An ɗaure zawarawa a gidan yari kan aikata zina
Published: 31st, January 2025 GMT
Kotu ta daure wata matar aure da wani magidanci a gidan yari kan aikata lalata da juna.
Kotun Majistare da ke Gwagwalada a Abuja ta yanke wa zawararwan hukuncin ɗaurin wata uku kowannensu ne bayan samun su laifin aikata zina da junansu.
Matar mai shekaru 25 da bazawarin mai shekara 30 sun amsa laifin a lokacin da aka karanta musu takardar tuhumar a gaban kotun.
Zawarawan sun kuma buƙaci kotun ta yi musu sassauci.
Da farko alƙalin ya ba da umarnin tsare su har sai sun kawo shaida da za su yi rantsuwa cewa su mutanen kirki ne, amma suka kasa.
Daga bisani Alƙali Olatunji Oladunmoye, ya yanke wa kowannensu hukuncin ɗaurin wata uku ko biyan tarar Naira 25,000.
Tun da farko, ɗan mai gabatar da ƙara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotu cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin a jawabin da suka rubuta a caji ofis, bayan an kawo karar su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: bazawara bazawari matar aure
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan
Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari.
Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka zarce ‘yan ciranin gargajiya na wasu kasashe kamar ‘yan Siriya da Falasdinawa.