2025: NAHCON Ta Ware Kujerun Aikin Hajji 1,407 Ga Jihar Taraba
Published: 24th, April 2025 GMT
Kujeru dubu daya da dari hudu da bakwai ne aka ware wa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Taraba domin maniyyata bana.
Babban Sakataren Hukumar mai barin gado Umar Ahmed Chiroma ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matakin da ake na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana na 2025 ba tare da tangarda ba.
Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma Musulmin muminai na gudanar da aikin Hajji a kowace shekara akalla sau daya a rayuwarsu.
Chiroma ya ce hukumar ta kai wani mataki na ci gaba ta fannin shirye-shirye kamar yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayar, inda ya ce sama da maniyyatan jihar 500 ne suka kammala biyan kudadensu.
Alhaji Ahmed Umar Chiroma ya kara da cewa a halin yanzu sama da Alhazai dubu biyar ne suka biya kudin aikin Hajji, yana mai kira ga sauran maniyyatan da su gaggauta biya domin cika wa’adin da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta kebe.
Ya yi bayanin cewa hukumar ta samu karancin masu zuwa aikin hajjin ba, inda ya danganta hakan ga tabarbarewar tattalin arziki ganin yadda amfanin gona da shanu suka ragu matuka a farashi.
Sakataren zartarwa ya bayyana manoma da makiyaya a matsayin manyan masu biyan kujerun aikin Hajji a jihar, inda ya nuna cewa gwamnatin jihar ta biya kujeru hamsin (50).
Chiroma ya ci gaba da bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara yin alluran rigakafi da tantance maniyyatan da ke shirin kammala shirye-shiryen aikin Hajji.
A cewarsa, hukumar ta kammala shirye-shirye a sansanin Alhazai a Jalingo, babban birnin jihar.
Sakataren zartarwa mai barin gado ya bayyana karara cewa jami’an hukumar sun ziyarci kasar Saudiyya inda suka samu masaukin da suka dace da mahajjatan jihar Taraba.
Umar Ahmed Chiroma ya yabawa Gwamna Agbu Kefas bisa daukar nauyin Alhazai hamsin, yana mai jaddada cewa wannan karimcin zai taimaka matuka wajen taimakawa mutane da dama wajen gudanar da aikin hajjin 2025.
Sani Sulaiman
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: shirye shirye
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa).
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman ayyuka da shirye-shirye tare da Bankin Duniya, Ma’aikatar Harkokin Waje, Harkokin kungiyar kasashen renon Ingila da Ci Gaban Birtaniya (FCDO), da Tarayyar Turai (EU), wanda hakan ya bata kwarewar da ta dace da sabon mukaminta.
Ya kara da cewa, Aisha Mujaddadi ta kasance a cikin kwamitoci da dama a matakin jiha da na tarayya, kuma ta taba zama memba a kwamitin gudanarwa na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna.
Sakataren Gwamnatin a jaddada cewa an yi nadin ne bisa cancanta, kwarewa da gaskiya, wanda ke nuna amincewar wannan gwamnati da kwarewar Aisha Mujaddadi.
Ya bayyana fatan cewa sabuwar Darakta Janar din za ta sauke nauyin da aka dora a kanta tare da kawo ci gaba mai ma’ana ga Jihar Jigawa.
Ya kara da cewa, nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin Darakta Janar na InvestJigawa ya fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria