Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah
Published: 29th, March 2025 GMT
Sunana Naja’atu Baffa Jihar kaduna:
Ni dai a gaskia ban son akwai wani anko da za ai wannan sallar ko babu ba. Ina son saka takalmi mai dan tudu ba sosai ba, sai mayafi blue black, sai atamfa ta riga (half bubu) da ‘skirt’, sai sarka da dankunne da Awarwaro ‘silver’. Ina sha’awar cin Snacks irinsu meatpie, samosa, doughnut da kuma cake, sai kuma Yoghurt mai inibi.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To batun shidimar sallah sai mu ce Alhamdullilah domin duk tanadin da mutum yayi sai ya kare, duba da yadda kayayyakin suturu ko tufafi suke tsada don haka sai mutum yayi amfani da abun da ya samu, domin gudanar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali ya fi komai dadi. To magana ta gaskiya shadda ita ce kalar kayan da zai fi yawa domin ita shadda ba a daina yayinta kuma tana daga cikin kalar suturar da duk mai hali ko sukuni zai so ya dinka, amma wasu kuma za su dinka yaduka domin kowa da irin kalar suturar da ta fi burge shi. To ni dai nafi sha’awar farin kaya musamman yadda manyan kaya ma’ana riga, binjima da wando da kuma hula fara wannan sune kalar suturar dana fi so musamman lokacin zuwa idi. Batun babu zabi duk wanda na samu zan ci, amma nafi son biskin alkama da miyar yakuwa ko jar miya. To da farko dai Masallacin idi shi ne guri na farko, sannan kuma sai ziyarce-ziyarce gidajen ‘Yan’uwa da abokan arziki.
Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar kaduna:
An yi wa sallah tanadi da dama kamar kayan da za a sa, Lalle, kitso, da sauransu. Bana tunanin gaskiya akwai wani anko da aka fitar domin a halin yanzu ko wa abin da Allah ya hore mai zai saka. Ina son saka shadda mai ‘stones’, ina son cin funkaso, tuwon shinkafa da miyar Agushi wadda ta ji ganda, kaji da kayan ciki, sai lemon ginger, sai farfesun zallar naman zabi.
Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:
Ana yin tanadi wa bukukuwan Sallah da yawa, amma dai ni kam babu tanadin dana yi wa sallar bana, batun anko ko yayin kayan da ake siya, ni dai kam har yau ban lura ba, amma dai bana Iyalai na suna sha’awar Shadda, kuma gaskiya ba na ina sha’awar cin sakwara da hadadden lemu (Ubangiji Allah ka kara hore mana). A bisa al’ada kuma muna kaiwa ‘yan’uwa da abokan arzuka ziyara, tare da taya murnar kammala ibada. Ubangiji Allah karva mana ibada, ya sa mun dace.
Sunana Muhammad Isah Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Tanadin dana yi wa wannan sallah shi ne ina so ta same ni cikin koshin lafiya da kuma ‘yan canji a cikin aljihuna. Wannan shekarar ta zo da son yin wankan shadda wato shampoo ita ce kowacce saurayi ko budurwa take/yake son sakawa duk da tsadar rayuwa da muke fama da ita. Ina sha’awar saka farar sutura ko shadda da farar hula a lokacin tafiya sallar idi. Abincin da nake muradin ci sh ine funkaso da jar Miya da naman kaji. Ina son kai ziyara zuwa gidan ‘Yan’uwa da abokan arziki in sha Allah.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar kano Rano LGA:
Babban tanadi shi ne Allah ya nuna mana ita muna raye da koshin lafiya. Haka ne kam duk da ana cikin yanayi ba za a rasa wadanda suka yin ba amma mu masu iyali iya yaranmu da iyayensu muka samu muka yi wa. da son samune ni dai sabuwar shadda fara idan kuwa ba ita ba to na sami koda koriya ce ko yadi shi ma fari ko koren. Waina da kunun daka ko na alkama da miya. Bayan dawowa daga sallar idi zan je gidan mahaifina da kuma gidan surukaina sai kuma na ‘yan’uwa da abokaina na kusa domin kara sada zumunci. Allah ya karvi ibadunmu.
Sunana Aisha T. Bello Jihar kaduna:
Sallah bikin daya rana in ji masu magana, a gaskiya na yi ma wannan sallah tanadi babba in Allah ya sa muna da rabon gani. Zan sanyaya raina ta samar da abun da na fi so a ci da sha, zan kai ziyara, zan je kallon hawan sallah, sannan zan kikkira ‘yan’uwa domin taya su barka da sallah da yardar Allah. A gaskiya bana jin wannan sallar akwai wani tanadi na anko kamar kullum, duba da yanayin rayuwa ana ta abun ci da sha ne, ina sha’awar saka doguwar riga da salla in sha Allah, sannan in sa babban mayafi in halarci sallar idi. In Allah ya ba ni dama ina so in kai ziyara jihar katsina don ganin dangina da ‘yan’uwa in sha Allah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Sallah Ƙarama Taskira ina sha awar Ina sha awar
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
“Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.
“Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.
“Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da wani asusu, a Zamfara a shirye muke mu ba da tallafin, idan kun shirya gobe, mu ma mun shirya.
“Mun shirya, kuma ƙofar mu a buɗe take, duk wani abu da zai kawo sauyi mai kyau a Zamfara muna maraba da shi, muna buƙatar tsari na abin da ku ke yi domin mu ci gaba da bin diddigin lamarin, zan samu wata tawaga da za ta riƙa hulɗa da cibiyar yaƙi da ta’addanci.
Tun da farko, Shugabar Rigakafi da Yaƙi da Ta’addanci (PCVE), Ambasada Mairo Musa Abbas ta ce, tawagar ta zo jihar Zamfara ne a madadin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da kuma kodinetan yaƙi da ta’addanci na ƙasa, Manjo Janar Adamu Garba Laka. “Muna nan a matsayin wani bangare na dabarun bayar da shawarwari na ƙasa baki ɗaya.”
“Muna son sake gode muku bisa irin karramawar da ka yi mana a Jihar Zamfara da kuma irin shugabancin da ka yi wa al’umma, muna sa ran haɗin kai don ganin cewa Zamfara ta zama kan gaba wajen yaƙi da ‘yan bindiga.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp