Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Published: 4th, February 2025 GMT
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI.
Yace dukaninsu mashaya jinin Falasdinawa ne, kuma sune suke gudanar da harkokin shugabancin Amurka a bayan fage. Banda haka su ne wadanda suke da biliyoyin dalar Amurka wadanda suke jujjuya duniya da su.
Yace: Amurka ta kara tallafin da take bawa HKI daga dalar biliyon 03 zuwa dalar biliyon 24 a wannan shekara wanda ya nuna cewa zasu ci gaba da yaki da kuma zubar da jin Larabawa ne fiye da kisan kiyashin da suka yi watani 15 da suka gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta caccaki kudurin IAEA wanda ta ce yana cike da siyasa
Iran ta yi Allah-wadai da wani kuduri da ta danganta da na siyasa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta dauka, tana mai cewa ba shi da tushe na fasaha ko doka.
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) da ma’aikatar harkokin wajen kasar sun fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Alhamis bayan da majalisar gwamnonin hukumar ta IAEA suka amince da wani kuduri da ke zargin Iran da rashin cika alkawuran da ta dauka na nukiliya.
Kuri’u 19 ne suka amince da kudurin wanda Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus suka tsara.
Kasashen Rasha, China da Burkina Faso sun kada kuri’ar kin amincewa da shi, Yayin da kasashen Afirka ta Kudu, Indiya, Pakistan, Masar, Indonesia da Brazil suka ce su kam ba ruwan su.
Sanarwar da Iran ta fitar dangane da wannan kudiri ta ce, Jamhuriyar Musulunci ba ta da wani zabi face mayar da martani ga wannan kudiri na siyasa.”
Sanarwar ta ce, Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, ya ba da umarnin gina sabuwar cibiyar tace uranium a wani wuri mai aminci.
Sabuwar cibiyar za ta kunshi sabbin na’urorin tace uranium na zamani inji sanarwar.
A cikin sanarwar, Tehran ta yi tir da kudirin na “siyasa da son zuciya” na IAEA Wanda Amurka da manyan kasashen Turai uku – Faransa, Jamus da Birtaniya suka tsara.
Iran ta kuma yi tir da shirun da Amurka da kawayenta na Turai suka yi wajen tinkarar yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kin mutunta yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Iran da Amurka suka tabbatar da sake ganawa a karo na shida a ranar Lahadi mai zuwa game da shirin nukiliyar Iran wanda a’a gudanar a birnin Muscat a shiga stakanin kasar Oman.