2025-05-18@15:52:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2805

«Sakatariya»:

    Ya ƙaryata zargin cewa an ci zarafin waɗanda ake zargin, yana mai cewa an bi doka da ƙa’idoji na ƙasa da na duniya a duk matakan binciken da aka gudanar. Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta an shirya shi ne domin yaudarar jama’a da neman tausayi tare da ɓata...
    A nasa bangare kuwa, shugaba Boric ya ce, kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ga kasarsa, kuma hadin gwiwarsu ya ba da tallafi ga al’ummomin kasashen biyu. Kazalika kasar Chile tana fatan yin hadin gwiwa da Sin wajen kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka da kiyaye karfin MDD, tare da kuma kare yanayin adalci na kasashen...
    Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.   Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma...
    Kasafin kudi na birnin tarayya Abuja (FCT) na shekarar 2025, kimanin naira tiriliyan 1.78 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisa, ya tsallake karatu na biyu. Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin FCT na 2025 ta wata wasika da ya aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen...
    Bukatun da shugaban Amurka ya fara gabatarwa shugaban gwamnatin Siriya al-Julani a gamuwarsu ta farko Fadar shugabanci ta Amurka White House ta bayyana cikakken bayani kan ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Siriya, Ali al-Julani, a birnin Riyadh fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar Laraba. A cikin...
    A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51 Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51,...
    Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana.   “Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga...
    Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, tare da ba da muhimmin jawabi. Inda Xi ya sanar da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen Latin Amurka da Caribbean wajen fara gudanar da...
    Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.   Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan...
    Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin...
      Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce zuba jarin Euro miliyan dari da goma sha ɗaya da tayi akan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani zai rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.   Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna, Ibrahim Hamza, ne ya bayyana hakan a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni...
    Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta...
    A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa...
    Rahoton MDD ya sanar da cewa, fiye da mutane 48,000 ne, ambaliyar ruwan saman da aka yi a Somaliya ya yi wa illa, yayin da wasu da adadinsu ya kai 17 su ka rasa rayukansu. Hukumar MDD mai kula da ayyukan jin kai da cewa ( OCHA) ce ta sanar da hakan,tana mai kara da...
    A yau Laraba ne dai shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya birnin Jakarta na kasar Indonesia, da zummar halartar taron wakilan majalisun kasashen da suke mambobi a kungiyar kasashen musulmi. Taron na wannan karon a kasar Indonesia shi ne karo na 19 da kungiyar ta kasashen musulmi take yi a matakin...
    Makaman sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyar, AK-49 guda biyu, harsasai sama da 400 da sauransu. CP Dantawaye, ya ce rundunar ta fara horar da jami’anta domin ƙara musu ƙwarewa da ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami. Ya ce wasu jami’an da suka halarci wani horo...
    Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da...
    Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar...
    Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin musulunci a nan Iran a shirye suke don fuskantar duk wani kuskureb da makiya zasu yin a kawowa kasar Hare-hare. Janar Salami ya bayyana haka ne a jiya Talata a...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an...
    Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan...
    Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta...
    Ya ce, aikin wannan cibiya ta “Saudi Noor” yana gudana ne a karkashin jagorancin Hadimin wurare biyu masu tsarki; Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mohammed bin Salman.   Hakan ya nuna manufar Saudiyya wajen gudanar da ayyukan jinkai a fadin duniya—wanda KSrelief ke tallafawa al’umma—domin inganta kiwon lafiya tare da magance cututtukan...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki...
    Kazalika, shugabannin kasashen biyu sun kuma gana da manema labarai a tare. Bangarorin biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan karfafa gina al’ummar Sin da Brazil mai makoma guda domin kara tabbatar da samuwar duniya mai cike da adalci, wacce za ta kasance mai dorewa cikin nagarta, da kara hada karfi da karfe...
    Amurka ta sanar da cimma wata yarjejeniya makamai mai tsoka ta Dala biliyan 142 da Saudiyya. Wanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, ke gudanar da ziyara a kasar Saudiyya irinta ta farko a ketare tun bayan sake hawansa karagar mulki. Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “mafi...
    A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance. bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata, yayin wani taron majalisar ministocin kasar, an rusa jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar. An kuma haramta tarurruka da sauran ayyukan jam’iyyun siyasar da kungiyoyin dake da alaka da siyasa...
    Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa. A yayin da yake bayyana goyon...
    Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata. Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai. HOTUNA: Trump na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Na hudu, zaman lafiya, Sin na fatan tabbatar da shawarar tsaro ta duniya tare da bangaren Latin Amurka, kuma za ta samar musu horo a bangaren aiwatar doka da shari’a bisa bukatunsu. Na karshe, muradun jama’a, inda karkashin haka Sin za ta samarwa dalibai 3500 na mambobin kawancen kasashen Latin Amurka wato CELAC tallafin kudin...
    Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudurin dokar da ke neman sanya tsarin mulkin karba-karba a tsarin shugabancin Najeriya. Kudurin dokar na neman wajabta yin karba-karbar kujerar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tsakanin yankunan siyasan Najeriya guda 10.
    A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka  da larabawan yankin tekun Pasha kamar...
    A yau Talata ne dai aka bude taron karawa juna sani karo na 31 a birnin Mashhad wanda shi ne karo na 31 da zai mayar da hankali akan yadda za a ci moriyar wannan fasaha ta fuskokin zaman lafiya. Hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ce dai ta tsara wannan taron kara wa juna sanin...
    Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga...
    “Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici...
    An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Musulunci kan zargin yi wa matar maƙwabcinsa dukan kawo wuƙa a Jihar Kano. Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun da ke zama a unguwar Kurna Asabe cewa wanda ake zargin ya kuma ji wa matar auren munanan raunuka. Ya yi wa matar wannan aika-aika ne...
    Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce, ya kuma kara da cewa idan makiya sun yi wani kuskure zasu yi nadamar hakan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana...
    Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga gwamnatin HKI kan hare-haren da ta kaiwa wani sansanin yan gudun hijira a gaza inda ta kashe ko takai mutanen da dama ga shahada, daga ciki har da mata da yara jarirai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya. Trump  zai ziyarci wasu kasashen larabawa a yankin, wadanda suka hada da Qatar da HDL da kuma Turkiya inda ake saran zai tattauna...
    Gwamnatin kasar Burtaniya ta gabatarwa majalisar dokokin kasar sabbin tsare-tsare na shigar kasar ta hanyoyi daban-daban. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Firai ministan kasar ta Burtania Keir Starmer yana fadar cewa abinda yake gabatarwa Majalisar don neman amincewarta, wani tsari ne wanda zai kawo tsabta a harkokin bada Visar shiga kasar Burtaniya daga...
    Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin ratayewa ga wani mutum da ta samu da laifin kashe abokinsa saboda hula. Kotun da ke zamanta a kan titin Miller ta yanke wa mutumin mai suna Adamu Isma’ila Arzai hukuncin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin soka wa abokinsa mai suna Auwal Shehu Kabara wuƙa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai da umarnin da Hukumar Kula da Harkar Wutar Lantarki a Najeriya (NERC) ta bai wa kamfanonin rarraba wutar da su biya diyya ga abokan huldarsu da ke rukunin Band A. NERC ta bai wa kamfanonin wannan umarni ne sakamakon rashin samar wa...
    Kasar Sin ta harba wani rukunin taurarin dan adam daga cibiyar harba tauraron na Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar. An harba taurarin ne jiya Lahadi da misalin karfe 9:27pm agogon Beijing, bisa amfani da samfurin rokar Long March-6 da aka yi wa ‘yan gyare-gyare. A cewar cibiyar ta Taiyuan, rukunin taurarin mai suna...