Muna buƙatar masu fassara a asibitoci — Al’ummar kurame
Published: 2nd, September 2025 GMT
Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe.
Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari.
Abba ya yi wannan kira ne ta bakin wani mai fassara a taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka shirya don inganta aiki.
Ya ce rashin masu fassara a asibitoci alama ce ta rashin kula da kurame a jihar, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum gare su.
An kama masu safarar muggan makamai a Katsina NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Da Mutane Zasu Bi Wajen Neman Diyya“Matsalarmu ba kiwon lafiya kaɗai ta shafa ba, a fannin ilimi, akwai makaranta ta musamman a faɗin jihar nan, kuma an bar yaranmu da dama a baya. Muna buƙatar ingantacciyar makarantar sakandaren kurame a jihar,” in ji shi.
Abba ya kuma yi kira da a sanya masu fassara a cikin shirye-shiryen gwamnati da kuma taron jama’a, don tabbatar da cewa bayanai kan manufofi da dama sun isa ga kurame.
Ya kuma bukaci gwamnati da ta tallafa wa mambobin ƙungiyar da jarin fara aiki, yana mai jaddada cewa da yawancinsu suna son yin kasuwanci amma ba su da hali.
Baba Kucici, sakataren ƙungiyoyin fararen hula a Jihar Yobe, shi ma ya gabatar da jerin tarin bukatun ’yan kasa a wurin taron.
Ya jaddada bukatar gwamnati ta samar da hanyar da za ta riƙa bibiyar ayyuka da shirye-shirye kai tsaye, yana mai cewa hakan zai nuna ɗaukar nauyi da kuma samun amincewar jama’a.
Aminiya ta ruwaito cewa tattaunawar ta tattaro masu ruwa da tsaki daga gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, da ƙungiyoyin al’umma don daidaita abubuwan da ’yan qasa suka sa a gaba kafin kasafin 2026.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Bikin hada-hadar ba da hidima na Sin wato CIFTIS na bana da ya kare a jiya a nan Beijing ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 85 da suka gudanar da baje koli da tarurruka, kusan kamfanoni 500, ciki hadda wasu daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya da manyan kamfanoni masu jagorantar bangarorinsu, sun halarci bikin, kuma an cimma nasara a fannoni sama da 900. A yayin da duniya ke fuskantar rashin tabbas, bikin CIFTIS ya karfafa mu’amala da kuma samun riba da juna.
Alkaluma na nuna cewa, a shekara ta 2024, jimillar cinikin ba da hidima na Sin ya fara wuce dala tiriliyan 1 a karon farko, wanda ya zama sabon tarihi, kuma ya kasance na biyu a duniya.
Masu zuba jari na waje suna kara zuba jari a Sin saboda babbar kasuwa. A halin yanzu, Sin ta zama abokiyar ciniki ta uku mafi girma a kasashe da yankuna 157, kuma ita ce kasa ta farko a fannin cinikin kayayyaki da ta biyu a fannin cinikin ba da hidima a duniya. A gun bikin na wannan shekara, Sin ta sanar da matakai da yawa, ciki har da “hanzarta aikin gwaji a yankunan gwajin ciniki cikin ’yanci da kuma yankunan ba da misali kan ayyukan ba da hidima na kasa” da “gaggauta bude kasuwar hada-hadar ba da hidima”. Wannan ya samu karbuwa sosai a wajen kamfanonin kasashen waje.
Ta hanyar tarurrukan baje kolin, duniya ba kawai ta ga sabbin abubuwa na tattalin arzikin Sin ba, har ma ta fahimci azamar Sin na hadin gwiwa da duniya da gina tattalin arzikin duniya mai bude kofa cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp