2025-11-02@14:13:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6426
«Sakatariya»:
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa...
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci. “Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da...
Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya...
Sakataren Ma’aikatar Yaki na Amurka, Pete Hegseth, ya ce ma’aikatarsa na shirin daukar matakin soja idan gwamnatin Najeriya ta gaza kawo karshen “kashe-kashen Kiristoci marasa laifi” a kasar. Hegseth, yana mayar da martani ga wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a Truth Social, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da yin shiru kan...
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya. Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa...
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan. Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka. Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan...
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku. Har zuwa lokacin...
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba. A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya...
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka. Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin...
Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya, yana mai zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana kashe kiristoci. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkabe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata...
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum. Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda...
Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata. Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta,...
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda...
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da...
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini. Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.” PDP ta dakatar da Anyanwu...
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande...
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini. Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Tinubu martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai jawo damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna...
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing. Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda...
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da...
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da...
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin...
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a a ‘Delta state’, na yi makarantar firamare da sakandare a Delta, sannan nayi aure a can. Yara na uku, Allah ya kawo rabuwa tsakani na da mijina. Babana dan ‘Nasarawa State’ ne, Mama ta kuma ‘yar Jihar Kano ce. Shekaruna Talatin da...
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya...
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da...
Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin...
Dan wasan da ya lashe kyautar a bara, Ademola Lookman na Nijeriya ba ya cikin jerin ‘yan wasan da aka lissafo a bana, inda hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf) ta samar da kwamitin kwararru wanda ya zakulo masu horarwa da ‘yan wasan da suka “Taka rawar gani” a tsakanin 6 ga watan Janairu zuwa...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta nuna damuwarta game da irin tashin hankali da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher. Iran ta sake jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Sudan, da hadin kai, da kuma cikakken yankin kasar yayin da tashin hankali ya mamaye kasar dake Arewacin Afirka. Ministan harkokin wajen kasar...
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai. Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa...
Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta bayyana shugabar kasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar. Shugaban hukumar zaben ya ce Shugaba Samia ta yi nasara a zaben da kashi 98% na jimillar kuri’un da aka kada. Bayanai sun ce manyan ‘yan takarar adawa ba su shiga ba, wasu kuma...
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya...
Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya soki hare-haren sama da Amurka ta kai wa jiragen ruwa a yankin Caribbean da Pacific, wanda ya kasance keta dokokin kare hakkin dan adam na duniya. “An ruwaito cewa an kashe mutane sama da 60 a jerin hare-haren da sojojin Amurka ke kai wa...
Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda ke neman wa’adin ta na farko a hukumance bayan ta gaji marigayi John Pombe Magufuli a 2021, ta tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar CCM mai mulki. Sai dai rashin shigar manyan ‘yan adawa da aka hana tsayawa ko aka daure ya jefa shakku kan ingancin zaɓen da aka gudanar, inda masu...
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa. A cikin wata sanarwa...
“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su...
3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon...
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya. Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci...
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe. “Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli...
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar. Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi. An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin...
Gwamnatin kasar Iran ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa . Tsibiran guda 3 da ake takaddama...
Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da aikatawa, a yanzu an tube shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko mukami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda da ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II. Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da...
Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dinkin duniya ta yi gargadin game da barazanar hadarin gwajin makamanin nunkiliya bayan da shugaban Amurka Trump ya bada umarnin a fara gwajin makaman nukiliya, Tace wannan matakin barazana ne ga tsaro da zaman lafiyar duniya. Farhan Haq mataimakin kakakin majalisar dinkin duniya ya shaidawa manema labarai a birnin New...
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a. Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne...
“Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.” Atiku ya ce duk wata doka...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Manyan Labarai Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai –...
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga...
Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League. Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4. Kotu ta...
Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa. A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Gummi yana wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara a majalisar wakilai. An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m An sake kama shi...