Leadership News Hausa:
2025-11-02@19:08:14 GMT

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

Published: 26th, August 2025 GMT

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa.

A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen Hausa da tarihinsa.

A Nijeriya, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sukan shirya taruka da laccoci.

A jami’o’i irin su Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu, masana da ɗalibai su kan tattauna kan ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma ƙirƙiro sababbin kalmomi da ke dacewa da zamani.

Haka kuma, jama’a na amfani da wannan rana a kafafen sada zumunta domin wallafa karin magana, hotuna da kayan al’adu, ko kuma rubuce-rubuce da ke nuna tumbatsar harshen Hausa.

Al’ummar Hausawa da ke ƙasashen waje su kan yi shagulgula da suka haɗa da rawa, waka, da sauran nau’ikan nishaɗi na gargajiya, abin da ke ƙara ƙarfafa zumunci a tsakaninsu.

Ranar Hausa ta Duniya ba ta zama lokaci na tunawa da harshen Hausa kaɗai ba, har ma da al’adu, kasuwanci da tarihin yadda harshen ya haɗa mutane da dama.

Ita ce rana da ke nuna alfahari da asali, tare da nuna irin rawar da Hausa ta taka wajen bunƙasa ilimi da ci gaban zamani.

Wannan yana ba da damar kallon harshen Hausa a matsayin abub alfahari da ya kamata a kula da shi tare da bunƙasa a nan gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Harshe Hausawa Rahoto Ranara Hausa Ta Duniya harshen Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan

Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan.

Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka.

Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump

Ministan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin.

A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen tashin hankalin.

A ƙarshen makon da ya gabata, RSF ta kori rundunar soji daga sansanin ta na ƙarshe a yammacin Darfur.

Rahotanni daga garin El-Fasher sun bayyana cewa ana samun kashe-kashe ba tare da shari’a ba, da fyaɗe da fashi har ma da hare-hare kan ma’aikatan agaji.

Wata Kungiyar Likitoci ta MSF a ranar Asabar ta ce ana fargabar dubban fararen hula sun maƙale sannan suna cikin mummunan haɗari a birnin Al Fasher wanda ya koma hannun dakarun RSF.

Rikicin Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023, bayan taƙaddama ta siyasa tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin ƙasar, da Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), Kwamandan RSF.

Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan yadda za a haɗa rundunar RSF da sojojin ƙasar bayan juyin mulkin 2021 da ya hamɓarar da gwamnatin farar hula.

Tun daga lokacin, yaƙin ya zama wani mummunan bala’i na jin kai, inda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce fiye da mutane miliyan bakwai sun tsere daga gidajensu, yayin da dubbai ke buƙatar taimakon gaggawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda