2025-07-06@20:37:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 17

«Satar waya»:

    Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya. A gun taron, sassan da abin ya...
    Al’ummar yankin Bachirawa a Jihar Kano sun yi ta maza sun cafke wasu matasa biyu da ake zargi da ƙwace waya a unguwar a yayin da ɓata-garin suke tsaka da ƙwacen. Matasan dai sun tare wata mata ce a unguwar suka ƙwace mata waya, wanda hakan ya sa mutanen yankin suka yi kansu tare da...
    Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar....
    Gwamnan Kano Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar. Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran Za mu ci gaba...
    Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta bayyana hakan a rahoton ayyukan ta’addanci na watanni 12. Rahoton ya bayyana ayyukan ta’addanci miliyan 51.89 da suka shafi iyalai, satar waya ce mafi yawa a ciki da kaso 13.8 da rahoton satar waya miliyan 25. Rahoton ya nuna akwai layukan waya da ke aiki a wayoyin hannu...
    Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta. Bayanai sun nuna cewa barayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a...
    Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji. Lamarin ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar...
    Rayuwa ta yi wa Talatu atishawar tsaki (ba sunanta na asali ba ne) tun daga shekarar 2018, bayan ta fada harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi a lokacin da ƙawarta ta ƙwaɗaita mata yadda lamarin yake. Ta kasance yarinya mai hazaka mai kimanin shekara 29, kuma ta yi karatu a Jami’ar Kwatano har ta yi aiki a...
    Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya, NRC ta tabbatar da kama ma’aikacinta mai suna Gift Eseeli, mai shekara 38, bisa zargin satar waya a Rafa Yard da ke kan hanyar Warri-Itakpe a harabar tashar jirgin ƙasa (WITS) Jihar Delta. Jami’an rundunar Man O’war na shiyyar Railway Command ne suka kama ma’aikacin. A cewar mai magana da...
    Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Tsaro da Gyaran Matasa, ya kama ’yan daba 31 a wani samame da ya gudana a unguwanni bakwai a jihar. An kai samamen ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Mayu, 2025 ƙarƙashin jagorancin Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata. Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace...
    Matsalar faɗace-faɗacen daba da kuma ƙwacen waya na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba ba ko na ƙwacen waya a sassan jihar ba, abin da ke sanya fargaba a zukatan al’umma. Munin...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta...
    Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago....
    Majalisar Wakilai ta buƙaci Hukumar Kula da Sadarwa (NCC) ta janye ƙarin kashi 50 na kuɗin waya da data da ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi. Wannan dai na zuwa ne a yayin da ɗan majalisar daga Jihar Bayelsa, Oboku Oforji ya gabatar da ƙudirin kan lamarin. Majalisar ta ce ƙarin bai kamata ba a...
    An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan...
    Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta kira zanga-zangar adawa da ƙarin data da kiran waya a Najeriya. NLC ta umarci rassanta na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya da su shirya domin fara zanga-zangar daga ranar Takara 4 ga watan Fabrairu mai kamawa. Ta bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce ganin an janye karin kashi...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya,...
۱