Gwamnatin Trayya Zata Zamantar da Kayayyakin Watsa Labaran ta
Published: 18th, April 2025 GMT
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kawo sauyi da kuma zamanantar da kafafen yada labarai na Najeriya da watsa shirye-shirye ta hanyar hadin gwiwa da inganta fasaha.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayar da wannan tabbacin a taron manema labarai na 2025 da aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
Da yake jawabi bayan dawowar sa daga taron kungiyar masu yada labarai na duniya (NAB) a birnin Las Vegas na kasar Amurka, ministan ya ce taron mai taken “Fasahar, The Trend, The Future,” ya samar da wani dandali na yin cudanya da masu ruwa da tsaki a duniya kan sabbin abubuwa da suka tsara makomar watsa shirye-shirye.
Ya ce shigarsa wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na bunkasa fasahar na bangaren yada labarai na Najeriya.
A cewarsa, “wannan zai tabbatar da kudurin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu sauyi mai dorewa a fagen yada labaran Najeriya.”
Ministan ya kuma bayyana irin rawar da ya taka a taron ‘yan kasuwan Najeriya da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa, inda ya gana da jami’an UNESCO kan shirin kafa cibiyar koyar da kafafen yada labarai da wayar da kan jama’a a Abuja. Ana sa ran Cibiyar da aka tsara za ta inganta tare da samarda ƙwararrun ‘yan jarida da haɓaka ayyukan watsa labarai masu dacewa.
Ya kuma kara jaddada cewa shirin gabatar da jawabai na ministocin da ake yi da kuma tarukan da aka shirya yi a fadin kasar nan na da nufin tabbatar da gaskiya, hada kan jama’a, da kara dankon zumunci tsakanin gwamnati da ‘yan kasa.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu, wanda ya bayyana muhimman ci gaban da aka samu a fannin samar da wutar lantarki, wanda ya yi daidai da ajandar gwamnati na bunkasa masana’antu a Najeriya da inganta samar da wutar lantarki a fadin kasar.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yada Labarai yada labarai
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Baje Kolin Kayakin Da Ake Kerawa A Iran Tare Da Taron Iran Da Afirka Karo Na Uku
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar.
EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan daga nan take samun kasuwa a kasashen duniya. Kuma yan kasuwa daga kasahe fiya da 100 ne suka shigo kasar don halattan kasuwar.
Esma’il Bakaee, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce ya na fatan a wannan kasuwar, kasashen Afirka da Iran za su amfani juna a harkokin kasuwancin da ake bunkasa a tsakaninsu.