2025-05-12@22:14:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4426

«Shigar mata»:

    Dangin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, da kuma ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankin. Harin ya zo ne a lokacin da ake samun ƙaruwar ayyukan ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasar, musamman a yankin Arewa-Maso-Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kashe naira biliyan 2 da miliyan 300 domin sayo  na’urar binciken cututtukan zuciya (cardiac catheterization machine) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.   Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai bayan zaman...
    Mataimakin firaminsitan kasar Sin He Lifeng, ya gana da babbar jami’ar hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a daren jiya Lahadi a Geneva. Yayin ganawar tasu, He ya ce, kamata ya yi mabambantan bangarori su daidaita bambancin ra’ayi da takaddama bisa shawarwari, kuma cikin adalci karkashin ka’idar WTO. Haka kuma, a hada...
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Liman Dahiru, ya kaddamar da wani shiri na kiwon lafiya domin inganta kula da lafiya ga mazauna gundumar Makera.   Shugaban majalisar zai sanya mutane 700 da suka fito daga gundumar cikin Tsarin Kiwon Lafiya na Hadin Gwiwa na Jihar Kaduna (KADCHMA), matakin da ake sa ran...
    Ɓarkewar cutar kwalara ta yi ajalin mutum huɗu yayin da wasu gommai suka kwanta jinya a yankunan Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol. ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a...
    A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun cimma matsaya tare da fitar da sanarwar hadin gwiwa bayan taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, hakan wani muhimmin mataki ne da bangarorin biyu suka dauka na warware sabaninsu...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar Iran da Amurka ba zata shafi matakin jan layi da Iran ta gindaya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa da gaske kasarsa tana tattaunawa da Amurka, kuma tana neman cimma matsaya, amma batun neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta wani zabi ne da ba za...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da mummunan kisan kiyashi a garin Jabaliya, tare da janyo shahada da jikkatan wasu a Khan Yunis A rana ta 56 da sake komawa yaki ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta kan wasu wuraren zama, da...
    Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar...
    Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyar yayin da suka kai hari ana tsaka da cin kasuwa a ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato. A cewar mazauna, maharan sun wawushe kayayyaki a shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna masu tarin yawa. Jami’ar...
    Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na  kungiyar Rapid...
    Jami’ar Maryam Abacha MAAUN ta rufe wasu gidaje biyu da ke zaman ɗakunan kwanan ɗalibanta mata a Jihar Kano. Hukumar gudanarwar jami’ar ta rufe ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Hotoro da titin UDB a Kano saboda zargin rashin ɗa’a. Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa Za mu ci...
    Yayin da ake cika shekaru 10 da kaddamar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka watau China-CELAC Forum, kafar yada labarai ta CGTN da hadin gwiwar jami’ar San Martin de Porres da cibiyar nazarin siyasa da tattalin arzikin kasar Sin ta Latin Amurka da jami’ar Santiago de Chile, sun fitar da wani sakamakon...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari...
    Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC. A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa. Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin fara taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.   Sabbin Kwamishinonin INEC din da aka rantsar su ne Mallam Tukur Yusuf, mai wakiltar yankin Arewa maso Yamma, da Farfesa Sunday Aja, mai wakiltar Jihar...
    Sojojin sun kuma kwato mujallun AK-47 guda biyar da sauran makaman yaki daga a yayin artabun.   Majiyoyin sojin sun bayyana cewa, farmakin wani sabon shiri ne na sake tarwatsa shirin ‘yan ta’addan da kuma dakile hanyoyin da suke amfani da su wajen kai muggan hare-hare a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Masana kimiyya suna ƙoƙarin fahimtar yadda garken awaki ke rayuwa a wani tsibiri da ke Arewa maso gabashin Brazil fiye da ƙarni biyu (shekara 200) ba tare da samun tsaftaccen ruwan sha ba. Ba a fayyace yadda ainihin awakin suka hau saman tsaunin Santa Barbara tun a farko ba, wanda ɗaya ne daga cikin tsibirai...
    Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar...
    Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita.   Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin...
    ‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi. A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19. Taken da aka bai wa taron karo...
    Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar...
     Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata....
    Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba.   Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.  ...
    Dubun wani ɗan daba da ƙwacen waya da satar babura a cikin shigar mata mata wajen aikata ayyukan laifinsa a unguwar Ɗorayi da ke Jihar Kano ta cika. An kama matashin mai suna Abdullahi, wanda aka fi sani da “Audu Manye,” ne bayan tsawon shekaru ana zargin sa da tunzura faɗan ’yan daba, fashi da...
    Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu.   Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar.   Gwamnatin jihar Bauchi ce ta...
    Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas. Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar...
    Lamido a ranar Lahadi ya ce, “Ina da yakinin cewa duk wadanda suka bar PDP za su dawo ciki har da Ganduje, domin nan ba da dadewa ba APC za ta balle ta rabu gida biyu, saboda tana rungumar mutane masu tunani daban-daban.   “Na fadi haka, kuma ina sake maimaitawa: nan da watanni shida,...
    ’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna...
    ’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwmanati inda suka harbe wani malami har lahira sannan suka sace mata uku a Jihar Zamfara. Cikin matan da aka sace har da matar malamin a wannan mummunan lamari ya faru a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, a ranar Asabar....
    ’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna...
    Kwamitin ya kuma haɗa da Honarabul Sulaiman Adamu Gummi, Kwamishinan Al’amuran Addinai, wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaba, sai kuma Alhaji Habibu Balarabe, Babban Sakataren Hukumar Zakka, a matsayin sakatare.   Yayin ƙaddamar da kwamatin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana sa ran tawagar za ta tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka zagaye na hudu, yana tafiya kamar yadda ya dace. Kuma kasashen buyu sun kara fahintar ra’yin juna. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran da nakalto Aragchi yana fadar haka a wani hira da da ya...
    Sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan birane da garuruwan yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, hare-haren jiya sum sun fi maida hankali ne a garin Tulkaram da kuma sansanin yan gudun hijirar yankin A wannan karomma sojojin HKI sun bada umurni ga...
    Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar  tsagaita budewa juna wuta. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ɓallewar ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) bayan kwashe fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakaninta da su, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga ci gaba da kasancewar kungiyar ta Ecowas. A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne kasashen guda...
    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta sanar da cafke wata mata da ta ɓoye hodar iblis tana shirin tafiya ƙasar Iran. Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce an kama matar ce a filin jirgin sama a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas. Muna...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron ministoci na dandalin Sin da kasashen Latin Amurka da Karebiya ko CELAC karo na 4, kuma zai gabatar da jawabi.   An shirya gudanar da dandalin ne a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a ranar Talata 13 ga watan Mayun nan, kamar dai yadda...
    Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin  tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta...
    Sabon shugaban darikar ‘yan katolika na duniya Fafaroma Leo na 14 ya ce yana matukar bakin ciki da abin da ke faruwa a zirin Gaza, inda ya bukaci a tsagaita wuta nan da nan, a ba da agajin jin kai ga fararen hula da suka gaji, kuma a sako duk wadanda aka yi garkuwa da...
    Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar. Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan, babban kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai ziyara a kasar Nijar a ran gadinsa a Afrika. A ziyarar tasa ya gana da firaministan Nijar Ali...
    “Babu shakka cewa INEC na fuskantar matsin lamba mai tsanani, daga mambobin APC da sauran abokan huldarsu wadanda ke tsoron TNN, domin sun shirya yin magudi a zaben 2027 wajen samun nasararsu. “Amma muna kira ga INEC da ka da ta bayar da kai bori ya hau a matsayinta na hukumar zabe mai zaman kanta...
    Ya ce: “A yau ni ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya. Ba kawai ɗan watsa shirye-shirye ba ne ni, ni ne babban mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya. “Don haka za ka ga yadda burin da ake ganin kamar an kashe shi shekaru da dama da suka wuce, ya dawo...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar...
    Wata muhawara ta kunno kai a Jihar Kano da ma wajenta bayan gwamnatin jihar ta ba da umarni a cire naira miliyan 670 daga asusun ƙananan hukumomin jihar domin saye da kuma gyaran motocin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhanmmadu Sanusi II. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kashe naira miliyan 50 daga cikin kudin...