Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025 Sun Kai Sabon Matsayi
Published: 29th, January 2025 GMT
Shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na shekarar 2025 sun gabatar da wata “liyafar al’adu” mai kyau da ban sha’awa, kuma mai fasahohi ga masu kallo na gida da waje, bisa sabbin dabaru. Ya zuwa karfe 2 na sanyin safiyar yau Laraba, a dukkan kafafen yada labarai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG ya kai sau biliyan 16.
Bugu da kari, yawan masu kallon shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 ta hanyar talabijin yayin da aka watsa shi kai tsaye a cikin kasar, ya kai kashi 78.88 cikin dari, wanda ya kafa sabon tarihi a cikin shekaru 12 da suka gabata.
Ban da haka, an tattauna shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 har sau biliyan 27 a dandalolin sada zumunta a kasar Sin, adadin da ya zarce na bara.(Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400.
Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza.
Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza a dai dai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da kuma killace fararen hula da ke fama da yunwa.
Tun cikin watan Maris ne Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya haramta kai kayan agaji zuwa Gaza, a wani mataki da ya ce na da nufin tursasa Hamas ta amince da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila.