ba.
“Zan iya yin ritaya cikin kwanciyar hankali, amma Nijeriya na fuskantar babbar barazana. Wannan ba don kaina ba ne – don ceton ƙasa ne,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa dole a zaɓi shugaban ƙasa mai nagarta da hangen nesa, ba wai kawai din ya fito daga wata jiha ba.
“Matsalolin da muke fuskanta sun fi girman la’akari da inda mutum ya fito. Muna buƙatar shugabanni masu hangen nesa da ƙwarewa don gyara Nijeriya,” ya bayyana.
Da yake magana kan sauya sheƙar wasu ‘yan siyasa zuwa APC, El-Rufai ya ce jam’iyyar SDP tana mayar da hankali ne kan gina goyon baya daga jama’a, ba wai kawai neman manyan ‘yan siyasa ba.
“Gwamna ɗaya yana da ƙuri’a ɗaya ne kawai. Jama’a ne ke yin zaɓe, ba manyan ‘yan siyasa ba,” ya jaddada.
A ƙarshe, El-Rufai ya ce tafiyar SDP tana ci gaba da karɓuwa a dukkanin sassan Nijeriya, ba a yankuna kaɗan kaɗai ba.
“Muna ci gaba da gina goyon baya a faɗin ƙasar nan. Aikin gina ƙasa yana faruwa ne a tsakanin talakawa, ba kawai a kafafen yaɗa labarai ba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp