2025-10-25@20:10:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10702
«Jihar Katsina»:
An tsara cewa a cikin wannan makon da aka shiga ne dai za a gana a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha domin share fagen ganawar shugabannin kasashen biyu. Fadar mulkin Amurka “ White House” ta bayyana cewa an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin ministocin harkokin wajen Amurka da Marco Rubio...
Shugaba kasar Venezuela Nicolas Maduro ne ya bayyana cewa, kasarta ta mallaki makamai masu linzami samfurin “Igla-S” kirar kasar Rasha har 5000, domin tabbatar da tsaronta. Shugaba Maduro ya ce, tuni an girke wadannan makaman a wurare masu muhimmanci, kuma za a sake girke su a fadin kasar domin bayar da kariya ga sararin samaniyar...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran wanda ya gana da tawagar masu shirya taron tunawa da Alamah Mirzai Na’ini ( R.A), ya ce; muhimman siffofi biyu da malamin ya kebanta da su, su ne kirkira a fagen ilimi da kuma a cikin ilimin siyasa. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana Allamah Na’ini a matsayin...
Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka
A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin...
Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya ta ƙaddamar da yunƙurin ƙasa baki ɗaya na yin rigakafi kyauta ga karnuka da maguna domin yaƙar cutar haukan kare inda Jihar Gombe ke shirin yin riga-kafi ga karnuka 2,500 a matakin farko. Da take jawabi yayin bikin ƙaddamarwar da aka gudanar a Gombe, Babbar Sakatariya na Ma’aikatar, Dokta Chinyere...
An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15
A wurin taron, kwamitin tsakiya na JKS ya kafa wasu tsare-tsare da za su zama jagora kan bunkasa harkokin tattalin arziki da walwalar al’umma a cikin shirin na shekaru biyar-biyar na 15 wadanda suka hada da sake tabbatar da shugabancin jam’iyyar baki daya, da sanya kula da mutane a gaba da komai, da neman samun...
Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba. Sanarwar Bayan...
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon matakan takunkumi da kasar Amurka ta dauka kan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin, kasar Sin ta kara saurin yin kirkire-kirkire a matsayin mai zaman kanta, wanda ya haifar da karuwar sabbin nasarori a fannonin da suka hada da fasahohin kere-kere, da na’urar mutum-mutumi, har ma ta zarce...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa zata kara karfafa dankon zumunta da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin da mahukunta hukumar NAFDAC suka ziyarce shi a ofishin sa dake Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana farin cikinsa...
Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan manoman da suke aikin girbin amfanin gona a yankin Mbor na masarautar Mushere na Ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyu a ranar Laraba da yamma. Shugaban Ƙungiyar matasan Mushere, Kopmut Monday ne ya tabbatar wa Daily Trust faruwar...
An zargi mayaƙan Boko Haram da ISWAP da kai hare-hare wasu yankuna biyar da ke Jihohin Borno da Yobe. Sun kai hare-haren ne garuruwan Mafa, Dikwa, Marte, da Ajiri a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe. Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa...
Rahotanni sun bayyana cewa Ƴan ci rani 40 daga kudu da saharar Afrika sun mutu, sakamakon kifewar kwale-kwale a kasar Tunisia, sai dai an samu nasarar ceto wasu mutum 30. Kakakin ofishin masu gabatar da kara a Tunisia Walid Chtabri ne ya tabbatar da kifewar kwale-kwalen dake dauke da mutane 70 ‘yan kudu da saharar...
Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya . Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen...
Alkalan kotu a Kamaru sun yi watsi da bukatar da jamiyyun adawa suka ka gabatar masu ta neman ko dai su soke wasu sakamakon zaben shugaban kasar ko kuma su soke zaɓen baki daya, inda suka ce za su sanar da sakamako a ranar Litinin, sai dai ta dage lokacin daga baya. Zanga-zanga ta barke...
Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf. Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani...
Sama da yahudawa 450 daga sassa daban daban na duniya ne suka yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran shuwagabannin kasashen duniya da su kakabawa gwamnatin Isra’ia takunkumin saboda kisan kare dangi da nuna rashin dan adamtaka da ta yi kan alummar gaza. Acikin wata budaddiyar wasika da suka rubuta sun bayyana cewa ba...
Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore, bisa ci gaba da zanga-zangar neman a saki shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Sowore, wanda aka kama a ranar Alhamis a birnin Abuja, wasu jami’ai dauke da bindiga ne suka yi masa dirar mikiya, sannan suka tafi da shi zuwa wani wuri da...
“Allah ya albarkace mu da shugaba mai tsoron Allah da kishin jama’a – mutum ne mai kaunar al’ummar jihar Kano da Nijeriya, kuma me aiki tukuru domin ganin ci gabansu,” in ji Yusuf. Ya kuma jaddada kudirin sa na ciyar da jihar gaba bisa tsarin falsafar Kwankwasiyya, wanda ke jaddada hidima, rikon amana, da...
Rahotanni sun bayyana cewa ministan leken asiri na kasar iran Ismail Khatib a wajen taron da aka yi a lardin chahar mahali bakhtiyar ya bayyana cewa iran bata da wani lamuni na kare maslaharta ta hanyar tattaunawa da kasar Amurka, yace Amurka tana ikirarin cewa za ta ci gaba da tattaunawa da iran, tana boye...
Shugaban Ƙungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya sallami dukkanin lauyoyinsa. A zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis, Kanu ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya kare kansa ba tare da taimakon lauya ba. DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna ’Yan uwana...
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da yin ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga cfa 30,000 zuwa cfa 42,000, wanda ya yi daidai da naira 108,780 a Najeriya. Wannan ƙarin albashi na daga cikin matakan gwamnatin domin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda gwamnatin ta...
Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama wasu mutum uku da ake zargi da sayar da wa ’yan bindiga makamai da harsasai a Jihar Kaduna. An kama su ne bayan wani samame da jami’an DSS suka kai a ƙananan hukumomin Igabi da Kachia. ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani...
Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kwara, Barista Senior Ibrahim Sulyman, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da inganta adalci, kyakkyawan shugabanci, da samar da damar samun shari’a ga kowane ɗan ƙasa. Sulyman ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai na watanni uku (quarterly ministerial briefing) da aka...
Fiye da gidaje dari biyu da tamanin (280) a Karamar Hukumar Lafia sun samu kwandunan ajiyar shara (trash bins) domin inganta kula da tsaftar muhalli da rage datti a babban birnin jihar. An gudanar da rabon ne a birnin Lafia, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Dr. Margaret Elayo. ...
Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi....
Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa. A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya...
Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar. Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu. ...
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana. Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar...
Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da...
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi. Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin...
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin...
Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki. A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin...
Kotun kasa da kasa ta ICJ ta bayyana cewa Isra’ila ta karya dokokin kasashen duniya lokacin da ta hana shigar da kayan agaji ga Falasdinawa a Zirin Gaza. Kotun na mai bayyana cewa akwai wajabci kan Isra’ila na bayar da damar shigar da taimako cikin sauki zuwa yankin, sannan ya zama wajibi ta guji yin...
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin...
Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza . Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce...
Majalisar tsarin mulki a Jamhuriyar Kamaru, ta ce sai zuwa ranar Litini 27 ga watan Oktoban nan ne za ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar. Majalisar ta sanar da ranar ne bayan ta duba tare da yin watsi da duk wasu kararrakin da suka shafi zaben na ranar 12 ga watan...
Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa naɗin da aka yi masa na mataimaki na musanman a ɓangaren yaɗa labarai ga shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), Abdullahi Usman Saleh. A matsayinsa na ɗan asalin jihar Kano, ɗaukaka darajar Malam Ahmad Mu’azu zuwa wannan...
Gaza : Sabani tsakanin Isra’ila, Amurka da Masar kan mataki na biyu na tsagaita wuta Rahotanni daga Isra’ila ne cewa sabani ya kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da Amurka da kuma Masar kan mataki na biyu na aiwtar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma. Kafar yada labaran Isra’ila KAN ta bayar da...
Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar. A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden...
A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu. Shugaban Amurka Trump...
Ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin mai tsara dabara kan harkokin yada labarai a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). A matsayinsa na dan asalin jihar Kano, daukaka darajar Malam Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari...
Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11
Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar...
Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da...
A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya...
Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025...
Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana
Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kasuwar yawon shakatawa ta kasar tsakanin watan Janairu zuwa na Satumban bana. Kuma sakamakon binciken kididdigar da aka yi ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, adadin yawon shakatawa da mutanen kasar Sin suka yi a cikin gida, ya...
Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa a nahiyyar Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su lashe kyautar CAF ta shekarar 2025 – rukunin maza. Cikin wata sanarwa da CAF ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce an yi la’akari da rawar da ’yan wasa da masu horarwa suka taka wajen...