HausaTv:
2025-07-31@18:30:00 GMT

Pezeshkian : Iran Za Ta Dakile Duk Makircin Makiya

Published: 11th, February 2025 GMT

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi kokarin dakile duk wani makirce-makircen da makiya ke kitsawa.

Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a da suka halarci bikin cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1979 a birnin Tehran yau Litinin.

Shugaba Pezeshkian Ya soki ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan na cewa yana son tattaunawa da Iran yayin da a lokaci guda ya ba da umarnin kakaba wa Iran takunkumi kan man da take fitarwa zuwa sifiri.”

Trump ya yi ikirarin cewa Iran na kawo cikas ga tsaron yankin amma “Isra’ila ce, tare da goyon bayan Amurka, tushen duk wani rashin tsaro a yankin da jefa kisan kiyashi a Gaza, hare-hare a kasashen Lebanon, Siriya, Iran da kuma duk inda ta ga dama.”

Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya suna neman haifar da fitina a cikin Iran, Sai dai kuma ba su san cewa a karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da kuma irin sadaukarwar da al’ummar Iran suke yi, za’a kawo karshen duk wannan mafarki.

Shugaban na Iran ya kara da cewa, Iran ba ta taba neman kaddamar da yaki kan wata kasa ba, kuma ba za ta taba mika wuya ga makiya ba.

Iran ba za ta taba barin makiya su aiwatar da munanan manufofinsu ba, in ji shugaba Pezeshkian.

Ya nanata kudurin Iran na samun zaman lafiya tare da makwabtanta bisa ‘yan uwantaka da mutunta juna, game da batun Gaza kuma, muna kare wadanda ake zalunta ne inji shi.  

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba

Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Manjo janar Musawi ya ce, ko kadan Iran ba ta yarda ko gaskata alkawullan Amurka,balle kuma zancen ‘yan sahayoniya.

Babban hafsan hafsoshin sojan na Iran ya kuma kara da cewa, sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana domin kalubalantar duk wan igigi na abokan gaba.

Manjo janar Musawi ya bayyana hakan ne dai a lokacin da ya yi tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Tajikistan Manjo janar  Imam Ali Sabir Zadeh.

A nashi gefen, ministan tsaron kasar ta Tajikistan, ya fara da yi wa janar Musawi murnar zabarsa sabon hafsan hafsoshin sojan kasar ta Iran, sannan kuma ya nuna bakin cikinsa akan rashin kwamandojin sojan Iran da su ka yi shahada a sanadiyyar harin ta’addancin HKI.

Manjo janar Imam Ali Sabir Zadeh ya kuma kara da cewa, al’ummar kasar Tajikinstan sun yi bakin ciki, don haka suna isar da ta’aziyyarsu ga al’ummar Iran.

Har ila yau minstan tsaron kasar ta Tajikistan ya yi ishara da tarayya akan harshe da al’ada da kasashen biyu su ka yi, haka nan kuma tarihi.

Haka nan kuma manjo janar Musawi ya yi wa Tajikistan godiya akan yadda ta kasance a tare da Iran a lokacin yakin kwanaki 12, lamarin da ya kara karfin alakar kasashen biyu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya
  • Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
  • Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba
  • Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Bauchi, Ahmad Makama, Ya Rasu
  • Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  • Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba
  • Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba  Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta
  • Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine